Recent Updates

Duk Karfin izzata Book 2 Page 35

 


💖The talent troupe writer's 💖





💋Duk Karfin Izzata 💋


By Star Lady



       





Page 35



Sosai take kuka har voice nata ya dai na fita sosai ta fara ganin dishi dishi takalman kafar ta ta cire ta riÆ™e a hannu ta cigaba da tafiya har ta É—an yi nisa da motar su,kaÉ—an kaÉ—an ta jiyo ringin watar yaya Khalid da ya bari cikin motar su tana kokarin juyawa ta koma wajen motar wata katuwar jib baka mai glass baki tayi parking a gaban ta tsayuwa tayi tana kallon motar bata ankara na sai ganin jabir tayi a gaban ta juyawa tayi tana kokarin komawa wajen motar su dan tayi picking call É—in da ake kiran yaya Khalid. Wasu jibga jibgan fararen mutane kiran turawa ne suka sha gaban ta kallon su take É—aya bayan É—aya 

Waya jabir ya ciro daga aljihun sa ya danna kiran tare da manna wayar a kunnen sa 


Jim kaɗan akayi picking call ɗin "hello dady" daga ɗayan ɓangaren dady yace "hello jabir burinka ya cika ko ka kama yarinyar da kake son ne?" dogon tsaki yaja cikin faɗa yace "dady ni fa ban gan taba sister ta kawai na gani wato dady daman da ka kirani kace min ga yarinyar ta fito wato rai na min hankali kayi ko? To wlh bakayi hakan aban zaba zaka biya" cikin muryan rarrashi dady yace "calm down my son kasan dai ba yadda za'ayi na baka wrong information ko? Kamar yadda na faɗa maka haka yarana suka faɗa min kasan shekara nawa sukayi suna min aiki wajen tsare hanyar fita gidan Abubakar saraki dan suga mai shiga da mai fita? kasan tsawon lokacin da na ɗauka ina aiki da su kuwa? basa bani information akan abu har sai sun tabbatar dan haka ka tambayi ita yarinyar da kace ita kaɗai ne awajen kaji ko kuma ka ɗauko ta ka taho da ita sai ka kirasu awaya..... jabir bai bar dadyn sa ya kai karshen maganar ba cikin tsiwa yace "dady ni zaka koyawa yadda zanyi aiki nane? ba ruwan ka da yadda zanyi tun da kai ka gaza ni zanyi kaya na" yana gama faɗin hakan ya katse kiran tare da tura wayar aljihun sa ya dubi yan daban nasa "kai ku kama min ita ku sata a mota mu wuce da ita" jin haka ya sanya Zahra ta fasa ihu tana kokarin gudu dan tasan halin jabir,damko ta yan koran nasa sukayi suka turata cikin mota suka shiga suka bar wajen da gudun gaske.


Katafare parking space dake gidan Abba motar su yaya bello tayi parking buɗe kofar motar yayi ya fito hasana ta biyo bayan sa riƙe da hanmun hajjo

Tsayuwa sukayi suna kallon gidan ba karami tsorata hasana tayi da ganin gidan su Ammi ba kankame yaya bello tayi suna bin gidan da kallo shi dai yaya bello bai ruÉ—e sosai ba kasan cewar yana shiga birni.

sun shagala da kallon gidan Haidar ya katse da cewa "muje ko?" dawo da kallon su kan haidar sukayi cikin sauri hasana tace "laaa kaga mai kama da baban su diyana" kallon Haidar da kyau yaya bello yayi aiko zancen hasana gaskiya ne Haidar kamannin sa É—aya da baban su hiyana Allah bai iko jini É—aya ya wuci wasa

   ganin kamar basu da niyar tafiyane ya sanya Haidar yayi gaba yana faÉ—in "idan kun gama kalle kalle naku zaku iya shigowa" cikin sauri suka bi bayan sa kai tsaye part É—in Ammi suka wuce


 zaune saman sofa mai zaman kanta 2 suka isko Ammi tasha kwalliya da dankareriyar kace pink color wuyar ta da hannun ta cike yake da gwala gwalai ta sanya alkyabban ta baki a saman kayan nata sai kyalli take tana É—aukan ido kallon É—aya zaka mata ka gane tana cikin kwanciyar hankali.


A kasa saman lallausan karpet É—in palon su yaya bello suka zauna hasana sai kallon palon take

    cikin girmamawa yaya bello yace "inawuni Ammi?" "Bello ku tashi ku zauna saman kujera mana" ba musu suka tashi suka zauna

Suna zama hasana ta miƙe zubur tana faɗin "lumewa nakeyi ba zan zauna ba zan nitse kasa,shi kan sa yaya Bello daurewa yake ya kame jikin sa waje guda ji yake kamar shima ya miƙe amma kasancewar yaga Ammi a zaune bata nitse bane ya sanya ya daure ya cigaba da zama bai tashi ba

Murmushin Ammi tayi kafin tace "to hasana zauna a saman karfe É—in ba damuwa" zama tayi suka gaisa da kyau ba karamin daÉ—i sukaji ba sai kallon Ammi hasana da hajjo ke yi

waya Ammi ta ɗauko ta fara kiran layin Zahra amma sai taji wayar a kashe mammaki ne ya kama tayaya zaa ce wayar auta a kashe abun da bai taɓa faruwa ba

ganin tunani bashi da wata mafita ne sai ta kira layin Khalid shi kuma ta kira bai É—auka ba

 sau biyu tana kiran sa shiru shiru hasbunallahu waniimal wakin take mai mai tawa a ran ta dan tun safe takejin faÉ—uwar gaba yanzu data kira layin su Zahra sai ji tayi faÉ—uwar gaban ya karu ko sunan Zahra ta tuna a ran ta sai taji kirjin ta na dukan uku uku 

Yaya Bello ya lura da halin da Ammi ta shiga lokaci guda ganin hakan ya sanya ya tattara nitsuwar sa cikin girmamawa ya fara magana "Ammi lfy naga yanayin ki ya sauya?" Ammi ta san wanene yaya bello dan haka bata ɓoye masa komai ba ta sanar da shi faɗuwar gaban da take ji tun safe sanna idan ta tuna sunan Zahra ko hiyana sai taji faɗuwar gaban ya tsanan ta .

    "to Ammi ina Zahra da hiyana nan suke?" Chewar yaya "ina ganin kamar suna wajen mazajen su ni ban sani ba nan na tafi na barsu suna hira amma kafin na tafi ita hiyana mijin ta ya kirata kaga kenan suna tare kiran su nake akan suzo ku gaisa kafin a kai ku gidan ku amma bari na kira shi É—in" tana kai karshen maganar ta shiga kiran layin bgs,sau biyu shi ma tana kiran layin sa bai É—aga ba wani tunani ne ya faÉ—o mata "anya wayan nan ba suna tare da matan su ba sai kiran layin su ake sun ki É—agawa to bari na kyale su na kira Yusuf su lamrat suzo su gaisa" da sauri ta kira layin Yusuf 

kira É—aya Yusuf ya É—aga yana faÉ—in "hello Ammi" "Yusuf ka turomin su lamrat suzo su gaisa da yayan su"  "to Ammi gasu nan zuwa" katse kiran tayi ta ajiye wayar suka fara hiran kauye da yaya bello


Da sallama Ahmad ya shigo palon Ammi,kusa da ita yaje ya zauna yana yamutse fuska "Baban hiyana ya akayi naga sai yamutse fuska kake ne?" guntun tsaki yaja kafin yace "Ammi ni wlh na gaji da zama ni kaÉ—ai kawai ki samo min mata ni ma,kila zan rage raÉ—aÉ—in rasuwar Aikam bani da wani Aiki fa sai tunanin sa" murmushi Ammi tayi kafin ta fara magana "aa baban hiyana garadai ka samo matar ka da kan ka kamar zai fi" "Ammi nifa ban san ina zan samo mata ba kai nifa ba zai iya tinkarar yarinya ince ina son taba gaskiya kawai dai ni ai mini irin Auren su bgs domin inaga.....bai kai karshen maganar sa ba idon sa ya sauka kan hajjo dake zaune kusa da hasana ta takure waje guda "wow Ammi da alama yanzu kam zan iya cewa mace ina son ta fa" ita dai Ammi tayi shiru tana kallon ikon Allah "ke zo" yayi maganar yana yiwa hajjo alama da hannun sa,kankame hasana tayi tana É“oye fuskar ta murmushi Ammi tayi ba karamin daÉ—in hakan taji ba "baban hiyana ka rabu da ita ba zata zo yanzu ba sai an kwana biyu ta saba da mutane yanzu dai bari su lamrat suzo su gaisa sai ka kai su gidan su akoi yan aiki da duk wani abun bukata a gidan" "Ammi gaskiya ni bazan É“oye miki ba ina son wanna yarinyar tamin" dawo da kallon sa yayi kan yaya Bello ya cigaba da cewa "kai ne yayan ta ko? to ina son kanwar ka amma zan iya hakuri sai gaba zaa samin ita a school ina fatan baa mata miji a garin ku bako? girgiza kai yaya Bello yayi kafin yace "baa mata miji ba" "good haka nake son ji yanzu dai muje na kai ku gidan ku gobe zanzo in sata makaranta da kai na" dogon salati Ammi tayi kafin tace "sannu baban hiyana wato ko kunya ta baka ji bako kai da nake gani mai kunya É—azun da safe yan uwanka sukazo nan suka karemin rashin kunya iya rashin kunya wai dan tsiya hirar nasuma a nan zasu min kamar basu da É—aki daga mai miÆ™ewa yace asame sa a É—aki sai mai matsowa yana wa matar sa raÉ—a daga gefe kuwa ga saura a zazzaune suna ta harkan su,ni ina gama sun mance da ni awajen wato kai ma yanzu zaka É—aura daga in da suka tsaya ko?" murmushin yayi ya sunkuyar da kai kasa tana É—an shafa gashin kan sa  dai dai lokacin su amrat suka shigo

Kusa da Ammi sukaje suka zauna "laaa yaya Bello kai ne?" Cewar amrat da sauri lamrat ta juyo

 cikin girmamawa suka gaida yaya Bello da fara'a ya amsa sanna suka gaida hasana 


Miƙewa yaya Ahmad yayi yana faɗin "muje na kai ku gidan naku wai Ammi inane ma gidan nasu?" "A lallai baban hiyana daman baka san gidan nasu bane kake wanna sauri sutashi ku tafi sannu ka da kokari" murmushi yayi yana faɗin "Ammi na ai farincikin na samu mata ne ya sanya hakan dukka" "eh lallai lokacin da zan hana ku shigowa part ɗi na yayi eyeee" gaba yayi yana faɗin "dan Allah Ammi inane gidan?" "gidan da Abban ku ya saiwa baban hiyana nan ne" "ok to mujen ku ko? Yana kai karshen maganar ya fice su yaya bello suka bi bayan sa.



Suna fita Abba ya shigo palon Ammi a ɗan ruɗe yace "Aisha na bar wayata a ɗaki tun safe yanzu nazo na samu miss har uku na auta nakira layin nata baya shiga na kira na mijin ta bai ɗaga ba ina take? miƙewa Ammi tayi cikin nitsuwa tace "ina ganin yaran nan suna tare da mazajen su ne fa domin nayi ta kuran layin shi shima bai ɗauka ba" "aa Aisha akoi abun da yake ba dai dai ba auta bata taɓa kashe wayar taɓa ina Yusuf yake? Lokacin guda tashin hankali ya bayyana a kan face ɗin Ammi cikin tsoro tace "to ka kira Aryan ko Yusuf kaji ina su baban suke" juyawa Abba yayi gaba ɗayan sa a kiɗime ya nufi hanyar fita yana faɗin "bari na nemo Yusuf muji kafin nayi magana da Safras" yana kai karshen maganar ya fice daga palon,

Komawa Ammi tayi ta zauna tana mamakin ina su Khalid suka je "Ammi ina Aunty Zahra ɗin?" chewar lamrat dawo da kallon ta Ammi tayi kan lamrat ɗin ta zuba mata ido sosai kafin tace "lamrat wanna watan kinyi period kuwa?" cikin kunya ta girgiza wa Ammi kai tana faɗin "aa Ammi" cool murmushi Ammi ta saki kafin tace "ku tashi kuje ɗaki kuyi hira da Aisha dan ta saba da ku" "to" sukace kafin su tashi a tare su shige ɗakin su,miƙewa itama Ammi tayi ta wuce nata ɗakin cike da zulumin ina Zahra da Khalid.



Maiduguri


Sai 3pm bgs ya dawo gidan Aunty farida zaune a palo ya isko Aryan da dadyn Junior ba tare da ya zauna ba yace "Aryan ya kamata muje ko?" Miƙewa Aryan yayi tare da fito da wayar sa daga aljihun sa dan ya kira Shahram a sukwane yace "what auta 3 miss call lfy kuwa?" cikin zafin nama ya fara kiran layin nata a kashe ɗago ido yayi ya kalli bgs dake tsaye ya tsare sa da ido yana jiran yaji menene

Ganin kamar Aryan bai da niyar magana ya sanya shi saurin ciro wayar sa a aljihu waro manya manyan idon sa waje sosai yayi lokacin da yayi karo da miss call É—in Zahra har uku na Ammi biyu da sauri ya fara kiran layin Zahra amma a kashe layin Khalid ya kira wayar tana ta ringing baa É—aga ba É—ago ido yayi ya kalli Aryan yayin da shima Aryan É—in shi yake kallon lokaci guda suka ja dogon numfashi 


A tare suka fara kokarin kiran Ammi dan suna da tabbacin ba lfy ba auta ta musu miss call har 3  kai ina ba lfy 

Call ɗin Aryan ne ya fara shiga wayar Ammi tana kwance saman gadon ta cikin sauri tayi picking tana faɗin "hello Aryan" jin voice ɗin Ammi lfylou ya sanya ya sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya yana faɗin "Ammi ya gida? Kowa lfy ko?" ciro wayar tayi daga kunnen ta dan ta tabbatar Aryan ɗin ne da gaske ya yake tambayar ta ya gida bayan a gidan suke jin haka ya sa tace "Aryan meke faruwa?" da ya fahimci ba komai sai ya nemi ya waske dan kar hankalin Ammi ya tashi


da kyar ya samu suka rabu da Ammi tana cikin kwanciyar hankali dawo da kallon sa yayi kan bgs dake tsaye,waro ido waje sosai Aryan yayi yana kallon sauya wan da bgs yayi lokaci guda idon sa sun kaÉ—a sunyi jaa sosai jijiyoyin kansa duk sun tashi sai huci yake ya kafe idon sa a kan wayar sa da alama wani abun yake kallo tun da ya ga bgs a wanna hali yasan ba lfy ba


Ba tare da yayi magana ba ya wuce bedroom na Aunty farida jim ka É—an ya fito É—auke da ita a kafaÉ—ar sa suka nufi waje,cikin zafin nama da taku irin na jaruman maza Bgs ya fice daga palon 

daga gidan Aunty farida kai tsaye Airport suka nufa Aryan na son tambayar bgs meke faru amma ya hakura dan ya san bgs ba zai faÉ—a masa komai a gaban Aunty farida ba kasan cewar bata da lfy


A ɓangaren jabir kuwa kafaren guest house na dadyn sa suka wuce da Zahra

Suna isa ya sanya aka fito da ita yaran baban nashi suka kewaye gidan da bindigu matsowa kusa da ita jabir yayi ya fara magana

  "Ke ina hiyana na?" Zahra da muryan ta baya fita sosai saboda kukan da ta sha tace "wasu sun É—auke ta" mari mai lfy jabir ya sakar mata a kumatu kafin yace "ni ba dake nake gaba ba hiyana da yayan ku nake nema dan haka yanzu ki bani number É—aya daga cikin yan gidan ku domin na kirasu su kawomin hiyana su anshe ki" cikin sauri Zahra ta fara karanto masa layin bgs yana sanyawa awayar sa


Sau biyu yana kiran layin Bgs amma bai É—aga ba kasan cewar bgs baya É—aukan new number

Mari mai karfi ya sake sakar wa Zahra cikin faÉ—a yace "ni zaki rai na wa wayo? ki bani number da ba zaa É—aga ba maza ki bani number da kika san ina kira zaa É—aga" already Zahra ta sha kuka har ta gaji yanzu gaba É—aya kukan ma ya dai na fita zuciyar ta ta bushe bata jin komai wani tunani ne ya faÉ—o mata "jabir wawane bai yi karatu ba ba abun da ya iya a school sai shirme dan haka bari nayi amfani da wawancin nashi na kafa masa tarko ta yadda yaya prince zai cin masa cikin sauki" katse mata tunanin da take yayi ta hanyar kara mata mari yana faÉ—in "ba dake nake magana bane?" Cikin dakiyar zuciya tace "number da na bakan nan shi ka É—ai ne number wan da na riÆ™e a kai na sai dai ka masa massage dan nasan baya kusa da wayar ne idan ka masa massage idan yazo zai gani" "good idea" ya faÉ—a kafin ya fara typing massage kamar haka "na É—auki Zahra tana hannu na akawomin hiyana azo a anshe ta" yana gaba typing ya turawa bgs 

Nauyayyar ajiyar zuciya Zahra ta sauke lokacin da taga ya turawa bgs sakon addu'ar allah jikan sa take masa a ranta dan tana da tabbacin ko ina yaya Prince yake nan da 30mins zai bayyana a nan.


Umarni zabir ya bawa yaran baban sa akan su É—aure masa Zahra a jikin itacen mango dake cikin gidan

  a take suka É—aure ta itakam ko a jikin ta dan burinta ya gama cika jabir tashi tazo karshe matikar yaya Prince yaga massage É—in nan shikenan kuma 


Jirgin su na sauka a Airport basu wani É“ata lokaci ba suka fito Aryan É—auke da Aunty farida a kafaÉ—ar sa dadyn Junior na bayan su 

"Aryan ku wuce gida ina zuwa sanna idan su Ammi suka tambaye ka ina auta Khalid da sister kace muna tare"cewar bgs yana kai karshen maganar ya nufi wajen motocin su

  ansan  key É—in motar dake hannun Abdol yayi ya shige motar da kan sa yaja da gudun gaske ya bar airport É—in.

Mamakin abun da ke faruwa Aryan yake har suka shige cikin motocin su suka bar Airport É—in.


Gudu suke da motar su kamar zasu tashi sama cikin kankanin lokaci suka fita garin kano,sunyi tafiya mai nisa tsakanin su da garin kano kafin su kutsa cikin daji da motar, nan ma tafiya mai nisan gaske sukayi kamar wayan da zasu bar dunuyar kafin su iso wani ka ta faren gida 

ta cikin gate É—in gidan suka kutsa motor su

bayan suyi parking ne suka firfito tare da fito da Khalid da hiyana da gaba ki É—aya sun jiggata barinma hiyana

waya ogan su ya fitar daga aljihun sa ya danna kira jim kaɗan ya manna wayar a kunnen sa yana faɗin "Oga yau fa mun fara aiki a cikin hotuna huɗu da ka baku munyi nasarar kama mutun biyu saura biyu suma mun sa musu ido muna ganin motsawar su daga gidan zamu kama su" daga ɗayan ɓangaren ogan yace "good yanzu abun da nake so da ku ita macen nan ina ganin kamar tana da mahimmanci sosai tun da har bgs da kan sa ya ɗauko ta a saman kafaɗan sa to ku kula da ita sosai shi kuma na mijin daman mun san already yana ɗaya daga cikin mutane shida da bgs ke matikar kauna dan haka ku masa azaban da sai ya gwammaci mutuwa kafin na shigo kasar macen ku barta sai na karisa bincike na tabbatar wacece ita yanzu abu ma na farko da na manta ban faɗa muku ba shine ku charje su ku raba su da duk wani abun dake tare da su dan nasan wanene bgs ku zauna cikin shiri dan zaizo tabbas zaizo ina son idan yazo ku haɗa su ku musu kisan mummuke ammafa ku kula kuma ina kara jaddada muku akan ku chire duk wani abun da kuka gani a tattare da su bgs ba na wasa bane" yana kai karshen maganar ya karse kiran juyowa ogan nasu yayi ya kalli su Khalid kafin yace "ku ɗaure mace shi kuma namijin ku kai she ɗakin horo amma kafin nan ku bincike su ku cire komai dake tattare da su ku kona" cikin dakiyar zuciya Khalid yace "dan Allah oga kayi hakuri kubar sister ta tafi ni ku riƙe ni ko kashe ni zakuyi ku kashe ni amma ita dan Allah ku kyale ta" wani mugun dariya ogan yayi mara daɗin ji

 sai da yayi dariyar sa mai isar sa sanan yace "daman muna tantama akan macen shin tana da mahimmanci a wajen kune ko bata da shi yanzu ka tabbatar mana tana da matikar mahimmanci mungode da ka bamu amsa ba sai mun sha wahala ba kai ku É—auki mace ku sanya ta a É—akin duhu shi kuma ku kai min shi É—akin horo bari na É—an wasa jini a kan sa kaÉ—an ita kuma macen zuwa dare damuyi ferfesun ta yau akoi sharholiya


Ko alamar tsoro babu a furkar hiyana cikin dakiyar zuciya tace "dan Allah ina son inyi sallar azahar kafin ku kai ni in da zaku kai ni" cikin fushi ogan nasu ya juyo zai zabga mata mari Khalid yayi saurin shiga tsakanin su yana faÉ—in "dan Allah oga kayi hakuri bata da lfy ne amma In Sha Allah ba zata sake magana ba" tsaki ogan nasu yaja cikin tsawa yace "ku sani nan ba gidan wasa kuka zo ba duk wan da ya sake kawomin shirme sai na fasa kan sa da bindiga yasin" 


hararar sa hiyana tayi ta kasan ido a cikin zuciyar ta tama faÉ—in "karamin mara kunya ne kai tun da ba zaka iya tinkarar yaya Prince da kan shi ba sai ka sato wayan da yake kauna dan ku cutar da shi ai cikakken namiji gaba da gaba yake tinkarar yaki ba ta baya ba" tayi nisa cikin tunani taji wani kato yana kokarin cire mata hijabin jikin ta da niyar su chajesu a zuciye  ta rufe ido ta zabga masa wani wawan mari cikin fushi tace "duk wan da ya sake yun kurin taÉ“a jikina a gidan nan wlh sai dai mu mutu tare mutuncina yafimin rayuwata jikina dan mijina kawai akayi shi ni jinin fulanin daji ne tsoro baya cikin jinin mu ni kuma kanwace ga babban soja da babu irin sa jarumin namiji É—aya tamkar da million wadda shi kaÉ—ai yake tarwatsa rungunar yan ta'adda komai girman ta ina son kusani tafasasshen jinin dake gudu a jikin bgs shine nima a jikina karkarinta dai kuce zaku kashe ni to idan kun kasheni ku kuma ku tabbata a duniya karku mutu" waro ido Khalid yayi yana kallon ta dama sister tana magana haka lallai mace mai mutun macece ban taÉ“a jin sister tana magana haka ba amma yau da zaa taÉ“a mutuncin ta dubi yadda take magana ko tsoro babu wato da a taÉ“a mutuncin ta gwara ta mutu In Sha Allah babu abun da zai sameki sister da izinin Allah tun da kekaye yun kurin kare mutuncin ki Allah ba zai taÉ“a bari aci mutuncin naki ba

Khalid yayi nisa cikin tunani bai ankara ba sai gani yayi wannan mutumin da hiyana ta mara ya É—auke ta da wani gigitatchiyar mari tare da kwashe kafafunta ta zube kasa ta buga kanta a kasa,gadan gadan mutumin yayi kanta da niyar dukan ta da sauri Khalid ya sha gaban sa yana kokarin bashi hakuri da karfi mutumin ya É—aga gindin bindiga ya bugawa Khalid a kai kan kace me jini ya fara zuba kamar famfo zubewa kasa Khalid yayi baya ko motsi cikin tsawa mutumin yace "mutunci ko to yau zakiga mutunci kai ku samin ita a É—aki yau sai kin gane shayi ruwane!!"



To masu karatu nima na tafi inje inyi nawa sharholiyar domin wanna lamari yafi karfina sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu more love lodi lodi 🥰

No comments