Namijin Gaske Complete Hausa Novel
[30/04 3:40 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
1⃣
By two besties
_salma Ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*( Marsal)*
®hausa online writters
Godiya ga Allah sarki da yabamu damar rubuta littafinnan *namijin gaske*wannan littafin yazo da abubuwa masu rudani,da sakacin mata,nasan zakuji dadin labarinnan dears,Allah yabamu ikon kammalawa lfy,inda mukayi kuskure Allah ya yafe mana gabaki daya ameen.
→☆STARRING☆←
→the handsome guy *ADAMS .A. BILLONIER*
→uwar gida ran gida *BUSSINEESS WOMAN BINTA*
→yar zaman banza *ummie*
→barrister *SUHAILAT*
→yar boko tsantsa *khalisat*(sugar baby)
AND OTHER.....
●adams ne zaune a tafkeken falon dayasha kayan alatu na zamani,kallo zakayiwa guy din kasan lalle kudi ya zauna daram,kai masha Allah kyakyawane ajin farko,da daya tilo ga shugaban kasa his excellency ahmad lawal,wanda mahaifiyar adams ta kasance shuwah,yayinda mahaifinsa ya kasance kannuri,shi kadai Allah ya basu ,yayi karatunsa a indonesia,inda ya karanci bussiness,bashida ra,ayin aure,but ra,ayinsa yanason mace shagwababbiya,yar lele,son rigima,da jan aji,da rashin son abin duniya,wanda takeson kwalya,mace mai tsiwa,da rashin kula da shishigewa mutum,ga iya girki duk inda ta gifta kamshi ke tashi ajikinta
Adams kyakyawane ajin farko,farine ba chanba,dogone mai faffadan kirji,baya dariya saidai yayi murmushi ,ga dogan hanci,bakinsa pink,dan karami ga daradaran ido,adams bayason raini,hadadden gayene wanda akamai lakabi da namijin gaske,yanada escort,mata sun mutu asansa,ko motarsa zakaga tambarin *NAMIJIN GASKE*
ADAMS YA DAUKARWA KANSA BA MACEN DA ZATA JUYASHI A DUNIYARNAN,YANA AMFANI DA KARFIN KUDI DA MULKI(but mudai marsal munce akwai)
Adams shalelen baba,yana kammala karatunsa abinda yazo ya tadda ya tayar mai da hankali mata uku aka daura masa aure dasu rana daya,ba dama ya musa dady
*DAWOWA LABARI*
Cikin bacin rai adam ya kalli matan dayake zaune a tsakiyar falo din yace to zan kafa muku dokoki
Na daya banson kazanta
Na biyu dole ko wacce ta aje aikinta zan sa mata kudi miliyan ishirin abanki in bude mata shop complex,sannan kuma banson taron kawaye da hayaniya,sannan in baninna kira maceba tazo ,to zata kwana a guard room din gidannan ita da karnuka suta cizonta
Sannan kar wacce ta fita ba tare da izini naba,baabinda babu na more rayuwa a gidannan
Sannan banson shiga hakkin wata koneman fitina
A tsarin rayuwata basaki,saidai in miki horo mai tsanani
Saboda akwai masu aiki kala kala a gidannan dafatann kun gane,kuma inason kowa tamin introduction din kanta meye alakarta dani
Dayar wata chocolate colour yar kyakyawa da dan jikinta duma dumatace nidai sunana binta umar abba ni yar kanwar dadynka ce,ni yar bussiness ce nayi karatuna achairo,yanzu nice uwargida ni aka fara kawowa,inAllah ya yarda zamubi doka
Murmushi adams yayi yace good
Dayar wanda ta kasance fara kyakyawa,tace ni sunana nafisa nidai nayi karatu nayi degree but banason yin aiki,kuma niyar abokin mahaifinkane,kuma ni fulanice,in Allah ya yarda za,abi doka azauna lfy
Kallo ya koma ga barrister suhailat da taketa faman latse latse awaya tana game
Adams y kura mata ido yace kefa
Kyakyawace yar fara ajin farko ga ido masha Allah,ga hanci a yatsine ta kallesa ta mayar da kanta tana kallon wayarta
Tsawa namijin gaske ya daka matayace badake nake maganaba?
Bata fasa abinda takeba kuma bata dago da kantaba tace nidai sunana suhaila .a. tanko na kasance shuwah ni yace ga kanwar mahaifiyarka,ni shuwahce yar maiduguri,nayi karatuna akasar turkey na karanci law,ni bazan iya barin aikina akan kudinkaba,donhaka tun wuri ka canja shawara tunda ba,ayi yarjejeniyar barin aikinba,kuma ni ba kowani doka zanbiba,tsaki tayi ta tashi kamshi na tashi ajikinta tadanyi takun kasaita tace ni zabin iyayenkace kuma ni ba sanka nakeyiba,wayanda sukesonka su yakamata subi dokarka
Bata karasa kalaman bakintaba taji saukar mari uku a jere
By
Marsa
[30/04 3:40 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣
By 2besties
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writters
●taga taga tayi uwa zata fadi,adams ya janyo hannunta,ya nunata dadan yatsa yace kisan wa zaki raina badai namijin gaskeba.
Binta ta faki idon namijin gaske tawa suhaila dake rike da kunci cikin bacin rai gwalo tana Allah ya kara
Suhaila tace nika mara,to wallahi muhadu a kotu,kai takamarka kudi,kuma wallahi bawanda ya isa yahanani aikina
Adams yace inkin isa ki fita gobe zan nuna miki ni na isa har nayi yawa,ya kalli binta yace kekuma ki sameni a turaka yanzu
Tafiyarsa yayi ya danna inter com,yayi shigewarsa bangarensa
Yayinda binta da ummi suka sheke da dariya,binta tace yarinya waike tsiwa gashi kinsha mari,angaya miki ana juya irin mazannan ne?
Harara suhaila ta dankara musu tace aini ba kwadayayya bace irinku,ni baya gabana kudinsa baya gabana ,banza makwadayyata wanda zuciyarku ta kekeshe ta mutu
Ummi tace ke ke karki saki ki zagemu,ai gwanda muci bulus,kece babbar banza
Binta tace kunga sai gobenku nabi mijina
Kishi kamar ya kashe ummi ko kulata batayiba,a zuciyarta tace in Allah ya yarda dukanku sainasa ya tsaneku ya muku sakkin wulakanci,namijin gaske ya zama nawa nikadai
Suhaila tsaki tayi tace Allah yasa ku kwashi kanjamau,tayi shigewarta part dinta,yayinda ummi da binta suka tafa kishi kishi
Wanka binta ta shiga,tasa matsatsu fitsararren kayan bacci ta shafa turare,ta fito ta dora zani akai,tazo ta wuce ummi datayi tagumi a falo,murmushin mugunta tayi tace ummi saida safe,pls ki tashi karfe goma kidan samin tafashasshen ruwan zafi,saiki kawomin adams yamin wanka
Tsaki ummi tayi tace wace jakarki,ai kinyi karya kice adams ne zaimiki wanka,abinda mun gane kin gama sheka ayarki awaje
Murmushi binta tayi tace hmmm ai ni dake duk jirgi dayane ya kwasomu ya diremu,harda suhaila din
Ummi ranta ya bace tace aini nayi matsi wallahi koke da duka zai koroki
Binta tace anniyarki yabiki,kaikayi koma kan mashekiya,tayi wucewarta abinta tana rangwada
Ummie kamar ta bita ta shaketa takeji,amma tafi kishi da suhaila don yar shuwahfa akace,gaskiya da sake,inbata tashi tsayeba dole ta fitar dasu,ahankali suhaila ta nufi bangaren da adams suke
Ta labe,ji tayi abinda yake wakana;but takasa tantance komai
;;;;;;;;,,,,,,;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;
Suhaila ce a kitchen tana hada,shayi tana dan wakarta
Kamshin turarensa taji
Namijin gaskene tsaye kekem dagashi sai farin singlet da shortnikker farare ya zuba mata dara daran idanuwansa,yace ke baki iya gaisuwabane iyeh
Tsaki tayi taci gaba da abinda takeyi,ji tayi an dan buge bakinta yace duk randa kika karamin tsaki wallahi sai ranki ya bace
Magana kasa kasa suhaila ta fara
Yayinda namijin gaske yace dama so nake ki dafamin ruwan zafi,binta zatayi wanka dashi
Sakin plate din suhaila tayi ya fadi,ya fashe tace iyeh,tab wallahi inna dafa shegiya uwata ta haifen tab,kaga shayi zan hada yau muna da shara,a kar in makara
Adams yace order na baki aike da zuwa office har abada,kinyi bye bye da zuwa office
By marsal
[30/04 3:40 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
3⃣
By 2besties💞
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®Online Hausa Writers
●ya fada yana hade rai wallahi baka isa ka hana ni zuwa office ba tunda ba'a cemin haka ba zuwa kamar nayi na gama kuma wllh ban zan dorawa wata gardiyar ruwa sai dai ta mutu ba wanka oho wannan ya rage naki
Kuma naga ta inda zaki uhmmm ta inda ake zuwa ta nan zani in kuma kaki ka bani takarda ta danni aiki na ya fiye min wannan zaman
Wani murmushi ya saki me cike da takaici yace au har kin manta abinda nace
Ba saki a tsari na dan haka aiki dole ki barshi yana fada yai ficewar sa cikin bacin rai ya nufi falo
Wani wawan tsaki ta saki rai bace ta fito tai hanyar dakin ta
Ummi ce labe take jin me suke yi tana ganin juyowar sa tai saurin koma wa ta zauna tana tana sa wayar karya
Ke ya kira ta dagowa tai a tsorace tana tunanin ya ganta jeki ki hada ma binta ruwan zafi tai wanka
Cikin sauri ta dago kanta suna hada ido taga fuska daure kamar wani zaki ga wani kwarjini da yai mata
Kasa tai da kanta tace dama ta samu a cikin ran ta amma a zahiri cewa tai to yallabe a nawa zan sama ta ruwan Kasan Yaki akae da zaman banza wani kallo yai mata
Yace Ke kike yunwar kudi ya watsa mata bandir din en dubu dubu gashi nan yai gaba ya barta
Ita kuwa suhaila daki ta shige da gudu tana kuka waya ta dauka ta kira dadyn Adams cikin kuka take magana subhanallah me ya faru dady ya tambaya
Dady ba shine yace bazan fita aiki ba kuma ni wallh bazan iya ajiye aiki na ba
Haka yace miki eh to bari nai masa magana share hawayen ki Karki damu kinji 'yata tom dady ta kashe wayar ta
Dakin adams Ummi ta shiga inda ta tarar da binta a kwance ta wani narke a gado tana jin an turo kofar ta kuma langwabewa ganin Ummi yasa ta hade rai malama Kije ki hada ruwan wanka kin tsaya gulma
Dariya Ummi tayi sosai lallai ma kin san baki da wannan matsayin kuma baki isa kisa nayi miki wani abun ba yanxu ma wallahi ba'a banza zanyi ba
Tashige toilet ta bar binta da takaici
[30/04 3:40 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
4⃣
By 2besties
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(Marsal)*
®online hausa writter
◆ummie ce keta waka adams ya shigo dakin,cije lebe binta ta fara kamar gaske tace mijina ka gaya mata ta daina min ihu a daki kaina ciwo yake
Tsaki dan gaske yayi yace to kudai mata kunada matsala
Ummi dake toilet tace gaya mata dai kuma kidaina cewa mijinkine ke kadai duka mijinmune
Ummice ta fito binta dake kwance sai galla mata harara take;ummi tayi murmushi tace,my dear nagama
Dan gaske ya murtuke fuska yace saura ki mata wanka
Da sauri binta ta hantsilo daga kan gado tace ai na zata kai zakamin
Ummi ta kyalkyale da dariya yayinda dan gaske ya daka mata tsawa yace akanme zan miki wanka raguwar rake,ai wanda yafara saninki shi yakamata yamiki wanka,be careful niba sa,anki bane
Ficewarsa yayi yayinda ummi ta sheke da dariya ta rangada buda ayyiri yiri iyayen dadi manya
Binta ji take kamar ta kwarara ihu tsabar takaici takasa magana
Adams yana fita mahaifinsa,ya kirasa a shagwabance yace hi dady ykk,dadynsa ya balbalesa da masifa yace to sarkin ikko da mulki to kabar yarinyar mutane taje aikinta kokuma ranka yabace,kashe wayar yayi
Yayinda adams ya tsaya yana mamakin wacce matsayi yarinyar nan ta taka har suka shaku da dady haka
Kamshin turarenta yaji tazo giftawa,farar rigace t-shirt da bakin siket high west tasa,ta dora rigar loya a kafadarta ,tasanya hijjabi fari baby hijab,ta sanya siririn glass fari ,fuskarta tasha makeup,tayi bala,in kyau
Har ta kusa ta gifta adams beyi maganaba,janyo rigarta yayi,yace ke wace dazaki hadani da mahaifina,ke gaki uwar muna fuka ko?
Harara suhailat ta dakamai tace eh dole in kwaci yancina haka kawai insha wahala inyi karatu,wani banza yazo ya siye karatu
Ran adams ya bace har wani daddagawa yake idonsa yayi jajur ya nunata dadan yatsa yace kinci sa,ar kinada sunan wacce nafiso a rayuwata,in ba haka saina karya bakinki
Kuma ki musa ki gani,tafiya suhailat tayi ta barsa a wajen,
Shima shiryawa yayi yanufi office dinsa
By
Marsal
[30/04 3:40 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
5⃣
By 2besties
_salma Ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(Marsal)*
®online hausa writters
◆bintace sai dube dube a dakinta take tana wallahi ba,a isaba duk wanda ya daukarmin sarkata yazo ya ajemin,anyi kadan wallahi tab,kokuma wlh inje in bankado asirin dazaiyi sanadiyar barin mutum duniya
Ummice tashigo tace ah binta maiya faru naketajin muryarki
Binta tace ba dole inyi ihuba,insha wahala namijin gaske yaban sarkar gwal kirar dubai wata shegiya tazo ta dauken,wallahi tun wuri a fitomin da abuna kafin namijin gaske ya dawo
Ummi tasaki salati kamar gaske tace ko sarkar naji suhailat tana magana a waya adakinta wai tasamu sarka zata kaiwa wata hajiya ta siya
Wani uwar ashar binta ta duro tayi wani juyi tace wallahi ko zan rasa raina saitaban sarkana,bari inje dakinta
Ummie taje ai tafita taje ta siyar saidai kiyi hakuri
Binta tace ina chab wallahi saita amoyomin sarkata
Ummi ta dinga zugata,zaune suke a babban falo suna jiran dawowar suhailat
Motar suhailat ce tayi parking a harabar gidan,fitowa tayi tana taku daidai cike dadin samun nassara a shara,ar da sukayi yau,
Intercom ta danna,kofar ya bude,shiga tagi hanyar dazai sadata da hanyar katon falo,wata mai aikice ta karbi jakarta tace anty sanda zuwa
Cike da mamaki suhailat tace dama akwai,masu aiki agidannan meyasa bama ganinku
Murmushi tayi tace ai maigida yace kar wanda yashigarmai wurin matansa,don bayason hada gulma, gaskiya yallabai yayi sa,ar mata irinki
Suhailat tace anjima zan kiraki kinji jeki abinki,
Tana shigo falon,binta ta tashi tasha daurin ture kaga tsiya,tace barauniya mikomin sarkata
Suhailat ta murtuke fuska tace wani sarka kike magana akai?
Binta tace au bazaki mikon sarkataba saina miki abinda bazaki manta daniba iye?
Suhailat ta matso kusa da binta ta buga kirjin binta tace ke mezanyi da matsiyacin sarkarki ku tuhumi kanku dagake har namijin gasken da abokiyar zamanki,
Wucewarta tayi yayinda binta ta cafko ta da niyyar marinta,rike hannunta suhailat tayi,tace ke ke karki kuskura kitabamin lafiyar fuska in ba hakaba sai na miki tabon da bazaki manta daniba
Da gudu binta ta nufi dakinta ta dakko wuka ta fito,tace wallahi koni koke indai bazaki bani sarkataba
Ummi tace ke suhailat ki bata sarkarta mana
Suhailat tace ummi baruwanki a wannan matter din
Ummi ta tashi tace da ruwana yar borin kunya barauniya
Suhailat tace au hademin kai zakuyi to bismillah
Kafin suhailat ta ankara taji an yanketa da wuka a hannu,jini ya fara zuba,kara suhailat tasa tace binta nikika yanka?
Binta tace au mamaki kike bari ma ki gani,kara yanka mata hannun tayi,kara suhailat tayi,yayinda itama tayu gudu taje ta dakko tangara ta bugawa binta a fuska,goshinta ya fashe jini ya dinga ambaliya,yayinda binta ta nufo wajen dambe aka fara,suhailat ta shake binta sai jibga take
Yayinda ummi ta bugawa adams waya gida ya rikice,yazo za,ayi kisa
Binta da taga za,a cuceta ta yi hanyar waje tatafi police station,yayinda suhailat ta kalli ummi tace saura ke wallahi duk sainaci ubanku
Ba,afi minti ukuba yan sanda sukaiso gidan suka kwashi,su ummi da suhailat akayi offishin yan sanda dasu
D.p.o ne yacewa suhailat keko?kina yar aiki a gidan yaron his excellency,mai yakaili kiyu fada da matarsa?
Suhailat ta murguda baki tace eh anyi din ku kasheni saiku huta donnataba matar namijin gaske saime dama niyyar kasheta nayi sai Allah baiyiba,tana zaman zamanta akan tace in kawo mata abinci,niki na dakko wuka na yanksta,kuma ni na sace sarkar gwal dinta.
D.p.o din ya daka mata tsawa yace ke au da abunda zaki sakamusu kenan,ai matarsa ta gayamin daga kauye suka dakko ki suka tufatar dake,don haka ina policawan suzo su shigar dake case aci ubanki
Policawane sukazo suka kama suhailat suka shigar da ita bayan kanta,sunata jibga,wata police din har wanka mata mari tayi
Ummice ta zauna tayi jugum jugum a kujerar office din,tana kallon binta da aka mata daurin bandage a goshi,tana tunanin makomarta jdan aka gano ita ta hada fadarnar.
Karan motocin namijin gaske sukaji,ummi ta dFe kirji,bintama ji tayi gabanta na faduwa
Suhailat dake tsare a cell,anmata raunuka tayi jugum-jugum sai hawayene yaketa malala a idonta
Namijin gaskene yashigo ranshi a bace,tundaga wajen office din ake kwasar gaisuwa har ya shiga,zama yayi a kujerar da yake fuskarta d.p.o yace d.p.o dukansu matana ne,meye dalilinka na kullemin matata iye d.p.o am asking you how dear you
Cikin inda inda d .p.o ya kwashe labarin karyar sa binta tabasu
Dafe kai namijin gaske yayi yace oh shit wallahi suhailat ba yar aikina bace matatace,kuma ita tatafi aiki,da kake ganinta bata shiga safgar kowa,sai an takalota,ummi da binta ya kamata ka tuhuma
Adams ya kalli binta ya wanke ta da mari jere har biyu yace wallahi kinban mamaki,adakinafa kikabar sarkar gwal dinki,ina kallo ta camera ummi tazo ta dauka ta fice abinta,amma kun nufi yarinyar mutane da sharri
Hakuri ummi take bawarwa
Rai abace adams yace officer arest them inaso suyi kwana shida a cell kafin lokacin matata ta warke,sumul inbata warkeba wallahi sai sunyi kwana talatin a cell ba damuwane bane
By
Marsal
[30/04 3:40 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
6⃣
*By 2besties*
_salma Ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writters
*Dedicated to Aunty fauzah*
◆jefasu binta akayi a cell yayinda aka fito da suhailat dake ihun ya kyalleta ta mutu a cell din,
Adams yayi murmushi yasan shagwabane ke damunta,
rikota yayi suka nufo waje tana ta kuka,bude musu miota akayi,hanyar asibiti suka nufa,akayi treating dinta sosai tasha wuya kuka kam har na jini takusa tayi,kwana uku ta warware aka sallamesu suka dawo gida
Suhailat ce tana ta danne dannen laptop dinta a tsakiyar kan gado,tana chatting da kawayenta
Kira taji dagawa tayi,muryar adams ne yace ina jiranki yanzu ki shirya tarbata yau
Tsaki suhailat tayi ta kashe wayarta gabaki daya,taci gaba da abinda take,
kamshin turarensa taji daga ido tayi ,cikin wani jallabiya yake,gashin kansa ya kara kwantawa luf luf,yayi matukar kyau
Mayar da kanta tayi kasa tana mallam meya kawoka dakina
Adams yayi murmushi yace nazo karbar hakki na, har wani hakki ne da kai lallai
Gadon ya hau tare da rufe laptop din da take danne danne Kaga malam lapiya ina aiki zaka katsen
Aikin da zakiyi yanxu yafi wannan muhimmanci tab wallahi baka isa ba kan suhailat tai wani abun tuni namijin gaske ya janyo ta da karfin sa ya rungume ta
kokarin kwantar kanta take amma takasa tuni ta fara kuka tana fusge fusge
Shikuwa gogan ya rikece hankalin sa yafara barin jikin ta saka makon wani ni'imtaccen kamshi da yake fita daka jikin suhailat
kan kace kwabo ya labubi bakin suhailat ya hada da nasa sun luluka duniyar ta ma'aurata
Kuka da cizo ba irin wanda suhailat batai tun tana iya magana tana masa magiya har ta hakura tai shiru sabida azaba ga karfin ba daya bane
Saida ya biya bukatar sa dan kan sa sannan ya haqura ya kyaleta wani wahaltaccen bacci ya dauke ta
Shi kuwa namijin gaske wani farin ciki ya tsinci Kansa gaskiya suhailat ta banbanta da binta ga ko ina na jikina kamshi fatar ta kuwa kamar ta jarirai kuma jaunyota yai ya rungumeta yana wanan tunani bacci me dadi yai awaon gaba da shi
kiran sallahn farko ne ya tashe shi,
kallon suhailat yai wadda take sharar baccinta a jikin sa shafa kanta yai sannan ya zameta a hankali ya shiga toilet sai da yai wanka sannan ya dawo dakin
A gefen ta ya zauna yana hura mata iska a kunne a hankali ta bude idon ganin ko wane tai yin kurin tashi sai dai gaba daya jikin ta ciwo yake haka ta koma ta kwanta tana kuka
Hannu ya kawo zai tabata da sauri ta doke hannun sa karka tabani mugu kawai wani murmushi ya saki sai kace bashi ba *namijin gaske* wanda kullum fuskar sa take a daure
Ki tashi ki wanka ki sallah bazan ba ka kyaleni
Koma wa toilet yai ya hada mata ruwan zafi sannan ya dawo
kan tai wani yunkuri ya sureta yai toilet da ita cikin bawo ya saka ta wani kara ta saki tare da rukun kume shi tana mugu ka cire ni kar na kone amma ina sai da ya tabbatar ta gasu sannan ya cire ta ya kuma hada mata wani ruwan
Ki wanka ki fito ki sallah ni janje masallaci harara ta sakar masa tare da murguda masa baki
Kofa yaja mata yai fice war sa
Sai da ta tsarkake jikin ta sannan ta fito doguwar riga ta saka ta tayar da sallah
Akan sallaya ya same ta durkusawa yai a gabanta kin tashi lapiya ban sani ba ta fada tana juya masa keya
Duk wani hanya da zabi yaga ya shawo kanta ya bi amma fir suhailata taki shi kuwa ya ma manta dasu binta da suke cell
By marsal💞[30/04 3:40 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
7⃣
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
_this page goes to *Aunty fauzah*thank you for ur prayer,we dedicate this page to you dear_
◆namijin gaske a office dinsa yaji kira daga office din yan sanda,sai yanzu ya tunama da wasu binta,dafe kirji yayi yace kash dama dady suhailat ya auramin kawai wallahi,yarinya sai uban ni,ima tamkar fanfo
Daga wayar yayi ya bada umarni asaki su binta su koma gida
Namijin gaske ya rasa yanda zanyi da kaunar suhailat,anya ba daukarta zaiyi su tafi amarci a london ba kuwa?
Suhailat ce kwance a falonta tana tuno abinda ya faru,sai murmushi taje ita kadai,gaskiya adams ya cika namijin gaske ya iya sarrafa mace,lalle kam saidai kuma bata sonsa,but haka zatayi manage har burinta ya cika tasamu wanda take muradi
Binta ce tashigo gidan tayi baki ta rame tun daga harabar gidan tafara ya Allah duk wanda yasa aka kulleni a cell Allah ya tsinemai albarka ta kalli ummi tace kekuma munafuka muje kiban tsarkata
Ummi tace dakata karki kara cemin munafuka gaki babbar dabba,dallah in baki saniba adams wayo yahada don yanason suhailat shiyasa ya kareta yadauki sarkan ya kai dakina
Binta tace eh fa wallahi muhada kanmu muci uwar shegiya,mushiga muyi wanka muci abinci tukun,ai dai ana haduwa a dinning da safe da yamma ko zamu hadu da ita
Namijin gaskene akan dinning yana jiran shayeeda ta kawo abinci,kwatsam saiga binta tashigo tasha wando da riga iya gwiwa taci kwalya,tadan zauna tace a a my love sannu da dawowa,hade rai adams yayi yace yauwa yaci gaba da latse latsen wayarsa,itama saiga ummi tashigo tasha doguwar riga yar gown tawani kashe daurin shoky,kashe mai ido tayi ta gaishesa dear sanda zuwa
Kara hade rai yayi yace lfy
Buga waya adams yayi yace malama kiyi sauri kizo kefe muke jira
Suhailat tace to sannu ubana in bani bazakuci abinci bane yau adakina zanci,inkunga dama kubiyoni kuxo muci,donni daidai cikina na girka tsayi tsaki ta kashe wayar
Ran adams yabace yatashi yayi part din suhailat yayinda ummi da binta suka matso kusa suka tafa,ummi tace ai yau mai kwatan shegiyar nan a wurin namijin gaske saiya shirya,mudai inta daku tayi laushi maje mu bada hakuri.
Adams yana shiga yaganta akan gado tana cin abinci,jallof din taliya da kifi,a katon plate,ko ina kamshi adakin,
Suhailat ta dago kai ta kallesa ta watsar ,kafin ta ankara ya hawo gadon ya warce plate din yace muba ,mutane bane iyeh
Murguda baki tayi tace aini ba baiwar kowa bace ai akwai yan aiki kuma akwai,matanka
Adams yace au kina nufin keba matata bace,kinacin sa,a fa kinada sunan wacce nafiso arayuwata
Harara suhailat ta dankaramai tace me ruwana ka hadeta ta koma ciki mana,kafin ta ankara ya aje plate din ya tsoma bakinsa cikin nata,yafara mata wassani masu kashe jiki
Cak suhailat ta tsaya ,takasa kwakwaran motsi,wasan nasa taga yafara wuce gona da iri,hankadasa gefe tayi dukansu numfashi suka fara maidawa
Yayinda namijin gaske ya kwanta rigigin ajan gado shi yasan yanda yakeji akan suhailat
Tsaki suhailat ta doka,tanajin haushin kanta da tasa aka dena game dinnan,kallonsa da tayi zai iyasa yanzu ta rinjayesa murya kasa kasa tace kaga mallam ka tashi ka dauki abincin ka fice daga dakina,ai yau naga ba kwanana bane
Murya kasa kasa shima ya amsa yace come on beb, cant you help me to decrease my temper
Murguda baki suhailat tayi tace inka isa kazo ka kwara kaga tafiyata toilet inka gama abinda kake ka fita
Tashi tayi da niyyar shiga toilet taji ya janyota ya mannata da kirjinsa,kokarin kwacewa ta dungayi amma ta kasa,
Haka ta bada kai bori yahau
Kuka take tayi,tana mai Allah ya isa kwando dubu,tana wallahi dole yau inyi wanka sau ishirin anzo angogamin cuta
Gatse dariyarsa adams yayi ,yace andaiji kunya kuma anji dadi duk bakin tsiwa jikake tsit
Tsaki suhailat ,tayi tace oh dai dolema inje inyi gwaji
Wanka suhailat tashiga tabarsa kafin ta dawo ya fita a babban falo taji hayaniya yana tashi
Fita tayi,namijin gaske tagani dauke da belt ahannunsa;ummi sai kuka take itama binta tana kuka
Ummi tace amma dai hakkina aka shiga dole inyi leke
Adams yace wallahi inbakiyimin shiruba saina babbalaki anan inga uban daya tsaya miki
Ahankali suhailat take taku ta iso wajen,tace haba namijin gaske ba girmanka bane dukan mace,meye aciki in sunyi leke ai matarkace ta sunnah ni
Ummi tace amma dai hakkina aka shiga donhaka wallahi bazan yardaba
Suhailat ta kallesu tace bari in baku example din darasin da mukayi,nan gaba basai kunyi leke ba kwayi kwas yanda ake tarairayan miji
Suhailat ta matso kusa da namijin gadke daya tsira mata ido,ta kashe mai ido cikin shagawa tace huhhhm soumate kallon ya isa haka,tsoma bakinta tayi cikin nasa tana masa hot kiss
Kusan sumewa binta tayi,yayinda ummi ta daddage iya karfinta ta kurma ihu subhanallahi......... an shigarmin hakkina
😂😂😂😂😂😂
By
Marsal
[30/04 3:40 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
8⃣
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
♠ wayyo Allah na shiga uku ana min karuwanci za'a kawance mini girki na wannan wane irin jaraba ne haka mutun ba girkin sa amma ana shiga hakki na
Basu fasa abinda suke ba sai ma wani salo sa suhailat ta fara yima namijin gaske
Ihu ummie ta kuma kurma ita kuwa binta baki ta saki tana kallon mamaki wannan shedaniyar in batai gaske ba zata Kwace masu miji su zama borori tun kan aje ko ina an fara nuna musu kissa a fili
Namijin gaske daukan suhailat yai basu zame ko ina ba sai turakar sa suna shiga suhailat tai zame jikin ta cikin tsiwa to ya isa haka cika ni ina da abun yi
Akuwa baki isa ba kin tsokano ni kuma Kice baki san zance ba to ae naga ba aikina bane kaje wajen wadda take ihu akan ka ta fito tayi bangaren ta tana fitowa parlo tagan su nan take ta canja tafiya tana wani gwalli
Binta ce tace wa ummie da ta cika tai fam Ke wallahi sai munyi da gaske wannan karamar karuwan kina ganin abinda tai masa ba kunya ba tsoron Allah
Ni nasan me zanyi bar ni da ita ummie ta kwafa ta shige dakin ta, ta fara kurbu kurbe da tushe tushe wai dan ta jawo hankalin namijn gaske😜
Yamma cin ranar ya fito suna zaune a parlo ummie da binta suna yada maganganun su
ita kuwa suhailat tana aikin ta a system kallon su yai daya bayan daya binta ce take ta wani kashe masa ido ita kuwa ummie tasowa tai tazo honey barka da fit....kan ta karasa ya katseta
kallon suhailat yake wanda ko kallon sa batai ba ya karasa kusa da ita yace kin ga dagowa tai ganin su ummie suna kallon ta yasa tasaki wani murmushin kissa
Na'am darling zoki raka ni gate mana tashi tai ya rike hannun sa suka fita dasuri ummie ta tashi tsaye ta sha gaban sawai me kake nufi ne ehee banza yai da ita suka huce
Motor park yaje inda wata dalleliyar moto yaje jagour baka sai sheki take kamar mudubi its ur gift ya mika mata keys din ita kanta tai mamakin dane shi tai tana murna kai amma naji dadi nagode
Kut me le shi binta ta fada wato shine y bata kyautar mota ni kuma ya bayan wanann sakar tab din Jan lallai ma namijn gasken nan
Ita kuwa binta da gudu ta shiga ciki dakin ta ta koma ta fara safa da marwa tana neman mafita
Wani tsumin ta tajanyo murmushi ta saki sannan tace namijin gaske in nasha wannan sai dai kaban kyautar gida kila ma ka hada da mota ta kafa kai ta fara kwankwada cikin karfin gwuiwa
Suhailat da Adams suka shige suka bar binta a tsaye
Adams ne a dakin sa yana ta juyi da tunani ina ma suhailat ce kadai matar sa ba wannan yari yuyu yu din yana wanann tunanin ummei ta shigo cikin wasu shaidanun kayan bacci tana wani kwarkwasa kallon ta yai sannan ya kau da kansa
A ransa yana tunanin wannan wace macece mara aji uhmm dear ya kake a dakile yace lapiya
Gaf da shi ta matso ta fara masa wani salo daamn a kusa yake tun nan take ya biye mata amma ina sam ba daya bane da suhailat
Cikin ta kaici ya shiga toilet ya bar ummie tana karairaya a bed..............
By marsal💞
[30/04 3:40 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
9⃣
*by 2besties*💞
_salma Ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
_this page is dedicate to our fans,thank you for ur support and caring_
Namijin gaske ya shigo ya dakamata wani uban tsawa yace ummie get out of my room idiot
A firgice ta tashi har tana tuntube,tasa kayanta tabar dakin ta kuka da alwashin neman kawarta suje wajen boka
Tsaki namijin gaske yayi ya danna wayarsa yakira suhailat,ringin uku bata dauka,aje wayar yayi akan gado yace oh shit wannan yarinyar tana da matsala wallahi,bata zuwa dakina saidai ni in bita
Tashi yayi ya zura jallabiyarsa ya nufi part din suhailat dake kan gado tana danna system dinta
Bata lura mutum ma yashigoba,kamshin turarensa ya bayyana dago da kyawawan idonta tayi tana kallon kyakyawar fuskarta daga bisani tayi tsaki taci gaba da aikin da takeyi
Hawowa kan gadon yayi,ta matsa gefe tana waikai wani irin bunsurune?😳
Tun danamijin gaske yazo duniya ba,a taba mai zaginda yaji zafiba kamar haka,da karfi yajawo gashinta datayi fakin da ribom,tsabar zafi ta saki laptop din yafadi akan tyles din ya tarwatse
Suhailat ta fusata itama ta daddage ta tsinkamai mari,tana wallahi saika biyani system dina kutumar ubanchan,tab lalle bakasan wacece suhailat bane
Namijin gaske ya dafe kunci lamarin yarinyar nan anya ba shafar aljanu aciki kuwa
Tashi suhailat tayi ta dauki agogon bango ta kwalamai,tana wallahi yau saika biyani system dina,kasan meye aciki
Fashewa goshin adams yayi, yayi danja malutu ya fito,tsayawa yayi yana kallon abin mamaki yanda take ta masifa kamar tasamu yaronta.
Daukar fillo tayi da niyyar makamai,adams yayi kokarin cafketa ya rungumeta kankam
Fusge fusge take tana kuka tana sakeni mugu azzalumi kawai,wallahi banason aurannan.
Adams kamar yayi kuka yakeji tunda yazo duniya bai taba tsintar kansa abakin cikiba irin yauba.
Cikin murya ahankali yace suhailat inkinawa Allah da annabi kiyi hakuri,in Allah yayarda zan siyomiki laptop guda ishirrin,kuma namiki Alkawarin bazan sake nemanki basai randa bukatarki ta tashi kya nemeni da kanki,suhailat kiyi hakuri kinji,
Jikin suhailat yayi sanyi sai shesshekar kuka take da ajiyar zuciya,
Tashi adams yayi yace nabarki lfy suhailat,duk abinda kike nema zaki iya kirana
Ritse idonta suhailat tayi kamar tace ya dawo amma ina baza iyaba.
Yana fitowa ya tarar da ummi da binta a falo,wakar dankwali yaja hula suke tayi,ko kallonsu namijin gaske baiyiba yayi wucewarsa bangarensa,ya shirya dan akwatinsa,ya rubuta wasika yar guntuwa ya ajiye,akan gadonsa
Airport din abuja ya nufa airport din abujah ya yi biza,ya nufi kasar malaysia,zuciyarsa cike da kunci da kyewar suhailat,gwanda yayi nesa da ita,in Allah yabashi mata a malaysia yayi auransa,ya manta da wata suhailat
By
Marsal
[30/04 3:40 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
🔟
*by 2besties*💞
_salma Ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writters
_this page is dedicated to *hauwa abubakar(mamee)*ur message has been delivered to us we have seen it,thank you so much dear_
Washegari,binta tayi bangaren namijin gaske,danufin dubowa ko lfy,tana shiga taga kayansa a hargitse ,mamakine ya cikata namijin gasken da bayaso ko tawul yagani a hargitse
Paper ta gani akan gado
Daukawa tayi tafara karantawa kamar haka;
_salam zuwa ga matana_
_inaso ingaya muku nayi tafiya bazan dawoba sai nanda wata hudu masu zuwa,sai burina yacika zan dawo,bakuda matsalar komai ,komai kuke bukata akwaishi acikin gidannan,kowa zan tura mata miliyan shida a account dinta_
_daga naku adams(namijin gaske)_
Rangada guda binta tayi cikin farin ciki ta nufi bambam falo rike da takardar ahannunta tana wakar sama mata
Ummie ce tashigo fallon rike da hollandia a hannunta tace keko binta samuwace kike wannan rawar?
Binta ta kara rangada guda tace yaya bazanyi murnaba keko takurarre ya tafi,yabar mana dukiya,sai yanda muka juyata iyeh karanta takardar nan kiji.
Da sauri ummi ta karbi takardar takaranta,ihu tasaki wanda yayi sanadiyar fitowar suhailat daga kitchen dinta ta nufi bambam falo ,kallon kallo aka fara tsakaninsu
Yayinda binta ta fashe da dariya tana Allah sarki gatan wata ya tafi,zamu nadi na banza
Ummie tace aini saina kashe yarinyar nan wallahi kuma in binneta a gidannan
Tsaki suhailat tayi tace inkun kasheni yau gobe wazaku kashe,aini nama ji dady wallahi
Kusani ni bandamu dana mijin gaskeba shiya damu dani yaketa bibiyata.
Dungure mata kai,binta tayi,itama ummi ta dungure mata kai suna wakar *cry cry baby let me see ur husband*
Binta tace kuma daga yau tunda nice uwargida sai abinda nace,ke suhailat daga yau da kowa ya dinga wanki da kansa,.kuma kawanda yakai karan namijin gaske wai yayi tafiya inba haka wallahi sai na sa an kashe mutum,ko danginmune sukazo muce yana wajen aiki
Zaro ido suhailat tayi tana kwallah tace aiko agidanmu ban taba wankiba balle kicemin inyi wanki da kaina
Binta tace oh dai kekikasani,dole kiyi,kuma dole kibi umarnina kinji ko?
Suhailat daki tayi da gudu tanata kuka,nashiga uku wazai magancemin matsalar nan ,tasan su binta tsaf zasu iya kasheta inta fada gwanda ta tsuke bakinta har Allah yasa ya dawo,wanka tafada ta fito ji tayi cikinta na ringin,gashi sha,awar fried rice takeyi,shiga kitchen dinta tayi,ta dora ruwan shinkafa agas
Ummice tashigo dauke da tukunya guda biyu a hannunta,tace ke malama sauke abincinki,zan dora abincina
Murmushin takaici suhailat tayi tace haba ke kuwa duk kitchen dinki bai ishekiba ,sai kitchen dina gaskiya kiyi hakuri banson neman fitina yunwa nakeji
Ummie ta wani danno ashar tace ai bada kudin najadun aka siya gas dinnan ba don haka anan naga damar yi bakida damar hanani barima ki gani.
Ummie ta aje tukwanen hannunta ta sauke na suhailat,ta dora nata tana bala,i
Suhailat bata tanka mataba,ta dauki tukunyarta azuciyarta tadau alwashin jure duk wulakancin da zata fuskanta indai akan namijin gaskene dole ta jure
Ajewa tayi agefe ta fita daga kitchen dinta ta wuce parlour dinta ,dawowa kitchen din tayi tabude fridge dinta tadauki cake da hollandia,ta kulle
Ummi ta sheke da dariya tace wayyo ni hhmmmmm gatana ya tafi,.
Suhailat bata kulataba tawuce bedroom dinta ta kwanta tanacin cake din hawaye yana zuba a idonta,shikenan tayi missing din dumin jikin adams,muryarsa,tarairayarsa
Rungumar fillo tayi😔tana kuka
Bayan kwana biyu,binta tana zaune da kawayenta an baje a babban falo anajin kida anatacin duniya da tsinke,sai ihu ake gami da shewa,ga lemuka dasu barasa da syrup iri iri,an baje sai shaye shaye ake,harda ummi
Suhailat ce tafito fuskarta da makeup,tasha kyau,ta sanya hijjabi har kasa,ta rataya jaka,
Toshe hanci tayi sakamakon warin sigari dataji,
Yanmata sunfi ishirrin afalon,ummie dake kwance akan cinyar wata tace ke ina zaki
Suhailat bata kulataba tayi ficewarta,tana isa harabar gidan taji amai ya taso mata,kwarawa ta dingayi,ba kaukauta,yan aiki sukazo suna mata sannu
Dakyar ta dawo hayyacinta,ta kallesu tace sannu nagode,kuskure bakinta tayi
Takalli dayar yar aikin da ranar ta mata magana tace pls zaki iya rakani asibiti wallahi jiri nakeji,kiramin direba
Dasauri direba yazo wajen,ya tukasu zuwa asibiti
Suhailat tanashiga asibitin,taji alert miliyan takwas ya shiga account,din daga,namijin gaske
Suhailat tayi murmushin takaici tashiga layin masu jiran ganin likita,kusada wata hamshakiyar mata tazauna,fara da ita gadan hanci ,hado ido sukayi da matan,matan ta matso tace baiwar Allah sannu ko?wallahi kin burgeni ni sunana hussaina ahmed,ina da aure anan abuja,kwanan nan nayi aure ga kanol,ni yar adamawace wallahi bansan kowaba a abuja zamu iya xama friends
Murmushi suhailat tayi tace ayya sunana suhailat ina aure a abuja nima bansan kowaba
Munsanyar number sukayi,suka dinga hira da bawa kowa adreess
By
Marsal
[30/04 3:40 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
11
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
⚫suna hira har aka zo kan suhailat office din doctor din ta shiga ta zauna ur welcome Mrs Adams (Namijin haske) murmushi yake tai me Ke tafe da Ke
nan tai masa bayanin abunda Ke damunta wata nurse ya kira yace taje da suhailat ai mata gwajin fitsari
Jin abinda ya fada tai saurin kallon likitan wanda Ke mata murmushi nashiga uku 🙆 ta fada a ranta haka ta tashi suka shiga wani lab ta bayar sannan ta dawo office din doctor
Kusan 10minutes saiga nurse ta dawo da sakamakon karba yayi yana dubawa fuskar sa da murmushi ya dago ya kalleta congratulations
Ban gane ba suhailat ta fada kina da juna biyu cikin firgici ta tashi me ganin yana mata wani kallon ne yasa ta zauna tana maida numfashi
Ya naga kin tsorata aa bakomai ok tom gaskiya da wuri zan ma namijin gaske wannan albishir din dan nasan ba karamin kyauta zan samu ba
Am doctor dan Allah ina neman alfarma tame fa karka fada masa ka bari ni zan fada masa zanyi surprising nasa kawai Kice baki so na sami kyauta ah ba haka bane,
To yadda kika ce hk za'ae nan ha rubuta mata magunguna ga wannan kidinga sha zai kara miki karfin jiki sannan kuma zai hanaki yin aman da kike yi
Sannan kicire duk wata damuwa dan kare kan ki da abinda Ke cikin ki fadawa wani halin dan ba wuya me ciki ta samu hawan jini to nagode nan ta tashi ta fita
Inda yai dai dai da fitowar hajiya hussaina daga daya office din
Yar uwa har kin fito eh ta fada yayin da tai saurin share wata kwalla da ta fito mata ah yana gan ki cikin damuwa ece dai lapiya hussaina ta tambaya
Shiru tai mata yayin da ta fara tafiya haba dan Allah ki tsaya kimun bayani wllh jinki nake kamar wata yar uwa ta tsayawa tai cak suhailat tayi har ta karaso kusa da ita
Kama hannun ta tai suka zauna a wasu kujerun gini dake haraban asibitin
Me ya faru yar uwa ina so ki dauke ni kamar wadda kuke uwa daya uba daya nima haka na dauke ki wallahi ki yarda dani
Haka likita yace ina da ciki to menene bakin ce kina da aure ba eh to da matsala ne
Ya salam kin ga yanxu wannan maganar ba ta nan bace in na koma gida mayi waya ko kuma inna sami lokaci na zo har gidan naki
Kiyi haquri ki kwantar da hankalin ki kinji sai da hussaina taga hankalin ta ya kwanta sannan ta tashi ta rakata pharmacy ta karbi magani sannan ta rakata har mota sannan ita ma ta tafi
A mota tai nisa a cikin tunani wai yau ita Ke da cikin namijin gaske amma baya nan kuma be san dashi ba gashi tunda ya tafi koda wasa bata kira shi ba shima kuma be neme ta ba daman yace sai ta neme shi da yana nan bata san irin kulawar da zai bata ba
wayyo ni suhailat its my fault
yanxu ya zanyi ga sharrin wannan mugayen matan nasa da ya tafi ya barni da su wasu hawaye ta share wanda yai dai dai da tsayawar su driver ne ya fito ya bude mata kofar mota
Hajiya mun kara so sai da ya kuma maimaitawa sannan ta Ji sannun hajiya Allah ya kara sauki Ameen kawai tace tai ban garen su
Yanda ta fita ta barsu haka ta dawo suna nan sai ma wasu shegun da suka kuma zuwa
Hayaki da wari ne sukai mata welcome da kyar ta iya sallama dan ita ma ta zama dole bata jira amsar su ba dan daman Tasan ba lallai Tasami amsar ta ba
Kan ta ne yai wani irin sarawa da sauri tai hanyar dakin ta har an dawo daga barbadar ummie ta fada maji magani daman yawon banza ake ba zuwa aiki ba munafuka
Wata daga cikin kawayen suce tai magana lallai ku wannan kuka tsaya kuka zubawa ido Tav wallahi in ba kuyi da gaske ba sai ta fitar da ku
Ae da kishiya ta ce wallahi da tuni da dade a bola.
kuka da amai ne suka tawo mata lokaci daya da gudu tai toilet ta fara kwarawa ba kakkautawa............
By marsal💞
[30/04 3:40 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
12
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
⬛ gaskiya binta baki da wayo Ashe karfa girman naki ya tashi a banza wata daka cikin kawar tasu ta fadi haka
Uhmm to mene abin yi au har sai kin tsaya wani tunanin abinyi akan wannan dube ta fa natural beauty fara kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa
Ke dahallacan ki fadi abinyi kin tsaya kin wani yabon ta ummie ta fada
Wallahi da namijin gaske ita ya fara aura ko kallon ku bazai ba bare ma dayake kyautar ku aka bashi wai naja wannan wane irin cin fuska ne haka ki fadi abin yi kintsaya kina wulakanci
Gaskiya fa take fada muku amma kuna ta wani ganin laifinta Ke wallh sai kun tashi tsaye musamman Ke binta da kanti ne ya taimake ki ba wani kyau gare ki ba amma badan haka ba ko a mai aikin namijin gaske bazaki zo ba
Uhmmm ae in da ace ni namijin gaske ya aura wllh ko Ke bazan bari ba ta nuna ummie da hannu
oho sai yanxu nagane abinda kike nufi kina bakin ciki da kishi ko to kwalelen ki wllh
Ya isa haka binta ta fada yanxu ya za'a ku matso kuji kar muje ko ana mana labe suka kwashe da dariya
To in taji akwai abinda zata iya ne wallahi ynx sai mu hada mata jini da majina nifa natsani yarinyar wallh zan iya komai dan naga ta bar gidan nan ummie ta fada
haka suka cigaba da hirar su duk akan yadda zasu cuci suhailat
Ita kuwa suhailat tana shiga daki da gudu tai toilet ta fara sheka amai
amai har ta hanci yake fito wa ba karamin galabaita suhailat tayi ba
Ga cikin ta wani murdawa yake kamar zata mutu sabida azaba wani kuka ne ya taho mata da kyar take yi a haka ta rarrafa wajen sink ta dauraye bakin ta sannan tayi wanka
Daki da nufa ragowar cake ta gani nan ta fara ci ba kakkautawa kamar ba suhailat ba yarinya yar gayu abinci sai ammasa yanga
Sai da taji ta koshi sannan ta hakura wani bacci ne ya dauke ta anan kan tayels
Sai wajen la'asar sannan ta tashi da sauri ganin in da take kwance jikin ta duk yai tsami sabida rashin sabo
Sallah tayi sannan ta duba wayar ta missed call ta gani hajiya hussaina ta kira ta da sauri ta bi kiran
Bugu daya ta dauka yar uwa Allah yasa lapiya na kira ki baki picking ba wallahi bacci nayi Ayya sannu yawwa ya jikin naki da sauki sai sannan ma ta tuna da ko maganin ta bata sha ba
Yawwa ya ake ciki yanxu hajiya wallahi ina cikin matsala sosai subhanallah me ya faru nan ta kwashe abinda ya faru sannan ta fada mata irin zaman da suke da su binta
Ba karamin tausayin ta hussaina taji ba har sai da tai kuka
Hajiya ki taimaka wallh bana son cikin nan zubar dashi zan je nayi
Kul na kuma Ji kin fadi wannan maganar yaza'ae Allah yai miki kyauta Kice baki so kin ga kin masa butulci
Kuma kije garin zubar war ki mutu inkije lahira kice ma Allah me?kin aika ta Laifuka har biyu ga kisan ran banji ba ban gani ba ga kuma sabawa mijin ki
sannan kuma in mijin naki yaji haka baka ramin tashin hankali zakuyi ba kuma kinga kince laifin ki ne yasa ya bar kasar
To yanxu ki cigaba da shan maganin ki ki dangana kar ki bari su sani balle suyi miki wani abun kin Ji ki dage da addu'a Allah zai taimake ki
Ko a gidan ku kar ki bari a gane kina cikin matsala in ma wani abun ya dame ki kai fadan in Allah ya yarda zan taimaka miki kuma zan zo sabida akwai abinda nake son fada miki wanda bana waya bane
Ni fa nagaji da zuwa aikin ma zanje na rubuta resigning latter a'a ki cigaba da zuwa shima zai dinga debe miki kewa kamin lokacin da zaki haihu
Ki haquri kinji yar uwata tom nagode nan sukai sallama tana jin dadi haduwa da hussaina
Haka ta cigaba da zama a gidan kamar wadda take a prison...
By marsal💞
[30/04 3:40 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
13
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online Hausa writer
🔷duk da tana cikin damuwa hakan be hana sawa cikin yai mata kyau ba sam be fito ba sabida gaba daya jikin ta ya bi ta kara fari sosai
Ummie ce zaune a parlo yau ba tari en iskan kawayen su tana zaune suna hira tana sa nailpaint a farcen kafarta suhailat ce ta fito daga kitchen tai dakin ta
Wai biki lura da irin kyaun da wannan shegiyar take kuma yi ba binta ta fada uhmm na lura mana wayan abinda take yi a wajen isakancin nata baki ga yanxu kullum tana hijab ba haka sukai ta zagin suhailat baiwar Allah
haka hajiya hussaina ta cigaba da taimaka mata da bata addu'o'i
Ko office zata hijab take sawa wanda Ke zuwar har kasa
Yau da huri ta gama aiki a office 12:15 waya ta ciro ta kira hajiya hello sis kina gida ne eh to ganin zuwa gidan hajiya hussaina ta huce
Sun Ji dadi ganin juna duk da hajiyan tana zuwa gidan sai da taci abinci ta huta yawwa kinga sakon dana Ke son baki wannan
man zaitun ne da na habbatssauda sai man kuma man hulba gasu nan a hade ki dinga sha sai kuma wannan zumar kin ga wannan hadin ana so mace ta dinga sha in tana da ciki ko bayan ta haihu ta dinga sha tana bawa baby dan kariya daga shaidanu a Islamic chemist na bayar aka siyo miki nagode hajiya
Sannan kullum in Kin tashi ki dinga karanta ayatulkursiyu da falaki da nasi kafa uku kina tofawa a hannun sannan ki shafa akan cikin kin Ji godiya sosai tai mata har kuka sai da tayi dan sai me son ne zai ma haka
Sai bayan sallar la'asar sannan ta tafi gida wanda yazl zaman mata tamkar kurku ku kullum sai tayi tunanin namijin gaske
Haka in zata kwanta sai ta kunna suratul baqrah sabida muna nan mafarken da take yi
Duk wata tsiwa ta suhailat yanxu ta daina in kaganta baza kace ita ce ba dan tazama musulumatun muminatun Allah sarki yanxu ba wannan shagwabar da sangar ta,
Da da bata ta wani aiki sai na duba loptop amma yanxu kullum tana rike da kur'ani ko carbi duniya kenan
Su binta kuwa an dauki aniyar ganin bayan suhailat yauma gidan wani boka kawar su zata raka su tafiya sukayi har suka isa wani ungurmin daji bakin kirin kusa da wata bukka suka karasa yawwa munzo naja ta fada amma fa da rarrafe akae shiga haka sukai ta rarrafa wa har suka shiga
Wani mugun bakin bamaguje ne a zaune bakyaun ganin kirari ta fara yi masa wata mahaukaciyar dariya ya saki
Ummie ce zata magana katsae ta yai na san abinda Ke tafe daku akan kishiyar ku ne eh boka me kuke so ayi mata batare da tunanin ba sukace muna so a haukartar da ita
Wata dariya yai wadda su Kansu sai da suka tsorata nan yai surkullen ta yace zan tura mata bakin aljani yau daddare godiya sukai masa sannan suka ciro damun kudi suka aji suka fita
Mota suna ta dariyar mugunta gobe wata sai bola haka suka dawo gidan cike da farin ciki a falo suka ganta ah'ah kanwar mu yau an fito shan iska ne kallon su tai cike da mamaki dan tunda take da su basu taba yimata magana me dadi ba
Daki ta shige ta barsu ana suna dariya,ko da dare yayi kunnan wayar ta tai ta fara sauraron karatun har barci ya dauke ta cikin baccin tai wani mugun mafarki da sauri ta tashi bakin ta dauke da addu'a kara volume tayi sannan ta cigaba da barcin ta
Da kyar aljanin da boka ya turo yasha sakamakon karatun ta yaji yana fita daga dakin yayi qardamar shiga ya kone da kyar ya koma wajen boka a kone
Wata uwar ashariya boka ya saki ganin yanda aljanin sa ya dawo lallai wanan zasu batan aiki da somawa da iya wa to bazan kuma yi Musa ba aiki ba
Washe gari ta tashi tsaf da ita tai shirin ta kamar kullum ta fito da niyar fita office
Tun dare sun binta suke baza kunne suji ta inda zata fara ihu dan kofar parlo ma a bude suka barta
Sai kawai ganin ta sukai ta fito zata aiki..,......
By marsal💞
[30/04 3:40 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
1⃣4⃣
*by 2besties*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writer
🔶sakin baki sukai suna kallon ta har ta fita basuce komai ba sun kasa tabuka komai ganin ta lapiya lau
Waya binta ta dauka ta kira naja kawar ta ya akai ta fice ko wane irin fice wa gata nan ras har ta tafi aiki
Me kike nufi kar dai Kice ba abinda ya same ta eh mana to ya akai be mata komai ba
Bayan boka kankat ne wajen iya aiki amma wannan abun akwai abin mamaki amma ganin nan bari na karasa so
Zaman jiran ta suka zauna suna yi sai bayan wani lokaci me tasho sai ga naja Ke ina kika tsaya muna jiran ki baki zo ba
Ah wajen harka ta naje inda zai fishshe ni to yanxu mene abinyi sai kin fada Ke muke jira muji yadda za'ae ummie ta fada
Ina shegiyar take ta tafi barbadar ta Kila ma yanxu ta dawo dan lokacin dawowar ta yayi
Suna zaune suna kulle kullen su ta dawo ban garen ta ta nufa wanka tayi sannan ta saka riga mara nauyi wanda ya bayyana cikin ta wanda take wata biyar fitowa tai zata shiga general kitchen
Gaba dayan su mikewa sukai cikin rudu da tashin hankali ganin suhailat da ciki har ta dawo tashige suna tsaye cike da mamaki
Kut me lee cee kunga abinda na gani wannan shegiyar kamar ciki ne da ita
Bura uban can wallahi baza ta yihu ba binta ta fada cike da masifa
Wata sabuwa yaushe ta samu ciki har yai kwari bamu sani tab kika sani ko a wajen yawon isakancin ta ta samu
Yanxu mene abinyi ga aikin boka ma sam be tasiri akan ta
Wata magana naja ta rada musu haka zaku yi kuma sai kun hada fa da dabarar ku ta mata sannan zaku ci nasara
Bakin ciki goma da ashirin ya hade musu
*Malesia*
Shi kuwa namijin gaske tunda ya tafi malesia gaba daya baya cikin nutsuwa hankalin sa gaba daya yana kan suhailat kullum yana cikin kewar ta
Da yammaci ya fita wajen shan iska idon sa yakai kan wata buduwar cikin sauri ya tashi kare mata kallo yai tana kyau sosai amma bata kama kafar suhailat ba haka yasa bodyguards Nasa sukai masa binciken wace ita
Khalisat yarinya ce buduwar yar boko baban ta hamshakin me kudi ne,
Namijin gaske ne zaune a palon gidan su yana jiran ta tun shigowar ta take kallon sa gaskiya wanna guy din ya hadu zama tai sannan yai mata bayanin kansa har ya sanar mata yana da mata uku in ta aminci zai aure ta ta zama ta hudu nan ya zube mata kudi yace sai yaji ta bakin ta
Ko da khalisat ta fadawa Maman kinyarda tayi tace yar ta bazata gidan kishiyoyi ba ae ita kadai ce a wajen baban ta ganin irin nacewar da tayi yasa ta haqura ba dan taso ba
Haka aka fara shirin bikin namijin gaske da khalisat yar bokon gaske
Ban gare suhailat kuwa kullum a tunanin namijin gaske take sam ynazu bata jin dadi gashi tana masifar kewar sa mudai marsal munce yarinya kin fara so namijin gaske❤
Zaune suke a parlo har suhailat sabida zaman dakin ya ishe ta suna zaune suna yarda mata haibaici ita kuwa azkar ne a hannun ta tana karanta wa
Gaba daya hankalin su ne yakai kan TV din da suke kalla sanawar auran namijin gaske suka gani sun girgiza da jin zance lallai ma namijin gasken ne munafuki ne ummie ta fada
To mene aciki ita ma tazo da kafarta zata fita binta ta fada ita kuwa suhailat hankalin ta ba karamin tashi yai ba
Suna cikin wanna halin suka ga ana shigo da jakun kuna ne irin na kayan lefe set uku (36) brown 12 an rubuta binta a jiki,
Black 12 ummie, sai kuma pink 12 an sa suhailat
Wannan kayan fa haka aka ce na kawo muku sannan kuma ya mika musu wata takarda wanna yace a baku......
By marsal💞
[30/04 3:40 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
1⃣5⃣
*by 2besties*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writer
🔴binta ce ta warce takardar wasika namijin gaske ya rubuta
_Assalamu alaikum ya kuke fatan kuna lapiya ga wannan kayan naku kowacce ta dau nata na fadar kishiya ne kuyi haquri ban gaya muku da wuri ba amma zan dawo nan da one month tare da amarya ta_
Wurgi tai ta takardar ummie ce tai saurin dauka ta karanta nan taje ta fara ashariya suhailat ce ta dauka tana karanta wa tai daki da gudu tana kuka shewa suka saki sannan suka tafa ahayye kishi kumallon mata
Anya kuwa ba wannan ne nawa ba kuwa ummie ta fada tana shafa wanda aka sa suhailat lallai omai
Sai an nuna mana banbanci
Gaba ta kai mu ni Bari na kwashi nawa binta ta fada
Wanda batasan name ne ba
Kishin namijin gaske kike yarinya
Kowacce ta kwashe kayan ta tai daki Saura na suhailat wanda ta rasa me Ke damun ta da sai Washe gari sannan ta fito da yake weekend ne
Hussaina tai ma waya tace in ba damuwa dan Allah ta zo tom shikke nan bari yara su tafi islamiyya sai na tawo tom sis
Sai da hussaina ta zo sanan tasa en aiki suka shigarwa da suhailat kayan ta daki
Hajiya ni ki tafi dasu bana so aa baza ae haka ba kiyi haquri ki barwa Allah kiyi addu'a Allah yasa ta gari ce
Haka tai ta bata shawara sannan ta bude kaya ne aka zuba masu masifar kyau da tsada dibarwa hussaina tayi ta bata aa bazan karba naki ne dan Allah ki karba ni wallh bansan me zan dasu ba ina da kaya ko na lefe na ma ko 25/100 Banyi amfani dashi ba
Ranar daurin aure da daddare momyn namijin gaske ce tazo tayi musu fada sannan sosai kamar gaske suka nuna mata sun Ji Ke binta kece Babba kiyi haquri dasu ku kuma ku bata girma yanda in amaryar tazo zaku Ji dadin zama
Dakin suhailat suka je ta kuma yi mata nasiha,my daughter yana ga kamar kina cikin damuwa bakomai momy kawai bana jin dadi ne to ki dai kwantar da hankalin ki
Wannan amaryar badan baya son ki ya auro ta ba tom.hajiya nan tai masu sallama ta tafi tayi farin cikin ganin suhailat da ciki amma ya akai Adams be fada mata ba kika ko kunya yake Ji gashi yanxu zata yi jikan fari haquri me tarar da rabo
Wani kuka suhailat tasaki gashi ba me rarrashi haka ta gaji ta rarrashi kanta tayi shiru
Bata san irin wadda ya auro ba ko ita ma irin su bintar ce oho Allah kai min jagora da wannan bacci ya debe ta cike da tunanin namijin gaske...........
By marsal
[30/04 3:40 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
1⃣6⃣
*by 2besties*
_salma Ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writters
💓kuka suhailat take,dakko laptop dinta tayi,sakkoni tagani na abokan aikinta kala kala,ana gayyatarta zuwa kotu domin magance wasu matsala,tsaki tayi tace inji da matsala ko dataku ta tura musu batta da lafiya,
Tashi tayi,da niyyar fitowa fallonta,su ummie tagani azaune suna mata kallon hadarin kaji,ji tayi sulbi ya kwasheta tafadi tim rubda ciki,kara tasaki yayinda suka kyalkyale da dariya binta tace naki wasane yarinya ai sai mun kawar da dan iskan cikinnan mu huta da takaici
Dakyar suhailat ta iya tashi ta kallesu tana hawaye tace binta kuji tsoran Allah,ba wanda yasan gobe meya kawoku falona,bayan kuma kunada falon abunnan yafara ishata dunkunga ina muku shuru,wallahi da dane bawacce ta isa tamin kallon banza ban saita mata hanyaba
Shewa gami da guda suka rangada ummiee tace iye nanaye idon mage ya waye ai dole ki dawo da halinki saboda gobe gatanki zai dawo to albishirinki ki bude idonki kiji,yana dawowa saikin shiga azaba mai tsanani wannan cikin da kike takama dashi sai nanda shekaru uku zaki haifeshi haka zakita yawo dashi karshema ya zama ajalinki
Suhailat ta kallesu tayi murmushi mai ciwo tace Ai Allah baya bacci balle gyangadi,kuma inji in gayamiki adu,ar nakeyi kullum insha Allah bazai fadi kasa banzaba,kema albishirinki nan da watanni hudu zakiji kukan baby acikin gidannan
Binta tace ai saidai ki haifi shege a mai duguri badai gidannanba,ai keda namijin gaske saidai kallo anesa
Suhailat tace a,uzubilllah Allah ya rabani da zuwa gidan boka,shiga bedroom dinta tayi ta kulle gagam
Ba zaginda ummi basu mataba amma tayi lif adaki tana tunani da son jin kamshin turaren namijin gaske
Hajiya hassanace tashigo gidan da tsakar rana ,ummie ce zaune a falo ansha kwalya ana jiran,namijin gaske,wani wawan,harara ummie ta daka mata tace uhhmmmm su kaza,da kalar dangi,uhhhhmmm nida karuwa
Hajiya hassana hartayi gaba tadawo baya ta murtuke fuska kekem tace ke dawa kike?
Ummie ta tafa hannaye tace kajini da mata dake nayi magana,wayasan ma mekuke aikatawa kuda suhailan ?
Ran hajiya hassana ya bace tace hmmmm duk dai cusa kaina miji bayasona na nace na nace,naje gidan bokan abu yaci turo oh shiyasa naketa wannan haukar ,bari in roki Allah ko nasamu haihuwa,af ashe nasha kwayoyi sunmin illah,kash nida haihuwa sai ikon Allah,tayi tsaki tashige bangaren suhailat
Maganar tawa ummie zafi matuka,harda dan zubar da guntun hawayenta,tana tunanin mai zatayi tahuce takaici
Jerin motoci da jiniyane suka cika harabar gidan da alamu,namijin gaske ya sauka.
Suhailat ce tafito daga wanka gabanta sai faduwa yake,ta kalli hassana tace gaskiya gabana faduwa yake ina tunanin kamar wani abu zai faru yau agidannan
Murmushi hajiya hassana tayi tace ba abinda zai faru kisa kayanki kiyi ado kije ki tarbi mijinki nasan zaiyi murnar ganinki dauke da cikinsa
Suhailat ta fito awani riga yar kanti dark blue and mai adon yalo cikinta ya fito tayi kyau sosai,kwalya ta tsantsara masha ,Allah tayi masifar kyau
Hajiya hassana tayi tafi tace wow au wannan saiki zautar da adams wannan kyau haka,yanzu abinda za,ayi kije naji muryarsa a falo.
Farincikine ya mamaye suhailat,tafita zuwa general falo
By
Marsal
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
1⃣7⃣
*by 2besties*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writters
Namijin gaskene,manne da wata yar farar yarinya taci english wear,sai wani shagwaba takemai yana biye mata.
Su binta da ummi na zaune sunyi jugum jugum
Kishine ya turnuke suhailat,ta kuramai ido yadanyi jiki,ya kara kyau da fresh,sanye yake cikin kananun kaya sunyi anko da yarinyar da ake kira da khalisat .
Suhailat taji kafarta yagaza daukarta amma tayi karfin halin karasowa tana yake kallone yadawo kanta musamman khalisat dataji tafi kowa kishi da its har raina kanta tayi,namijin gaske bai dago da kwayar idonsaba but yanajin takunta amma yazama dole shima yarama wulakancin da tamai
Ahankali suhailat ta karaso wajen ,dakyar ta ritsina,tagaidashi tace welcome back dear.
Danne dannen wayarsa yake ko kallon inda yake batayiba,khalisat cikin shagwaba tace my only one tashi muje muyi wanka mana
Murmushi sakar mata yace hakanefa,anjima sai mu tafi restaurant
Yar dariya khalisat ta fashe dashi tace to u have to pick me up
Murmushi yayi ya ajiye wayarsa ya mika mata surarta yayi yanufi part dinsa da ita sunata dariya da wa juna chakulkuli
Suhailat ta shanye kukanta tayi tsit
Ummie da binta suka kalli juna kowacce ta danne kishinta suka farawa suhailat dariyar keta,suna reshe ya koma ga mujiya oh ni yasu nazama bora an zubani a kwandon shara .
Suhailat tafashe da kuka tayi part dinta da sauri tana zuwa tafada kan cinyar hajiya hassana tana kuka mai ciwo
Hakuri hassana tafara bata tana lallashi da nasiha.
A hankali,suhailat tafara samun nutsuwa hajiya ta bata wasu shawarwari da kisa,ta tashi sukayi sallama,
Suhailat ce ta hada coconut juice,tayi doughnut,da farfesun kayan ciki da fruit salad,tasa su a flask da jugs masu kyau ta axa afaranti,tazo ta wuce general falo bataga kowaba tayi farinciki matuka
Shashin namijin gaske ta nufa,yana kan gado ba riga ajikinsa,sai wando short nikker fari kal,khalisat ce kwance ajikinsa tawani narke sai zubamai shagwaba take tanamai kuka,lallashinta yake
A hankali suhailat tashigo,da sallama namijin gaskene ya amsa ya kura mata ido,ta rame tayi baki amma hakan bai hana kyanta fitowa sarariba,
Abin dayasa hanjin cikinsa ya kada,ganin cikinsa ajikinta,tausayintane ya kamasa amma bai nunamata ba yace mekika zoyi anan suhailat,ko kinzo ko raba masoya masu kaunar junansune
Ritse ido suhailat tayi tanajin zafin kalmarnar,ta ajiye abincin akan stool ta kallesa ido cikin ido tace ko daya nakawo wa amarya abincine,juyawa tayi da niyyar tafiya ta tsinkayi muryar khalisat yace ke suhiyat ko suhailat kike zoki daukar mana hoto nida my only
Suhailat ko juyowa batayiba tafita daga dakin tawuce falo,tazo ta gifta ta falon bints taji sauti da sumbatu yana tashi kasa kasa, ahankali ta kutsakai zuwa falon bata taba shigaba ko ina kalkal yake,sautin taji ya dadu,ta wajen bedroom din,ahankali tadan leke ta inda akasa sakata,abinda taganine yasa numfashinta ya tsaya,har taji nakuda yakusa ya kamata,ummie ce da binta tsindir haihuwar uwarsu suna aikata luwadi da madigo
Innalillahi wa,innahiraihi raji,un take ambata,kafarta takasa daukarta ahankali ta fita daga shashin binta,ta nufi shashinta tana ganin kamar a mafarki dama su binta yan lesbians ne,kuka tasaki tana dana sanin shigowa gidan namijin gaske gashi taga abinda yafi karfinta
By
Marsal
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
1⃣8⃣
*by 2besties*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writer
⬜kuka sosai suhailat take yi ciki da nadama da da nasani ashe su binta halin su daya shiyasa suka hade mata kai suke mata hulakanci
Ya Allah ka kare ni da al'umar musalmai su kuma ka shirye su dasu fa masu halin su a duk inda suke in baza su shiryu ba ka nesanta mu da su
Dole na kuma ta ka tsantsan dasu wannan tunanin sam ya hana suhailat rintsawa gashi kuma uwa uba adams yai mata hulakanci a gaba matar sa wayyo Allah ni suhailat Allah kana gani ka fitar dani daga wannan halin da nake ameen a haka har barawo bacci yai awon gaba da ita
Shi kuwa namijin gaske da amarya sa soyayya suke nuna ma junan su abinci da suhailat ta kawo namijin gaske ya janyo ya bude kamshi girkin ne ya doki hancin su
Janyo khalisat yayi baby matso muci abinci gaskiya honey bazan iya cin wannan girkin ba bayan Kace restaurant zamu kiyi haquri kinga yanxu dare ya fara kuma gashi mun debo gajiya ki daure kici ko kaka ne
Haka yai ta lallashin ta har ta yarda ya fara bata a baki
Tausayin suhailat da sonta ne fal a karkashin zuciyar namijin gaske daurewa kawai yake kuma yayi alkawarin nuna ma.suhailat kuskuren ta
Washe gari su binta ana parlo ana jiran namijin gaske suna zaune suna gulmar su shi kuwa suna can suna rakashewar su basu fito ba sai da 'ya'yan hanjin su suka fara kuka
Fitowa sukai a parlo sukai kicibis dasu kallon suwa ye ku khalisat tai ma su ummie amma da yake su suka kawo minfunci duniya sai suka shanye dan su sami damar da zasu hade kai su musgunawa suhailat
Amaryar mu barka da tashi ummie ta fada ya tsina fuska tayi darling wai ina abincin yake ne nifa yunwa nake Ji gashi can a dining binta ta fada tana rawar jiki
Tafi sukai dining area sannan suma suka bi bayan su binta ce tai saving nasu duk dan ta burge amarya
Yallabai barka da tashi suna rige rigen fada atakaice ya amsa musu a ransa ya tunanin halin da suhailat take kamar ya tashi yaje amma sai ya danne
Ita kuwa suhailat ta shirya zata fito ta Ji muryan khalisat tana shagwaba wani kishi ne ya tokare mata mokogwaro ta koma daki tana kuka tana danasin sakin damar ta da tayi gashi nan wata a sama ta dauka
Tun kan ae nisa tana kwasan hulakanci ta ko wane bangare gashi ta alkawaranta kanta duk halin da take ciki baza ta kai kara gida ba........
By marsal💞
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
1⃣9⃣
*by 2besties*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writer
_Kuyi haquri da jin kirin da aka samu wannan ya faru ne sabida gaba daya bamu samin isashen lokaci ku kara haquri_ 🙏
♦sabida tsabar kukan da tai kanta ya fara azabar ciwo ga damuwa da take ciki Idonta ya kumbura fuska tayi jajir sabida azaba jiri ne ya fara diban ta ba shiri ta sulale kan gado
Ina dayar ya fada a ya tsine binta tace Kila tana dakin ta da kullum haka take bakin hali da bakin ciki Basa barin ta ta fito
Sannan kuma tana kunyar ta fito da cikin Shege gidan aure da sauri namijin gaske ya dago jin an shegan ta sama da
wani tsawa game da mari ma sakarwar ummie ki iya bakin ki kar na kuma Ji wata bakar magana ta fito daga bakin ki bama Ke ba har Ke ya nuna binta
Ko ga kan khalisat be biba ta tashi
Cikin bacin rai ya bar wajen daki suhailat ya nufa a kwance ya same ta tayi lamo a gado wani tausayin ta ne ya ratsa shi amma da yake shin din namijin gaske sam be nuna mata ba
Sai da ya kare mata kallo tayi masa kyau sosai gashin ta ta baje a gado sha'awar shafa cikin ta yai yaji lapiyar dan sa amma kawai ya danne abun
Ke ya fada a hankali ta bude idon ta dan tun shigowar sa kamshin turaren sa yai mata sallama ki tashi kar ki tunanin wani abu ne ya shigo dani
A hankali ta yunkurin tashi ganin dakin tai ya soma juya mata komawa tai ta kwanta
Me ya hana ki fitowa ya fada muryar sa daure bana jin dadi bazan iya fitowa ba
Koma me Ke damun ki ki cire wannan kishin naki dan in kika barshi a ranki zaki wahala dan yanxu nasan nayi aure na sami mata wadda nake so take sona kuma zabi na
Rintse idon tai dan Ji tai maganganun sa kamar yana Sara mata adda hawaye ne masu zafi suka silalo
Hakan ya tabbatar masa da yanxu tana son sa tsabar taurin kai ne yasa baza ta bashi haquri ba
Jin shiri yayi yawa ya tabbatar mata ya fita ta kuka ta fara wiwi gashi ba me rarrashi suhailat ta koma marainiyar karfi da yaji ynaxu hussaina kawai take fada ma matsalolin ta itama din bakomai zata fada mata sabida zaman aure sai haquri kowwace mace da irin matsala dake fuskan ta
Ganin ya dade be fito daga dakin ba yasa khalisat ta tashi rai bace tayi sashin ta sukuma suka fara tunanin irin matakin da zasu dauka na daukan fansa........
By marsal💞
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣0⃣
*by 2besties*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writer
🔶sun cikin kus kus ya fito wani kallo ya watsa musu wadda ko waccen su ta shiga tai tayin ta yai gaba ya bar su anan
Binta gaskiya lamarin nan sai mun tashi tsaye sosai kiga daman na fada miki zai so cikin sa kin ki yarda gashi yanxu harda marina
To yanxu mene abinyi shawarar da naja ta bayar ita zamu fara dauka
To kira ta muji yanda za'ae kee ummie sai kace wadda ake biyawa jaka karatu aw ta maimaitawa kin ki ki gane ni wllh har nagaji da fadan abu guda
Ke dakata Karki cimun mutunci naga fa matsalar nan bani kadai ta shafa ba harda Ke Ummi ta fada
To amma kin san yace baya son yaga kowacce kawa tazo ko binta ta fada haka ne
To yanxu zo kiji binta ta rada ma ummie shewa sukayi sannan suka tafa
To kinga mu fara gwada wannan shawaran sai muga me zamuyi bayan sa
Suka tashi cikin karfin gwaiwa
Shi kuwa namijin gaske dakin sa ya nufa ya kwanta ruf da ciki yana tunani yanxu ne ya kamata ae yaja suhailat a jiki dan ya kamata ya nuna mata kulawar sa
Khalisat ganin shiru be biyo ta ba kuma parlon shiru ta biyo shi dakin sa a bakin gadon ta zauna ta fara shafa kansa baby yana ganka cikin wannan hali
Kana dani me zai bata maka rai janyo ta jikin sa yayi kaina ne Ke min ciwo kin san bamu sami isashen bacci ba nan suka fara soyayyar tasu kamar wasu mayu kullum suna tarea makale da juna😏
haka su ummie da binta sukai ta shirin kulla ma suhailat mugunta
Sai da suka tabbatar suhailat lokacin fitowar yayi suka zuba Shampoo akan tayels gashi kuwa yasha mopping kowaccen su ta koma daki ta labe suna jiran tsammani
Suhailat kuwa tana daki yunwa ta ishe ta sai murkususu take abinka da me ciki bata jure yunwa ciki rashi karfin jiki ta daddafo ta fito
Santsin tayel gami da na shampoo suka kwashi suhailat Ayya jikakai tim ta kifa da ciki
Wata azabarbiyar kara ta saki ta da sauri namijin gaske ya tashi jin kara kamar ta suhailat kamr karar nake Ji khalisat ta fada eh nima dai haka
Da sauri ya fito har yana kokarin faduwa khalisat na biye da shi da gudu ya karasa wajen ganin suhailat a kwance jini yana xuba jijjagata ya fara sam ba alamar rai a jikin ta kara ya saki ya rungumota
Sai a lokacin su binta suka fito suna fadin lapiya me yafaru ina suhailat sam bata san inda kanta yake ba
Daukko min keys da gudu khalisat tai dakin sa shi kuwa daukar suhailat yai sai mota ko takan bodyguards nasa bebi ba suka shiga mota shida khalisat
Shewa su ummie suka yi ahayye nanaye yau maga takamar da ake mana da shegen cikin yau sai dai a rariya sukai dariya suka tafa
Farin ciki kamar su xuba ruwa a kasa su sha
A million ya figi motar Allah ne kawai ya kai su lapiya sabida irin gudun da yake shararawa
Suna isa aka karbeta akai A&E (accident and emergency) likitoci suka rufu akan ta
A bakin kofar dakin yai ta safa da marwa sai da suka dibi Kusan 3hours sannan wani likata ya fito yana share gumi da sauri suka isa wajen sa
Ya jikin nata ka biyo ni office ya fada yai gaba su kuma suka dafa masa baya
Ki koma wajenta ko da zasu fito da ita to khalisat ta fada ta koma inda suke ta zauna
Shi kuwa suna shiga doctor ya fara fada kamar be san namijin gaske ba ya zai a bari tai irin wannan fadawa haka gashin nan da kyar muka iya shawo kan lamarin da tuni cikin ya zube
To yanxu me yafaru ya fada hankali tashe ka kwantar da hankalin ka an samu an mata kullin baki mahaifa sai dai a kula amma wanna ba karamin hatsari bane dan ita kanta za'a iya rasa ranta
Aka fito da ita aka kaita dakin Hutu khalisat ce a wajen ta har ya dawo Kije gida ki hado mata kayan bukata ni zan zauna
Tana fita yazauna a gefe gado ya rike hannun gam yana tausaya mata amma wannan yasan makircin bazai wuce nasu binta ba
Shafa cikin ta yai da tuni amsa asarar sa hmmmm shi kadai yasan irin hukuncin da su binta zasu fusakan ta
By marsal💞*👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣1⃣
*by 2besties*
_salma Ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
*wannan shafin na sadaukarwa da khadijah kankarofi,ina tayaki adu,a ubangiji Allah yasa ki dace kuma Allah ya cika miki burinki*
→★ adams yashiga zurfin tunani,kawai yaga an banko kofa anshigo khalisace kamar zata haukace tsabar kishi
Adams yace my only meye faru,fadawa tayi jikinsa ta fashe da kuka tace ina bukatarka my only zan iya mutuwa akanka taso muje hotel dan Allah
Adams ji yake kamar ya kwarara ihu khalisat tanaso ta kasheta ita kullum bata gajiya ba damar ya musa mata,ya tashi yana karewa suhailat ido suka fice.
Bude ido suhailat tayi ta fashe da kuka mao tsuma zuciya,tanaaon shan shayi amma ba maitaimaka mata.
Wata nurse ce tashigo tace aunty mekike bukata?
Suhailat tace shayi nake bukata kuma banga an kawo kayan shayiba
Nurse tace karki damu aunty ainan asibitinku,bari inje office din doctor in tambaya
Kafin tarufe bakinta mominta tashigo da kanwarta cikin murna suhailat tace momy dama zan sake ganinki
Kuka momy tasaki tace anya wannan suhailat dinace waya zamarmin dake haka?
Kuka suhailat tasa yayinda momy matakara fashewa da kuka tace suhailat ina shi adam din yake?munje gidan abokan zamqnki sukace kinyi bari kina asibiti inashi adam din ai yakamata ya zauna ko kina bukatar wanu abu
Suhailat tayi murmushin takaici bazata iya boyewa momy ba tace yadauki amaryarsa sun tafi hotel
Momy tace what?bazaiyuba wallahi bazan lamuntaba bari inkira mahaifinsa yazo yajawa dansa kunne yasakarmin diyata donni ba,a rainamin hankali
Ruko hannunta suhailat tayi tace no mom ki barshi kawai
Momy tace rufemin baki sokuwa maiduguri zaki koma,danna waya,ringin biyu dadyn adams ya dauka yace ranki ya dade
Momy tace inafa wani ranki ya dade his excellency kazo asibitin a&e danka yanason kashemin yata wallahi bazata sabuba
Dadyn yace what?ganinan zuwa,ba,afi mintunaba karar injiniya yacika asibitin,dady da momin adams aka bude musu mota suka fito sai kwasar gaisuwa ake
A fusace dady yashigo yana ina adams din
Momin suhy tace kalli yanda yabar yata suka tafi soyewa da amaryarsa,gaskiya nibazan yarda ba don lokacin da aka kawomai yata fresh take abar sha,awa amma kalli yanda tayi baki tarame
Dady ya dafa kan suhailat yace yata kiji tsoran Allah ki gayamin abinda ya wakana tun lokacin aurenku.
Momyn adams tace eh ki gaya mana musan matakin dazamu dauka
Suhailat tace tunda na auri namijin gaske bai taba dukanaba yana bala,in sona ina wulakantasa,basu labari tayi komai amma bata basu labarin abinda binta suke mataba.
Salati dad ya dauka yace zaizo yasameni wallahi saina dau mataki shiwai dan soyayya ko bari ya dawo
By
Marsal[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣2⃣
*by 2besties*
_salma Ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
®online hausa writter
¤namijin gaskene ya danno kai harabar asibitin,yasha jinin jikinsa daya hango motocin *his excellency*
Khalisat saikara mannemai take fitowa sukayi daga motar khalisat na rike d take away
Jiki asanyaye yashigo dakin
Momynsa ta kallesa tace to romeo and julliet iyayen soyayya kun dawo,to bata mutuba,ka kyauta son nace ka kyauta wannan ya tabbatarmin dakai lailai namijin gaskene kwarai,kunbar yarinyar mutane to kabani takardarta kokuma ka samesu akotu.
Adams yace mom bafaka bane kafin yakarasa dadynsa ya wankesa da wawan mari har guda biyu yace kai kasan wacece suhailat awuri da wurin mom dinka to inbaka saniba kasani yau suhailat yar kanwar mom dinkace,mahaifinta shi yasha fama har yau na haye matakan danake,tun banida komai yabani kudi najuya nazama hamshakin maikudi kuma da taimakon Allah ta dalilinsa nazama shugaban kasa,kaci amana kaci amana kabani takarsarta kafin in tsinema Albarka kabi duniya
Adams jikinsa yayi sanyi yaje ya durkusa agadon suhailat ya rukko hannun suhailat yace suhailat ki gaya musu kina sona ,karki gujeni suhailat wallahi ina matukar kaunarki suhailat
Momynsa tace munafuki tashi suhailat karki yarda da kallamansa mayaudari tashi kabada takardarta ko nima in tsinema
Kuka adams ya saki,ya ce suhailat zansakekine badan banasonkiba zan sakekine domin bin umarnin iyayenmu suhailat nasakeki saki daya
Adams yafita aguje yakuka maicin rai,shiga motarsa yayi yanata kuka,khalisat ce tashigo tace haba dear,meye abin kuka bayan gani
Adams yace suhaikat bazaki ganeba bazaki ganeba inajin kaunar suhailat ajinin jikina tayaya kike,itace macen dana faroso arayuwata ki tukani bazan iya ttuki ba
Haushi khalisat yabata ta tukasu zuwa gida,dakyar namijin gaske ya fito daga mota,bintane zaune sunyi jigum jigum
Sunaganin khalisat tashigo suka mata inkiya da ido,mayar musu tayi alamun ansamu nassara
Namijin gaske ya wuce dakinsa kota kansu baibiba ya haye saman gado,yakira bodyguard dinsa yace yazo
Ba,afi mintunaba sai gashi yashigo,namijin gaske yabashi miliyoyin kudi yace inason kasiyomin barasa ,amma karku bari kowayagani ta kofar baya zaku shigomin dashi gwanda insha inmanta da suhailat
Abin yabawa bodyguard din mamaki yace yallabai amma kasamn haramun ne kuma akwai illlah acikinsa kuma bantaba gani kashaba.
Dakamai tsawa adams yayi yace nabaka minti biyu kaje kasiyo
Ba,afi minti ukuba saiga bosyguard din yana sshigowa dakaton din giyoyi kala kala yana tausayawa rayuwar adam
Adams yadauki giya daya yabude yq dinga kwankwada,yasha kwalba biyu,surutan banza yafara
Khalisat tana shigowa,taci karo da warin giya cikin mamaki tace adams giya akan wata banza
Adams yaga khalisat tana mai gizon suhailat,dagudu yanufi wajen yana suhailat meyasa kika zabi ki gujeni
Khalisat taga yafasa kwalbar yana. Suhailat taho inji duminki,ina da gudu tafita yana biye da ita khalisat ta taddasu binta azaune afalo cikin nishi tsce wallahi kowa yagudu namijin gaske zaiyi kisa ya haukace
Da gudu binta ta nufi shashinta ta kulle,ummi da khalisat suka fada shashin suhaikat suka kulle
By
Marsal
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣3⃣
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
🖤 kixo dan Allah Karki guje ni kice kina sona Karki bari su rabamu haka yai ta buga kofa amma basu bude ba
Ke wai me ya faru ne ummie ta tambayi khalisat nima wllh ban sani ba dg na shiga ya taso yana kiran waccen banzar suhailat din dariya sukai su tafa dan yanxu sun hade kan su da ita wallahi kadan ma suka gani
Haka ya gaji ya koma sama ya kuma kwankwadar giyar sa
Kullum yana daki duk yabi yayi baki ya rame, ita kuwa suhailat tana gidan su ba irin kular da ba'a bata amma tunanin Adams ya hana ta sakewa gashi cikin ta ya tsufa ya shiga watan haihuwa
Tunani Adams yake yanxu da ta haihu tagama iddar ta wata karamar akwati ya daukko ya zuba dollars a ciki sannan ya rubuta wasika yasa a ciki
Wani daga cikin bodyguards din sa ya akai gidan su suhailat dan Aiken ne ya isa gidan su suhailat suna zaune tayi jugum kamar kullum haba daughter kin sa damuwa aranki kuma kinsan bake kadai ce ba hb dan Allah kicere komai dg ranki
Mome Adams fa Ke ki kyale shi kin ji kuka ta saka ana haka dan ake ya shigo hajiya wai gashi inji oga ya mikawa suhailat a sanyaye ta karba ko har ya tafi tana juyawa takasa katabus
Daki ta tashi ta shiga ta bude wani akwati ne me kyau budewa tayi kudi ne 1million dollars ne sai takarda
Budewa Tai ta fara karantawa
_Assalamu alaikum ya kike dafatan kina lapiya Ke da abinda yake cikin ki suhailat na janye sakin da nai miki tun ranar kiyi haquri wallahi ba laifina bane ga wannan kudin ba yawa me kaunar ki har abada Adams namijin gaske_
Wasu hawayen farin ciki ne ya zubo mata ko nauyin cikn jikin ta bata Ji ba ta fito parlo da gudu mome kinga ta nuna mata tsaki tayi Ke ni kyale ni ba inda zaki koma haba mome ni fa...Ke rufe min baki wadda bata san ciwon kanta ba
Sam namijin gaske ya daina walwala ya daina shiga harkar su
Suna parlo suna hira nifa gaskiya nagaji da ganin Adams a haka khalisat ta fada uhmm kyale shi zaiyi zai gama ne ummie ta fada ae wallahi zamu yi maganin su ne gaba daya Bari naja ta dawo daga tafiyar da tayi zamuje wajen boka me kankat aci uban su
Cikin dare ciwo ya turnike suhailat tun tana daurewa har ta fara kuka momee ce ta jiyo kukan ta da sauri ta fito tayi dakin tana isa taga nakuda ce aka dauke ta sai asibiti
Haka sukai ta kai kawo har Allah ya sauke ta lafiya ta haifo santalelen yaron ta me kyau namiji kato mome ce ta fara bugawa tana fadawa yan uwa da abokan arziki ko kan kace me asibiti ya cika damkan da yan uwa ita kuwa tana ta sharar baccin ta hankalin kwance
Momeen Adams ce tazo tun da dauki dan take kallo ikon Allah kamar su daya da Adams haka kowa yai ta daukan dan cike da so
Har aka sallami suhaily namijin gaske be san ta haihu ba momen sa ce ta kira sai da ta kira Sau biyu be dauka ba sai ana uku yana dubawa yaga mome cikin sauri ya dauka
Eh sai yanxu na tabbatar da baka da mutunci ya Kwana uku da haihuwar matar amma.ko waya baka kira kaji lapiyar ta ba mome me ta Haifa namij in ka ga dama kaje ka gani
Tuni wani farin ciki ya lullube shi yafara shirin zuwa ganin dan sa
Haka yasa akai masa.odar kayan jarirai ma masu tsadar gaske
Ya shirya tsaf fuskar sa cike da annuri khalisat ta shigo shirin me kake haka ga wani farin ciki da kake suhailat ce ta haihu namiji kamar saukar aradu taji zance har ya fita bata sani ba
Da gudu ta fito tana kirin su binta ku kuna ina ne ku fito kar bakin ciki ya kashe ni ni kadai me ya faru suhailat ta haihu wani uban ashar ummie ta saki me ta Haifa namiji ta basu amsa.kamar zata kurma ihu......
By marsal💞
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣4⃣
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
🔵mene abinyi yanxu ta tambaya dan tun da yaji haihuwar yake wani farin ciki wallahi har na tsani dan da zan ganshi zan iya kashe shi
Shi kuwa yana isa gidan su suhailat yana ta wani washe baki yana yake karbar yaron yayi yana kallon sa cike da so ba kunya ya wani rungume shi yayi yana shafa yaron shi kansa yaga kamar sa suke yi dashi
Duk da tana kewar sa amma ko kallon sa batai ba satar kallon ta ya dinga yi tayi masa kyau sosai sabida kulawar da take samu ko wannan kumburin na jego bata yi ba
Suhailat wai baki ganni ba ne murmushi kawai tayi masa ta tashi ta bar gun duk da bata kula shi ba amma yaji dadin murmushi da tai masa.
Nan yai ma dan sa huduba da sunan mahifin sa mome ga shi nan ya mika mata shi yana fadar sunan da yasa masa
Ko da yaje gidan su fada momeen sa ta dinga yi masa kamar zata dake shi kuma gashi ta haihu ta gama idda mome ae ni na meda ta tun a ranar kuma ko ita ki tambaye ta kiji
Ga kayan baby sai akai mata
Wane kaya kuma Alhaji ma ya sa an hada anjima za'a tafi kaiwa to mome sai a hada da su nan ta gaji da fada ta koma nasiha
Haka akaita shiga da kayan baby dana suhailat kamar ba gobe kaya ne masu kyau da tsada
Ran suna suhailat tayi kyau sosai kamar wata amarya haka akai taro akai lapiya kowa ya koma gida yana san barka da inda suke kiran yaro da sultan
Kullum.sai Adams yaje gidan su yaima Momeen sa magiyar a dawo masa da suhailat da kyar da yarda zata je gidan su koda taje mahaifiyar suhailar fir taki sai da dadyn sa yai magana sannan ta yarda zata koma
Haka akai ta shiri ran da za'a dawo da suhailat ba irin kukan da batai ba duk da yanxu ta tabbatar da irin son da Adams yake mata
Haka aka kawo ta gidan ta ita da sultan ya kuma girma yayi kyau sosai gwanin sha'awa kiri kiri su binta suka nuna bakin cikin su a fili
Wata kulawa admas Ke bawa suhailat da sultan hakan ba karamin ciwo yake ma su khalisat ba
Sam suhailat bata shiga sabgar su tana ta taka tsam tsam da dan data
Naja ce kawar binta taje musu gidan boka me kankat boka ne ya daka mata tsawae kika zo yi afuwan Kasan banda wani wanda yake biyan bukata sai kai nan ta fara yi masa kirari wata dariya ya dinga shekawa
Mene bukatar ki akan maganr wannan kishirya kawata muna so ka yi aikin da zata haukace tsawa yayi mata har sai da bukkar ta girgiza bazai yihuba har yanxu aljani *dakkariyari* be gama jinya ba
To boka ka sa tsana a tsakanin su sannan shima yaron kasa ya tsane shi nan yai wata dariya ajiye masa kudi tai ta fita da rarrafe kamar yarda dokar sa yake
Taje ta labarta masu har wani party suka hada ganin Adams baya nan
Dauki Adams yake ya dawo yaga dan sa jirgi yana sauka driver ya daukko shi inda binta,ummie,khalisat sai kuma suhailat da sultan suna gefe ana jiran dawowar namijn gaske
Motocine suka fara shigowa kansa ne yai wata irin sarawa jariri na dibarsa dade kansa yai ya zauna har sai da ya lafa sannan ya fito
Da gudu khalisat taje ta rungume shi haka su binta akaje ana kwarkwasa ita kuwa suhailat ganin ko kallon ta be ba yasa jikin ga yai sanyi sai da yazo daf da ita tsinkar muryar ta yai tana masa sannu da zuwa wata irin tsanar ta yaji a ransa kallon banza ya watsa mata sannan ya shige
Juyawa suke gaba dayan su suna mata gwalo
To wannan me yake nufi Kila ko gajiya ce ta shige daki sai da yai wanka sanan suka hallara a dinning ita ma fitowa tai ta zauna wata tsawa ya daka mata Ke tashi ko bani waje kallon sa yai shike da mamaki bazaki tashi ba. Ko sai nayi ball dake da gudu ta shi tai dakin ta dan Ji yai gaba daya baya son ganin ta da ita da sultan
By marsal💞
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣5⃣
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
⬛wata irin shakara da yanga kwarkwasa suka fara yi masa shi kuwa yana wangale musu baki yana farin ciki ganin sun hade kan su
Murna kuwa sunyi ta kamar wanda akai musu albishir an basu jirgin sama ✈
Haka rayuwa ta cude ma suhailat ko fitowa tai sun dunga hantarar ta kyara da zagi ba irin wanda Basa yi mata
Suhailat ce tazo gifatawa khalisat tai magana
Darling wai mene amfanin wannan a gidan nan ne ta nuna ta hmmm ni dan kar momee tai min fada wallahi da tuni na korata gidan su
To ba sai ta dinga ayukan gidan nan ba a sallami en aiki binta ta fada gaskiya ne tunda baza a dinga ciyar da ita a banza ba ummie ta fada batare da yayi dogon tunani ba yace a kirata
Jikin ummie har rawa yake ta tafi kiran ta da sauri tazo karta kuma wani laifi tana goye da sultan ta durgusa kanta akasa gani Ke ko bude kunnen ki kiji daga yau Ke zaki dinga aikin gidan gaba dayan su tundaga wanke wanke goge goge har girki kuma in kika yi ba dai dai ba ranki sai ya baci tashi Kije
Ah Ke zo nan binta ta fada to ae baka ce ta dinga bawa flowers ruwa ba sabida gaba daya za'a sallami en aiki to kinji abinda tace ko
Kuma aikin ki daga yau zai fara
Maza tashi ban son ganin ki tana kuka ta tafi cike da bakin ciki wannan wace irin rayuwa ce Allah ka kawo min sauki
Tundaga wannan lokaci rayuwa tai mata zafi aiki safe da rana tarame tayi baki tana kitchen tana girki ta kwantar da sultan a parlo yana bacci
Ummie ce ta fito wane shegen ne ya ajiye wannan a nan sa hannu tai ta tunkudo shi daga kan kujerar tai saurin komawa daki
Tana kitchen ta jiyo kukan sa da gudu ta fito da gudu ya fadi kasa bakin sa ya fashe sabida azabar kukan da yake har shidewa yai ya kasa kuka
Ita ma kukan tasa ta dauke shi tai daki dashi ta gama jijjagi yana bacci ta ma manta da girkin da take
Binta ce a parlo tana kwala mata kira da sauri ta fito Ke wacce irin jaka ce sabida baki san darajar abu ba kin bar abu ya kone
Kiyi haquri sultan ne ya fadi shine nake rarrashin sa mari ta kwada mata to daga yau kika kuma wllh sai kin gane kuren ki banza
Wallahi da hauka kika dace kuma ki maza ki gama mijin mu ya kusa dawowa
Tana goye da sultan dan yanxu bata bari suyi nisa sabida azabar da su binta Ke masa a farfajiyar gidan tana bawa flowers ruwa
Hajiya hussaina ta shigo sam bata gane ta ba sai da tai gaba juyowar da zatayi wazan ganewa idanuna suhailat ce ko me kama da ita nice Hajiya mamaki ya hana ta magana matsowa tai kusa da ita tana kallon ta kuka ta saki suhailat haka sukai mai dake
Yi shiru hajiya kar su Ji kamo ta gaban ta yana dukan tara tara haka tai palon tai sa'a bakowa a parlon suka shige daki tana kuka tana fada mata
Kiyi haquri in Allah ya yarda zan taimaka miki in na koma zan turo miki addu'o'in da zaki dinga yi bari na tafi kar naja miki wani laifin
Suna fitowa sukai karo da khalisat wai mugun kallo ta watsa mata lallai kan mage ya waye Hajiya hussaina na ma kallon banza tai ma da sannu Allah zai kawo karshen ku
Ta fita ta bar ta su binta ummie ku fito kuga ikon Allah da sauri suka karaso
Dai dai da zuwan namijn gaske lapiya wata kawar ta me zugata ce tazo nan ta shirya mata karya nan take ya hau ya zauna
Kan Kace me ya fara dukan ta ta ko ina tun tana.kuka har ta daina sai da suka ga ta galabaita sannan suka ja shi dakin sa aka barta a kwance
Bayan 30munites binta ta fito a kwance ta ganta freg ta bude ta daukko ruwa me shegen sanyi ta kwara mata a zabure ta tashi da halla tashi ki bawa mutane waje kan ma kara miki wani baza ta iya tashi ba haka.ta rarrafa tana shiga ta tarar fuskar sultan duk busashen hawaye yayi kuka har ya gaji
By marsal💞
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣6⃣
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
♥rungume sultan tai ciki da tausayin sa wannan wace irin rayuwa ce kuka ne ya kubce mata tayi me Isar ta idon ta ya kumbura sosai muryar ta kuwa ko fitowa bata yi
Kira taji ana kwala mata da gudu ta fito dan ta san kiran wadan nan ba alkhaeri bane gani Ke a gidan ubanki haka kika gani in an kira ya tsaya a tsaye
Tan kokarin durkusawa taji an warto kafarta take ta zube bakin ta ya bugu da tayels nan take ya fashe
Daga yau sai yau duk lokacin da daya daga cikin mu ya kuma kiran ki kika tsaya a tsaye wallahi sai mun miki wanda ya fi wannan khalisat ta fada
Maza jeki kitchen ki hado min water melon shake da chefs kuma sauran ki kawo beyi sanyi ba
Ta tashi zata tafi khalisat tace wai saurin me kike ne eheee dawowa tai ta durkusawa indomae zaki dafan da scrambling egg Saura kiyi min shirme ki raina wayon ki
Ke ta dago kai ummie ce ta yi mata wani mugun kallo sannan tace ki dafo min checking peper Saura ki kiyi da sauri ki tsaya wannan shashancin naki ko kuma ki zabgan yaji
Kitchen ta nufa tana aiki tana kuka gaba daya ta kunna gas din sabida karta bata lokaci suyi mata taron dangi cikin kan kani lokaci ta gama ta ajiye a dinning
Durkusawa tai nagama ta fada cikin isa ummie tace wallahi in har naci naji ba yanda nake so ba daga Ke har shegen dan naki sai kun gane kuren ku
Bata ce komai ba tashiga daki ta zauna ta rafka uban tagumi Allah ka kawo min sauki a wannan rayuwa in mutuwa ce alkhaeri Allah ka dauke ni in kuma wani laifin nai kake jarrabta ta to ya ubangiji ka yafe min
Jitai ana kwalla mata kira ke daman sunan da suke kiran ta dashi Ke nan
cikin hanzari ta fito suna dining haka ake girki a gidan ubanki a kawo ba wani abu ne sanyi khalisat ta fada cikin gadara
Komawa tai ta hada pineapple with coconut juice da ruwan kankara ta hada dan kar ace be sanyi ba cikin wani babban jug tayi ta kawo ta juya zata tafi Ke zo nan
Bata Ankara ba taji an watsa mata ruwan lemon gaba daya a jikin ta wani sanyi ne ya ratsata kuka ta fara yi tana wai me nai muku kuke min haka kun mai dani kamar wata baiwar ku
Au tambayar mu kike lallai har yanxu baki gama huruwa ba tunda bakin ki be mutu ba
binta ce ta karasa kwara mata sauran lemon bace ki bamu waje kan na galabaitar da Ke jaka kawai Ke ba kina tun kawo kin haihu ba
Sai dai ki kuma haifar wani a bola ummie ta fada ni wallahi nagaji da ganin ta a gidan wallh daman kun Bari ya Kore ta khalisat ta fada
To ae ba yanxu ba ki Bari lokaci yana nan tafe wadda da kanta zata gudu
Dariya sukai gaba daya sannan suka tafa
Wani azababban zazzabine ya rufe ta ga ciwon kai take jikin ta ya dau zafi ta fara kakkarwa sabida jigatar da tayi ba Hutu kullum haka take fama rarrafawa tai ta daukko paracetamol a drawer ta sha ta kwanta ko zata Ji relief
Haka suhailat take rayuwa cikin kunci da masifa iri iri in su basu dake ta ba to zasu shirya mata makircin da admas din zai dake ta
Suhailat ce goye da sultan tana moping dib parlon da gayya suke bata shi tanayi suna batawa
binta ce ta fito da underwears din ta tari guda Ke maza ungo jeki wanke min su tas Saura naga badai dai ba kuma ki san yanda zaki wane Karki min mugunta ki tala min su
To bari na gama ki gama me lallai Ke wai ban gaya miki in nasaki aiki duk abinda kike ki ajeye kiyi min ba a salube ta karba ta tafi laundry na gidan
Ta zazzagewa wani karni ya doki hancin ta amai ne ya tawo mata nan ta dinga kwararawa ya salam yanxu panties din wannan yar iskar zan wanke na yar lesbian innalillahi wa'inna ilaihir raju'un duk da a washing machine zata yi amma tana kyankyamin taba su
Sai da ta wanke su tas sannan ta kai mata cikin fargaba kar tace basu yi ba.........
By marsal💞[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣7⃣
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
⚫shiga toilet ki shanya su sannan ki wanke min shi tas in kin gama ki gyaran daki sannan ki niken wannan kayan Saura kuma naga an sacen dan an saba
Ba gyara kwata kwata a toilet din kamar bana mace ba nan ta wanke shi ta gyara dakin tas sannan ta fito jikin ta duk yayi tsami Sabida gajiya
Shi kuwa namijn gaske gaba daya baya jin dadi gidan sam wani duk rahar da yake da ya shigo zai Ji yai masa zafi ga wani irin tsanar suhailat da yake Ji shi ya rasa mene dalilin
Wayar sa ce ta fara ringin kamar bazai dauka ba sai ya dauka dadyn sa ne
Jiki ba kwari ya dauka hello dady son wau me yake damun ka ne gaba daya baka zuwa gidan kuma in ba'a kira ka ba baka kira dady wallahi aiki ne yai min yawa to kai dai dinga sassautawa kan ka
Kar ka sa marwa kanka wata matsalan to dady ina jika na sai da yai jim sannan yace yana gida shi gaba daya ya ma manta dashi
Ka boye su bare su zo mu gansu dady ban son su dinga fita sabida kar a kwaso masa gajiya ya fada dan ya gaji ma da zance yaron ko maganr sa shi da uwar sa ba yaso to ka gaishe su zasu Ji dady ya kashe wayar
Ta gama aiki tana daki tana ma sultan wasa wayar ta taji tana vibrate dan badamar tasa ta a ringin su binta suce tana hada musu munafunci dauka ta cikin jin dadi
Hajiya hussaina ce ta kira ta yar uwa ta ya kike lafiya Hajiya wasu kwalla ta share wai har yanxu basu daina yi miki abubuwa ba
Wallahi Hajiya sai addu'a dan kullu sabbabin azaba suke fito min dasu yanxu ban isa nayi nisa da sultan ba sai suyi masa wani abun
Ko imani basu dashi bare suyi tunani wannan da be san me duniyar take ciki b
To ki kara haquri na san kina yi sannan ki dage wajen addu'a Allah yana jin ki kuma yana kallon su
Sannan zan sa a dinga yi miki addu'a to nagode Hajiya zan turo miki da kudi ki dinga yi min sadaka dasu
Kinga ni ba halin fita to ya za'ae kimin transfer din ta waya zan miki sai ki turo min da account number dn ki
Ki bari Nasa ae miki aa Hajiya wai ba raina abinda kike min nake ba kawai ina so ayi addu'a sosai
Sannan kisa a dinga yimin sauka in an gama sai a yi abinci sadaka Allah ya yayemin wannan masifar to shikkenan Ke ma kin dage da addu'a sosai sai kiga Allah ya karya duk wani sharrin da sukai miki
Sukai sallama sannan ta tura mata ba dare ba rana haka take addu'a ko aiki take yi bata daina addu'a
Su binta kuwa suna nan suna sake sabon shiri domin yanxu ko makirci suka hada mata su fada masa baya dukan ta sai dai yace to Ke kinji ki gyara
Da yamma tana waje tana bawa flowers ruwa sultan yaba bayan ta yana faman kuka ajiye wa tai ta fara jijjiga shi amma ya ki daina kukan
Namijn gaske ne gefe yana karanta newspaper tunda sultan ya fara kuka ya tsaya yana kallon su kamar ya kure ta sai kuma ya kasa taso wa yai ya karaso inda take jijjiga sultan
Matsawa tai kirjin ta na dukan tara tara kawo shi taji ya fada gaban ta ne ya wani mugun faduwa na shiga uku ta fada a ranta kawo shi mana ta sake maimaita mata
A tsorace ta mika masa shi ya karbe shi ya koma garden
Allah yasa ba wani abu zai masa ba
Wasa ya fara masa kan kace me yaro ya fara dariya kamar me tana dafa gefe tana kallon sa kamar ba shi ba suna hada ido ya daka mata tsawa back to your business
Jiki na bari ta cigaba da aikin ta wani sanyi taji yana ratsa ranta Allah nagode ma dan rabon da ta dauki dan tun yana jariri
Khalisat ce ta fito da niyar zuwa wajen namijn gaske tsayawa tai saroro me zan gani
Adams Kasan me ka dauka kuwa kallon rashin fahimta yai mata me kike nufi nuna sultan tai wanda yake wasa da hannun sa
Naga ka dau wannan to ba dana bane ba zaro ido tai lallai aikin su ya fara warware wa tana wannan tunani taji yana cewa shima yana da hakki akaina kuma ya kamata ace nasan halin da yake ciki domin.....katse shi tai Kaga Adams bana son dogon zance waya ce danka bane tashi tai a fusace ta shiga cikin gida........
By marsal💞
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣8⃣
*by 2besties*
_salma Ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
☆adams yaci gaba da yiwa sultan wasa ,sultan sai dariya yake
Bintace tafito tana yamutse fuska tace dear waimeye haka?
Adams yace kamarya?badana bane akwai wani da acikinnan kamarsa?
Binta ta murguda baki tace kaidai kasani,yanzu muzakawa gorin haihuwa kukan munafurci tafashe dashi
Yayinda khalisat tafito tana huci tace wallahi bazaiyuba dole in kashe dannan kowa yarasa
Da karfi ta warci sultan ahannun adams ta tika dakasa,kara ya saki numfashinsa ya dauke
Itama suhailat ta dora hannu aka ta kurma uban ihu nashiga uku,dana kun kashemin dana innalillahi wa,innahiraihi raji,un
Adams rai abace ya kalli khalisat yace kin kyauta kin kashemin dana
Harararsa khalisat tayi tace and so what kuma nakashe banza
Ran suhailat ya bace tayi kukan kura tayo kan khalisat tadinga kai mata bugu idonta ya rufe,
Binta tanaganin haka tayi shashinta da gudu
Namijin gaske yana zuwa ya daddage ya fesawa suhailat mari pas kyawawa guda uku yace ke a matsayinki na yar aiki harkin isa ki dukarmin matata inkyaleki
Suhailat tace adams wannan wani irin zaluncine nagaji dazaman gidannan ka sauwakemin nagaji kuma sai ubangiji Allah yasakamin
Momyn adams ce tashigo tare da hajiya hassana
Momyn adams tace to Dama ance komin nisan jifa kasa zai dawo gashi yau nagani da idona na sheda,suhailat jeki sako mayafinki mutafi kingama zaman aure agidannan
Adams yace momy yaushe kikazo?
Harara tadakamai tace ina zakasani kana tare da shedan ta kasani daga yau bani bakai ka nemi wata uwar badainiba,kaida suhailat har abada kunyi nesa kuma zansa jami,an tsaro da cameras sosai agidanmu ko an ganka na yarje akama ka
Hajiya hassana ta dauki sultan dayake tsakanin raida mutuwa ta dorasa akafadarta tana zubar da hawaye,itama suhailat tafito sanye da hijjabi tana zubar da kwallah dauke da akwati a hannunta
Momy tace aje musu akwatin anan in Allah ya yarda keda gidannan har abada
Aje akwatin suhailat tayi ta kalli namijin gaske tana karajin kaunarsa da sonsa tamkar ajininta ,bin bayan su umma tayi hawaye nafita a idonta
By
Marsal
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
2⃣9⃣
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
_this page is dedicated to our fans,thank you for ur support and ur love,we gave u around of love in our heart_
Asibiti aka nufa da sultan akasamai drip,suhailat tayi kuka harta godewa Allah dataga wahalar dasultan yakesha
Ga hannunsa ya karye abin tausayi
Hajiya hassana sai tausarta take,mutane yan gaisuwa suka fara cika a asibitin,momyn suhailat ce tashigo tare da dadynta
Suhailat taruga aguje ta rungumi momy tana momy sunason kasheni zasu kasheni zasu haukatani sun rabani da mijina momy mainayi musu
Kuka momy tasata kalli suhailat data rame tayi baki ba lallema adinga ganetaba .
Dady yace suhailat haka suka zamarmin dake?lalle azzalumai ne dole in dau mataki
Tarin sultan yakatse musu hanzari,da gudu suhailat ta nufi wajen,tana dan matsamai kirji,dago hannu sultan yayi yana wa suhailat murmushi,barcine ya kwashesa
Yayinda suhailat taji gabanta yayi mugun haduwa,dagudu tawuce su momy taja wata doctor tana doctor pls kizo ki duban yarona kar ya mutu
Dagudu suka shiga dakin yayinda doctor din ta auna sultan girgiza kai tayu jiki asanyaye tayi yake tace ki kwantar da hankalinki yana baccine.
Girgiza kai suhailat tayi tana a a ban yardaba jikina ya bani kamar dana ya mutu
Momyn adams da jikinsa yayi sanyi tace haba suhailat ki kwantar da hankalinki
Momy ta dakawa momyn adams,harara tace tayaya zata kwantar da hankalinka bayan an zalunceta
Momyn adam tace haba hajara haba hajara ina matsayin yayarki yar uwarki zaki dinga gasamin magana
Momy tace dole ingayamiki magana iya san raina saboda duk abunda yafaru kece sanadi ke kika matsa ayi aurannan,gashi sunaso. Su nakasamin yata
Kuka momyn adams tasa nagode hajara ba laifinki bane nagode
Dadyn suhailat yace haba kuyi shuru mana kisawa zuciyarku hakuri,kekuma doctor ki gayamana gaskiya in mutuwa yayi musani
Doctor tace alhaji sai hakuri rai yayi halinsa
Sakin baki suhailat tayi tana kukan zuci daga bisani tasaki ihu tayi kan sultan ta kankamesa gam gam tana sultan_sultan _sultan karka tafi ka barni ina sonka sultan
Hassanace da momyn adams suke riketa dabata baki;amma ina kuka take tana ta sumbatu da kuka da fadin sunan sultan
By
Marsal[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
3⃣0⃣
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
Wani likita ne ya shigo tare da nurses sukace su basu waje ina sam taki saki gadon da sultan yake da kyar aka ban bare ta daga jikin gadon suka tura shi suka fita
Wani kuka tasa ki tare da zubewa kasa a sume nan itama aka dauke ta
Cikin ikon Allah likitoci suka taru akan sultan suka ceto ransa da kyar turo shi sukai suka kaishi dakin da suhailat take
A hankali ta fara bude idon ta abinda ya faru ne ya fara dawo mata da sauri ta tashi Hajiya hassana ne da mome suka yo kan ta suna mata sannu
Ina sultan yake dan Allah kuce be mutu ba kuka ta saki mome ce ta rike ta tana bata haquri
Hannun ta taja har bakin gadon da sultan yake wani farin ciki ne ya ishe ta ganin sultan yana bacci hankali kwance an dorai masa kansa da bandages daukan sa tai ta rungume shi tana kuka tashi yai daga baccin yana mata dariya nan itama ta fara dariyar farin ciki
Nan likita ya shigo ya basu sallama gidan su suhailat dake abuja suka huce ita kuma Hajiya hassan tayi gidan ta
Binta ce da su ummie farin ciki ya ishe su shegiya ana cen ana kukan mutuwa yanxu sai mugu dan da za'a dauka ae masa wasa
Ni wallh ba abinda ya batan rai irin wa ae shima yana da haqqi akai na yanxu kinga sai ya nemi wani me haqqin khalisat ta fada
Dariya suka kwashe sannan suka tafa to yanxu Mene abinyi ku matso kuji nan suka hadu binta ta rada musu wata maganar dariya suka kuma saki gaba dayan su
Kulawa sosai Momeen suhailat take basu ita da sultan nan take suka warware sukai kyau kamar basu ba,
Dadyn Adams ne zaune shi da momen sa alhaji ni wallh abinda yaron nan yake sam baya kyautawa ya fifita matan sa akan suhailat ga abubuwan da suke mata yanxu da wuya iyayen ta su bari ta komo
Duk yadda muke da mahaifiyar ta amma sai da ta kusa fadan magana
Gaskiya be kyauta ta ba waya dady ya daukko ya danna kiran sa yana zaune jugum ya rasa abinda Ke damun da sauri ya dauka cikin fada dady ya fara magana
Kai wane irin yaro ne mara jin magana kai maza maza kazo ina son ganin ka kan raina ya gama baci
Tab ko wane laifi naiwa dady nasan ba karami bane a hanzar ce ya shirya ya fito ko takan su khalisat be biba
By marsal
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
3⃣1⃣
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
A 36o yake gudu cikin kan kanin lokaci ya isa gidan a parlon dady ya tarar da su durkusawa yai har kasa ya gaida mome amma ko kallon arziki be samu ba dady kuwa da kyar ya amsa
Lallai Adams basai kayi haka zaka nuna mana Cesar ka girma ba dagowa yai da sauri wani mugun kallo mome ta watsa masa
Mome menayi au baka sani ba to bari kaji duk irin abunda kake wa suhailat ya dawo kunne na wato sabida rashin adalci shiru tai batare da ta karasa ba
Mome kiyi haquri ba laifi na bane to laifin wane ni kaina mome ba'a son raina nake haka ba wllh amma ae laifin suhailat din rufe min baki shashasha wanda ya kasa rike gidan sa dady ya fada
Yanxu sabida rashi mutunci irin naka tunda ta baro gidan ka baka taba zuwa dubata ita da yaron da yasami hadari ko bayan komene kai ka ja
Kuyi haquri in Allah ya yarda zanje haquri ya basu sannan ya tashi ya fita
Hmmmm alhaji yaron nan sai an hada masa da addu'a lamarin ya girmama to Allah ya sawwake
Daga gidan su gidan su suhailat ya nufa jiki ba kwari dan yasan Momeen suhailat ba wasa sallama yai a dakile mome ta amsa ko gaisuwar da kyar ta amsa ya jikin sultan ban sani tsohon mara kunya
Mome dan Allah kiyi haquri wallahi ba laifi na bane eheee lallai ba laifin ka bane shine zaku taru kai da matan ka ku kashe min 'yata da jikana ko to wllh da wani abun ya same su da sai munyi shari'a da kai ae ni ban san kai yaron banza ne ba sai yanxu
Mome dab Allah kiyi haquri ina sultan din yake au ina ma magana kai mara kunya ko sai ka tashi kaje inda yake ka dauko shi
Ita kuwa suhailat tana tsaye wanda tun shigowar sa take kyau ya kara yi mata nan taji son sa na kuma nunkuwa a ranta kamar baza ta fito ba gudun kar yai mata hulakanci a gaban mom yasa ta daure ta fito dauke da sultan
A sanyaye ta gaisheshi dagowa yai kai sai da gaban sa ya fadi ganin irin kyaun da tai masa fuska a sake ya amsa nan ta mika masa sultan
Tab wadda take fadan ma dan ita ta fito wajen mijin ta ba tare da wata damuwa lallai ma suhailat din nan momy ta tashi rai bace
Yana ma sultan wasa yana satar kallon ta duk wani abu da yake Ji game da ita ya daina sai ma wani son ta da karu a zuciyar sa
Da kyar ya bada sultan dan sam be gaji da kallon sa shi da uwar sa ba gani yake kamar ya sace ta su gudu
Yana fita mome ta fito kodai wallah anyi mara zuciya duk irin abinda yake miki amma har wani rawar kafar fitowa kike ko duk wannan abin dan na kwato miki encin ki nake mome wllh sam ba laifin sa bane
Sharrin matan sa ne ni kaina nasan irin son da yake min baya musu to shikke Allah ya kyauta amma ko sani ba inda zaki koma da sauri ta dago kallon da momy tai mata ne yasa ya sauke kanta da sauri
Shi kuwa Adams nan ya maida gidan su suhailat wajen zuwan sa duk da ba wata magana da take shiga tsakanin su da suhailat amma suna satar kallon junan in sunyi kuskuren hada ido sai su sakar ma junan su murmushi
Ko daga aiki ya dawo baya koma gidan da wuri sai ya biya wajen suhailat nan su khalisat suka kasa gane kan sa
A dakin khalisat suke zaune anya kuwa bakwa ganin kamar aikin nan ya warware dan ina zargin haka ko bacci bayayi sosai
Nifa jiya ina bincike ya wayar sa bayan ya shiga wanka pictures din sa nagani shida shegen dan da be mutu ba wata uwar ashar binta ta saki zai taba yihuwa ba wallahi
Nan take ta kira wayar kawarta naja'atu Ke ba lapiya ba wallh gaba daya aikin nan ya warware to ku kuma kawo kudi a kuma sabon aiki Karki damu wannan karon fa bazamu sassauta mata ba me kankat za'ae shikke nan karku damu
Shi kuwa Adams zuwan da yake yi yasa wata soyayya ta kuma kulluwa a ran su gidan su ya zarce wajen mome tana zaune da remote a hannun ta ah son ya akai Sosa keya yayi cike da kunya to yau kuma ni ake jin kunya gaskiya wannan maganr ba karama bace
Mome dan Allah Kije ki bawa Momeen suhailat haquri a dawo min da ita a razane ta tashi rufan asirin bazaka hada mu fadan da bazamu shirya ba agaban ka tace lokaci take jira ka basu takarda ba dani kai da kai laifi kai zaka je bikon matar ka
Mome dan Allah ki taimaka wllh ina mutukar son ta tab ba dani ba in na kuma zuwa sabida kana ganin baka sha wuyar dawo da ita ba Kila ma ku hadu ku kashe ta ba inda zani
By marsal
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
3⃣2⃣
*By 2besties💞*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
Mome ki taimaka kai tashi ka ban wuri ka dame ni
Fita yai ba kwarin jiki ko gida be huce ba ya tafi gidan su suhailat tun kan ya karasa magana mome ta daka masa wata tsawa lallai sai yau na tabbatar baka da kunya
Ae kaida suhailat kuma hmmm magana ta kare kuka yake mata sosai kamar wani karamin yaro
Kai kamaji London za'a kaita ta karo karatu kaje matan ka sun ishe ka haquri ba irin wanda be bata amma ina fir ta ki haqura
Gida ya koma rai bace ido yai ja kamar wani gauta ummie ce ta tawo tana kwarwasa zata taba shi ya hankade ta har sai da ta fadi kasa kallon kallo akai tsakanin binta da khalisat
Da ido binta tai mata inkiyar ta bishi tana shiga yana kokarin cire kaya honey wai me yasame ka ne mari ya fara zuba mata sannan ya zaro belt ya fara dukanta ta ko ina da gudu ta fito
Binta da ummie kuwa mamaki ne ya hana su guduwa nan ya hada su gaba daya ya fara tafka shegu en iska kun rabani da matata me hankali
Wallahi kuka sake muka rabu wallh gaba dayan ku sai kun gwamce baku sanni ba ya shige ya barsu suna kuka
Wajen dadyn su ya nufa yana kuka ya fada masa komai sai da yai masa fada sannan ya kira dadyn ta shima kin yarda yai
Kamar wani zararre ya zama duk wanda yasan zai fada aji ya fada aje a rarrashi gidan su suhailat amma ina
Da kyar mome ta yarda an fara shirye shiryen komarwa ta wani farin ciki ne ya ishe su duk su biyun kullum yana gidan makale da ita
Su kuwa su binta kuwa wata tsanar suhailat suka kara satar fita sukai gaba dayan su naja'atu tai musu jagora zuwa wajen boka me kankat
Wasu damun kudi suka ajiye masa boka so mike ka haukatar da ita hauka mara warkewa dariya yai yace angama
Tun lokacin da akace zata dawo yake kuma kawata mata bangaren ta
Cikin dare mome taji ihu tun yana kasa kasa har Taji yayi yawa da gudu ta taho suna rige rige da dady
Daga bangaren suhailat suka jiyo suna shiga suka ga suhailat ce take ihu gashinta yai buzu buzu
Kuka mome ta saki wayyo na shiga uku me nake gani kardai ace haukace wa kikai ganin surutan da take kuma tana surutai ya tabbatr musu suhailat ta haukace kuka suke yi har dadyn
By marsal[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
3⃣3⃣
*by 2besties*
_Salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
Tufafin jikinta suhailat ta yaga tana dariya da kankame momy tana fadin momy gasunan da garwashin wuta zasu konani,gasu da bakin kaya
Kuka momy take tana mata tofi
Yayinda kanwarta wasila tashigo tana kuka itama
Dady ya rige suhailat aka daddaureta da jikin karafunan gadon,sai ihu take momy bata fasa,mata tofiba
Dady cikin tausayawa yace saidanace kar ayi aurannan kika matsa gashi ai sunaso su mata lahani
Ita dazaman auren nan tagamashi har abada
Momy tace,alhaji ko da ace kai zaka yarda mu kara tarayya da iyayen adams a matsayin surukai bazan taba yardaba kalli yanda sukeso su illatamin yata tilo gaskiya dasake lamarinnan
Dady yace yakamata hajara mu dauketa mukaita kauye wajen malam dikko,yamata rukiya,in Allah yasa ta warke sai mu mata bizza ta tafi london tayi zamanta acan har Allah ya kawo mata miji,
Momy tace duk abinda kace alhaji shi za,ayi amma muboye sirrinan kar dan iskan yaronnan yaji yaje ya saceta,estate din dazata zauna azuba ma,aikatan tsaro sosai.
Basu gama rufe bakiva sukaji sallamar momin adams da dadynsa da adams din a parlour anzo tafiya da suhailat
Tsaki momy tayi tace wai me mutanen nan suke nemane iye?
Dady yace rabu dasu
Wani ihu suhailat ta kwallah wanda yayi sanadiyar jawo hankalinsu adams dake zaune a falo suka shigo ana rige rige
Adams yaje jikin gadon yana masoyiya mai yasameki ?waya miki haka?
Momy ta dagamai tsawa tace adams matsa daga jikin gadonnan kafin ranka yabace duk wayajawa yata shiga halinnan kaida iyayenkane sanadi don haka bani baku har abada.
Momyn adams tace hajara kinsan abinda kike fada kuwa iyeh?yanzu baki yarda da kaddaraba kenan,har mu kike zargi da hargitsa rayuwar suhai?
Momy tace eh ke yayatace amina but dake da dangi na tsaneku banason ganinku ,daga yau bani bake,kuma Allah ya isarwa yata sai kunga sakayya .
Momin adams ta fashe da kuka yayinda dadyn adams yace
By marsal
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
3⃣4⃣
*by 2besties*
_Salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
Mome dan Allah kiyi haquri wallahi ba.....da hallacan rufe min baki duk ba sanadin ka bane akai mata haka kuka sosai Adams yake
Ita kuwa suhailat bata san me take ba,tana ta ihun ta na mahauka ta
Kin gani ko Amina kin ga halin da kuka ja 'yata ta fada ko to wallahi Allah ya...da sauri ta toshe mata baki haba hajara kar fushi yasa ki manta yanda muke dake mana kiyi haquri
Ki kyale ni wllh indai da raina sai kun bamu takardar saki dan wannan kaddararren auren dashi gwanda babu wace wahala ce bata shiga ba duk hakan be isa ba sai an haukatar min da ita
Adams kuka yake kamar karamin yaro ganin yana kokarin raba zumunci a hankali ya tashi ya nufi wajen suhailat kamo hannun ta tai wani uban ihu ya ta saki gaba daya hankalin yayo kan su
Wayyo dodo karka tabani kokarin guduwa take amma daurin da akai mata yasa ta kasa sai gaganiya take tana ihu
Adams momen suhailat ta daka masa tsawa fita kan nasa security su fita da ku tana nuna masa kofa
Cikin kuka mai ban tausayi Adams ya fita
Hajara in rai ya baci hankali Ke nemo shi kar ki zo ki na danasani a gaba momen Adams ta fada cikin kuka fita nace ban son ganin ki
Haba hajara be kamata kina haka ba kin san bawa baya taba huce kaqaddarar sa kiyi haquri kisa tawakkali mana,
kana ga irin cutar da sukai mana kai wallahi kika kuma magana sai ran ki ya ya baci ba shiri tai shiru tana share hawaye
Bari na kira malama dikko muji ya za ae tom alhaji, cikin sa'a yana kiran sa wayar ta shiga da sallama ya fara
Alhaji ya gidan eh to lapiya amma ba kalau ba subhanallah me ya faru wato yau ne muka tashi da wani bakon lamari anan gidan nawa,
Yar wajena suhailat ta tashi da hauka ya salam.to shine na kira naji me ya kamata ayi
Yanxu dai kamata yai ku taho da ita sai muga me yakamata ayi mata tom malam an gode madallah in Allah ya yarda zamu tawo
To Allah ya sawwake sai kun karaso to malam nagode ya kashe wayar
Ya alhaji me malam din yace?
By marsal💞[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
3⃣5⃣
*by 2besties*
_Salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
Yace mu je can sai a ga me ya kamata ayi mata to Allah yasa a dace Ameen
Ta maida kallon ta ga suhailat tayi kasake abin tausayi mudai marsal kau da kanmu mukai sabida tausayin ta
Je ki kawo mata abinci wllh Kaga ni na manta ma sabida sam bana cikin hayyacina ta fita debo mata abinci
Kurrr dady ya kafa mata ido yana kallon ta wai yau suhailat ce a wannan hali yarinya yar gayu ko a mafarki be taba ganin tana shirme ba amma yau gashi tana hauka
A parlo wasila ce dauke da sultan yana kuka tana jijjigashi sam Yaki shan madarar sa tana kuka tana bashi da kyar yake karba
Haka mome ta kawo mata abinci tana ajiyewa suhailat ta warce plate din ta fara ci hannu bibbiyu duk su biyun sun kasa wani motsi sai kallon ta da suke yi cike da tausayi ruwa ka dauka ta sha
Ragowar ruwan da ta sha ta watso musu a firgice suka tashi je far da cup din tayi take ya fashe ita kuwa ta fara haukan ta
Am hajara ki shirya ta sai mu tafi aeyi komai akan lokaci to amma alhaji baza ta bari na shirya ta ba sai na sami wanda zai taimaka min to bari a turo ma'aikata tom
Shi kuwa Adams har ya fara ficewa daga hayyacin sa sai surutai yake yi ko gidan su be je ba yayi gidan sa
Su ummie suna zaune a parlo anci kwalliya,khalisat wasu shegun kaya tasa ita kuwa binta nail polish take ma kafarta shigowa yai a firgice
Yaso basu tsoro amma suka dake tashi khalisat tai ah ango ango ina amaryar mu ko kallon ta be ba,
Mahauciyar amarya zaki ce ummie ta fada gaba daya suka sheke da dariya har yai gaba ta jiyo a fusace kujerar dining ya daukko ya fara dukan su da ita
Wayyo shima ya haukace ku taimaka mana amma ina ko hanyar guduwa babu sai da yai musu lis sannan ya tafi dakin sa ko ganin gaban sa baya yi tsabar tashin hankalin da yake ciki
Dube dube yake har yakai inda wine din sa yake take ya dauka ya kafa kai sao da ya shanye kwalbar duka sannan ya jefar in few seconds bacci yai gaba dashi
A dakin suhailat da mome ta kai hannu zata taba ta sai ta doke tana ihu ganin haka yasa sauran suka kasa zuwa inda take tsawa mome ta daka musu kufice ku bani waje en iska yau suhailat din ce abar gudu
Ku fita gaba dayan ku na sallame ku daga aiki ko kaya kar ko wace shegiya ta dauka sum sum suka fita kar munafukai
Wasila ce ta shigo dauke da sultan tana ganin su tai wajen amma sabida a daure take ta kasa sai kara da take yi dady ne ya shigo wai me kuke yi haka ne har yanxu
Karbar sultan yayi don wasila ta taimaka amma ina da kyar suka jira mata doguwar riga
Suna rike ta tana fusgewa alhaji ba wani abu da zaka iya yine Kaga ba bari zata tai a kaita mota ba kuma kar muje tai wani abu a hanya
Waya dady ya ciro ya kira doctor sai da kiran ya kusa tsinkewa sannan ya dauka alhaji bana kusa ya akai am dan Allah kazo da matsala ka tawo da anaesthesia(allurar bacci) lapiya alhaji kai dai kawai kazo ina jira ka ya kashe bejira me zaice ba.....
By marsal💞
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
3⃣6⃣
*by 2besties*
_Salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
_Masoya dan Allah kuyi haquri na rashin posting din da bamuyi ba Kwana biyu hakan ya faru sakamakon makaranta kuyi haquri in sha Allah zamu yi kokarin muna yi ko kaka ne mun gode da kaunar ku_
Cikin sauri doctor ya karaso iso wasila tai masa har dakin ganin ya girgiza gani halin da suhailat tai
To alhaji me zan mata eh zamu fita ne shine muke so kai mata allurar bacci sabida doguwar tafiya zamuyi kar ta tashi a hanya a sami matsala
Hada allurar yayi gaba daya su ukun ne sukai kokarin ka mata amma da kyar suka iya dan wani karfi ne yazo mata cikin kwarewa doctor ya danna mata allura
A hankali bacci ya fara dauke ta har hawaye saida doctor yayi sannan ya fita yana jimanta musu
A mota suka sata suka kama hanya sai kauye suna fata Allah yasa a dace mukuwa muka amsa musu da Ameen
Gaskiya na gaji da wannan ji irin dukan da yai min akan wannan shigiyar wallahi ba riba ni tunda nake ba'a taba duka na ba amma sanadin wannan auren gashi har jini aka fitar min khalisat ta fada ta fashewa da kuka
Ae kuwa bazaki ce haka ba duk abinda akai sao yau dan an sami tangarda Kice haka ummie ta fada wllh duk da naji dukan nan dan tunda nake ba'a taba yimin irin sa ba amma ban damuba wllh binta ta fada
Ummie kuwa da kumburarran bakin ta
Ae ni zan iya komai dan naga na fitar da kishiya me ummie da fada
To me kike nufi da haka cikin masifa binta ta fada eh xan iya fitar da kishiya to wllh kin ganni nan zama daram dam ba inda zani wllh sai dai ku dan yanda nake ta fari haka nan sai dai ku fita ku barni
Haba wannan wane irin masifa ce haka ga duka ku kuma ga masifar ku nidai wallh nagaji khalisat tai dakin ta cike da tsamin jiki
A zauren gidan malam suka zauna wanda har yanxu bacci take bata farka ba
Zuwa can malam ya shigo kun karaso sannun ku yawwa tana ina gata nan mome ta nuna ta
Zungurar ta yai da sandarsa a zabure ta tashi tana zare ido tana kokarin guduwa ya daka mata tsawa zauna
Kwarjin yai mata ta zauna tana muzurai kare mata kallo yai wato alhaji wannan sihiri ne akai mata kuma in Allah ya yarda zamu gano bakin zaren
To Allah ya taimaka malam zam zam yasa aka kawo masa yayi addu'o'i a ciki karbi ki sha ya mika mata banza tai masa tsawa y kuma yi mata itama tsawa ta daka masa bazan sha ba
Tashi yai ya fara watsa mata ruwan aaddu'a tana ihu yana watsa mata har sai da ya kusa karewa
Jikin ta ne ya saki gaba daya ta fadi jagab
Mikama mome yai ragowar yace ta bata hannu na rawa mome ta karba ta dura mata
Wani irin gurnani ta fara kamar wata damusa wata zabura tai ta cafki mome da kyar su malam suka rike ta
Karatu malam ya kunna sannan ya fara zuba mata wani rubutu a jiki ka tsaya Kar ka Kona ni sani akai
Kallon kallo sukai malam yace to zaka fita ko kuwa shiru yai batai magana ba kuma watsa mata yai kara ta saki wadda gaba daya sun tsorata mome ta kan kake dady tana kuka
Zaka fita ko sai na Kona ka bazan fita ba domin ammin alqawarin jini kullum sai an kawo min to kuwa yanxu zan Kona ka tunda taurin kai zakai min
By marsal💞
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
3⃣7⃣
*by 2besties*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
_we dedicated this lovely and specials page,to our sweet mums,we love you dearest mums,no one like you in this word,we wish we will be 2gether😭_
*God bless you mothers*
●ayoyi masu ma,ana yadinga kona aljanin dashi,suhailat ta galabaita,tamkar ta rasa ranta,mallam bai fasa karatun al,qur,aniba,
Wani kara suhailat tasa ta zube,kasa sai barci,
Mallam yakalli momy dake kuka yace hajiya meye abin kuka alhamdulillah yarki tasamu lfy,amma karku kara barinta ta taka garin abuja
Dady yace jazakhallahu khairi mallam,ai insha Allah daga nan sai england london zata wuce ,taje tayi rayuwarta acan,
Alkhairi mai yawa dady yawa mallam, dakyar ya ansa,suhailat ta farfado tana dube dube,bakinta yayi nauyitakasa tambayar abinda yasameta,
Ahaka sukayi sallama da mallam suka wuce mai duguri,
Daddy ya canzawa suhailat wayoyi harda sim,ya rabatada duk abinda ya danganci namijin gaske
Suhailat kuka take takalli wasila ,ahankali tabata number tace kibawa masoyina namijin gaske duk ranar daya nemeni
Dady yace wai suhailat bazaki taho mu tafiba? ,
Suhailat tace dady sultan dinafa?pls dan Allah abarni intafi da sultan dina?
Abinda dady baitaba mataba yau shiya mata tsawaya daka mata yace ke! Inkika kara ambaton abinda ya danganci su adams sai ranki yabace,sultan wajen ubansa za,akaisa kuma kun rabu har abada.
Wiwi suhay tasa kuka,dagudu taje ta rungumi momy tare da sultan tana momy zan rabu daku badan nasoba,zanyi kukan rashinku,
Kuka momy tasa itama,yayinda suhay ta kalli sultan daya rike mata hannu gagam yana wasa,kuka takara fashewa dashi tana sai wata rana yarona.
Wasila ma kuka take tana daga mata hannu,mota sukashiga,sai airport inda tashiga jirgi tana kuka,tana dagawa dady hannu.
Tunawa tayi da namijin gaskenta,zama tayi har aka iso england din,
Fitowa tafarayi ,bodyguard da bakaken kaya tagani su biyar ga fararen motoci,anzo daukarta
Dayan yazo bude mata mota,ta rike murfin motar,cikin harshen turanci tace bana bukata
By
Marsal
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
3⃣8⃣
*by 2besties*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
★wani katan estate aka iso,bodyguard sunfi ishirin masu tsaron lafiyar katon gate din,estate din ya matukar haduwa
Galala suhay tasaki bakinta dama dady yanada irin wannan arzikin?
Bata gama rufe bakintaba saidataga an bude tafkeken kofar,majiya karfi ishirin,saida akayi checking din sauran bodyguard din da suhailat ta taho dasu,kar aje akwai namijin gaske acikinsu,saida akawuce hadaddun kofofi da gate goma,ko ina security na aiki,ga computer.
Wow harabar gidan ya matukar haduwa,ga swimming pool da lambu agefe,an shimfide filin da grasa cafet kore shar abin sha,awa
Ga mata zarata masu lura da wajen sunata aikinsu,lipter tahau,suuuuuuu saigata a hadaden falo wanda fadar haduwarsa karyane
Wasu mazane sukata shigowa da abinci,mata na serving dinta.
Ko ina computer yayi yawa,kome kakeyi ana kallonka,ga bindigogi ko ta ina
Tagumi suhailat tayi,tarasa mai yake mata dadi,tanason taji dumin mijinta ,takamu da azababben sonsa,kukane yakwace mata
Yayinda wata kunyangi tashiga tace ma 'alhaji yace kar abarki kiyi kuka,don haka kiyi hakuri
Suhailat tace kinga ba ruwanki da kukana,donme bazan yi kukaba narasa abokin rayuwana
*NIGERIA*
namijin gaskene ransa abace,ya kalli khalisat yace abinda kuka aikata kun kauta lesbian agidana innalillahi wa,innahiraihi raji,un,kunci amanata kun nunaku shedanune,kuje nasakeku saki biyu
Kuka khalisat tasa tana kayi hakuri darling,wallahi ba laifna bane ummiece ta jani
Ummie dake kuka tace wallahi karyane itace ta zugani,ita ta saniahanyar nan.
Binta sai disco take ,tana party damusu gwalo azuciyarta,yau Allah yataimaketa,wai ai inta rasa namijin gaske mutuwarta yaxo,yanda take kwasar kudi da abota da matan manya,Allah yasa dai kar yan iskannan su tona mata asiri.
Binta tace amma khalisat kunyi asara,kuji tsoran Allah kutuna zaku mutu ,kuma akwai hissabi
Ummie ta lankoyo ashar ta durawa binta tace ke harkin isa k mana wa,azi wacece shugaba,shegiya
Binta ta zaro ido tace nizakuwa sharri?
Adams yace kinga kema,bisu nasakeki saki biyu,ku baku isa ku sani kukaba macece tasani kuka ,kuma ita nakeso,ita zamu dauwama da ita,ku kuje kwa gani,duniyace inkayi maikyau kagani,kuma namuku alkawari zanje in nemo *farincikin raina*ko da ace zan rasa raina,kafin infito ko wacce ta tattara kayanta tabarmin gida
Kuka binta tasa tana wallahi karyane,pls kayi hakuri inasonka
Kuka suke sosai namijin gaske ko,ajikinsa ya dauki laptop dinsa mai nuns inda kake,yafara binciken wasila ta facebook,yamata friend request,tuni tayi accepting
Inda yagaya mata ,nan take wasilat tabashi numbar suhailat,da address din inda take a london
Farin ciki adams yacika dashi,yayi downloading din address din acomputer dinsa,yafara searching,abin yakusa ya firgitasa anya zaicika burinsa nadauko masoyiyarsa kuwa?
Ko ina securities ne,gidan nasama da kasane,ko ina akwai security da bodyguard majiya karfi da akayi shekara ana basu trainning,ga computer ko ina aiki yake
Motsi kadan zakayi ,kaji bindiga,ga katon gatedin wanda sai majiya karfi ishirinne zasu iya budewa.
Salati adams yake,gashi ji yake kamar yamutu saboda,sonda yakewa suhailat anya burinsa zaicika kuwa,gashi mahaifinta baya magana sau biyu
Neman wasila yayi again a whatsapp ya gaya mata abinda yake faruwa,
Wasilat tace yaya adams maizai hana kayi shigar mata,ko kayi shigar wani bodyguard dinta kaje ka ceci masoyiyarka dagarayuwar kunci?
By
Marsal
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
3⃣9⃣
*by 2besties*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
Adams yace no bazan iyaba,ajarumina zance,bawai ragoba,zanyi amfani da hikimata da basirata in lalata computer din gidan gabaki daya
In duki na duka,indauke masoyiyata ingudu da ita,muje muyi rayuwarmu da ita koda a karkara.
Wasila tace yaya adam kana ganin suhailat zata iya rayuwar karka?kodayake garin masoyi baya nisa,Allah yabaku sa,a nidai dan Allah ka lura da kanka ko ina tarkone agidan
Adams yace- badamuwa indai zan dauke masoyiyata,ai shikenan,
*ENGLAND*
_suhailat kwance take,tana kuka da tunanin namijin gaske,da rayuwardasukayi abaya,da kukan rashin sultan kusada ita,_
Kuka tasaki mai ratsa zuciya,tana ina kakene namijin gaske,masoyina nasan zakazo ka ceci masoyiyarka daga wannan kuncin rayuwar,inajin kamshin ni,imantacciyar iska ma,ana kana tafe masoyina
Tashi tayi tabude labule,gizo idonta yake mata koyaya,namijin gaskene a tsakiyar gidan,bodyguard sun zagayesa sun nunamai bindiga,
Gidanne yayi duhu,ma,ana namijin gaske ya lalata,cameras da lantarkin gidan,
Bodyguard suka nemasa suka rasa,,lipter yahau,domin isa falon da suhailat take,suka artabu da bodyguard,
Da sauri yasauka daga lipter,sunata kaiwa juna naushi da bugu,cikin zafin nama namijin gaske yake gocewa,
Suhailat ce tashigo falon dagudu tana kukan farinciki
Rungumar juna sukayi yana aika mata da sakon kiss
Jijjigashi suhailat tayi tana adams ba lokaci ka rufe,babinnan,wallahi in bahakaba rayuwarmu tanq cikin hatsari,muyi sauri mubar nan
Basu ankaraba sukaga ,bodyguard da securities sunfi talatin,sun kewayesu,kowanne dauke da bindiga a hannunsa
Suhailat cikin damuwa tace mijina kaga abinda nake gaya maka ko?yanzu meye abinyi?
Murmushi namijin gaske,yayi shima yazaro bindiga yadasa awuyar,suhailat yana mai bawa bodyguard din umarni yace duk wanda ya dan motsa wallahi saina kasheta,nima inkashe kaina,kowa ya ajiye bindigarsa,akasa inbahakaba wallahi saina kasheta
Ahankali kowa yayi surrender,namijin gaske,yahau lipter,sukafita,suka hau mota,wani fuska yasa,yayinda suhailat tayi shigar tsofaffi,har aka gama checking a airport bawanda ya ganesu,
A nigeria suka sauka,inda suka tari mai taxi,sukace ya kaisu kauyen daura,
Anzuba policawa da airforce ,gidan t.v da radio duk ana neman namijin gaske
Namijin gaske yace suhaiy dita zaki iya rayuwa akauye?
Girgiza kai suhailat tayi tace zanbika ko cikin rami zamu shiga tare;mu rayu tare mu mutu tare,ko da ace duniya duk takika ni inasonka,zamu dauwama cikin farin ciki da annashuwa,
Hellcopter sukaga ya gifta,kasa sukayi suka buya,awani daji maiban tsoro
Macizine katoto ya buyo ta bayan suhailat ya harbeta,kara zata saki namijin gaske yayi hanzarin rufe bakinta
Ya dauketa cak,ya nausa cikin kauyen da ita,wani gidan jar kasa,mai dauke da bukkoki suka nausa,
Suhailat sai nishi take sama sama,can numfashinta yadauke.
Wata tsohuwace ta fito dabukar tana meke faruwa ayayannan
By
Marsal
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
4⃣0⃣
*by 2besties*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
Su wane a nan ne lafiya tana haska yar fitilal Kwana hannun ta ganin mutane a zaune yasa taja da baya a tsorace
Mutane ne ko aljanu ni yar nan yau me zan gani
Baba mu mutane namijn gaske ya fada ki taimaka mana dan Allah ko da ruwa ne
Matata tana cikin wani hali kallon inda suhailat take tayi kawance take kamar mara rai dan gaba daya bata motsi sai hannu ta kawai da yake motsawa
Tausayi ne ya kama tsohuwa jiki na rawa ta shiga bukkar ta ta debo mata ruwa a wani tulu mai sanyi
Gashi ta mika masa ya karba a hankali yake bata ruwan da kyar take sha sakamakon ciwon da taji ga yunwa ga shi ta galabaita
Sai da ya sha sannan ya mika mata,dan Allah zaki taimaka mana da wuri kamin gobe kinga halin da take ciki
Shiru tsohuwa tai kamar baza tai magana ba can tace ku shigo
Wani karamin daki suka shiga ga duhu ga zafi haka ya shimfide suhailat a wani karamin gado na kara
Ya zauna tana tai masa sannu
Daga ina kuke d'ana a wannan dare shiru yai be mata magana ba yana share zufar da take keto masa
Iya dan Allah ina so ki taimake ni da waje kamin Musa taji sauki
Too zaro ido tayi cike da tsoro tab babbar magana d'an nan
Lafiya dai iya? Ae garin nan yana da wasu dokoki wanda bako da kyar yake iya su dan tsaurin su
Kunga mu bama son bako sabida me gari yace zuwan baki yana haifar da matsala
Kuma da rana ce ba wanda zai kalle ku in ma ba'a bi ku da jifa ba innalillahi wa'inna ilaihir raju'un namijn gaske ya fada
To yanxu ya za'ae ya tambayi tsohuwa to akwai wani me magani acan gangare idan gari ya waye sai a kira shi in ta wake sai asan me yakamata ayi
To mun gode nan ya nemi mafici ya dinga yima suhailat fifita a haka bacci ya kwashe shi
Sai asuba yaji tsohuwa tana masa magana firgigit ya tashi jikin sa duk yai tsami ga ciwon da yake masa
Bari naje nai ma me magani magana kamin hantsi yayi a cika to iya sai kin dawo ta fita tana yafa mayafin ta aka
Shi kuma ya tashi ya debi ruwa yayi alwala yai sallah ya zauna jira tsohuwa ga yunwar da take damunsa
Can sai ga tsohuwa ta dawo tare da wani mutumi yana biye da ita shigo malam
Shigowa yai kallon sa Adams Ke yi wata shiga yai ga layi a daure a jikin sa
Nuna masa suhailat tayi,
Sannan ya karasa ya fara dube duben sa har ya gama ba wanda yai magana
Wani daurin magani ya bayar ga wannan adinga bata tana sha wannan kuma a shafa mata wajen ciwon to angode tsohuwa ta fada
Gefen zanin ta ta kwance ta ciro wasu dan kudi ta mika masa
Da sauri namijn gaske yai magana a'a iya ki bari na bashi bari d'an na ae bakomai
Ta fita tana kara sa maganr ta wuta ta iza hadawa nan kuwa hayaki ta turnuke suhailat da Adams suka fara tari
A haka har ta gama sannan ta kawo musu wani koko yayi wani baki yunwar da yaje ji ne yasa ya dauka yana kafa kansa wani karni ya bugi hancin sa "ya salam"
Da kyar ya iya sha amai na taso masa haka yasha da kyar
Dai dai lokacin suhailat ta farka ruwa ya fara bata sannan ya rike kokon ya fara bata karnin yana bugar hancin ta ta fara kwara amai
Tsuhuwa tana waje tana sakar kaba tajiyo kakarin amai da sauri ta shigo lafiya ta fada iya amai take yi Ayya sannu nan ta taimaka masa suka gyara ta
To ko kokon ne bata sha eh to ina jin shine to bari naga ko kwad'on rama ne ae mata dan kar ta zauna da yunwa
Lokacin har makwabta sun fara firfitowa sabgogin su....
By
marsal
[30/04 3:41 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
4⃣1⃣
*by 2besties*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
Marka wai me kike yi ne haka tun d'azu naga kina shige da fice?
Wata tsamurmurar mata ce me siffar aljanu ta fada
Kai zanga lokacin da zaki daina gulma delu wai shin ma ina ruwan ki da abunda nake yi?
In banda gulma irin taki Ke da bashiga harkar ki nake ba shine yau kike tambaya ta to ban sani ba munafuka uwar munafukai
Ke marka Karfa ki zagen dan wllh kika fadan mara dadi sai kinji ba dadi bar ganin Ke tsohwa ce ko kece bishiyar dabino dan tsufa sai na rama
Oho ma dai duk son ki da gulma wannan dai baza ki ji ba sa'idinawa tashige ta bar deluwa tana masifa
Eh maji ma gani duk wani abu da ake rufe mana da kafarsa zai zo ya same mu duk Daren dadewa eheee!
Da kyar suhailat Ke cin kwadon raman da aka kawo mata
Adams dan Allah ka komar dani gida zan mutu,
kar na mutu banga mome da sultan ba kataima ka min
Kiyi haquri suhailat zuwa nan da wani lokacin in sha Allah zamu koma
kinga yanxu da matsala kuma kin san bada sanin su na daukko k ba kina ganin irin neman da ake mana,kiyi haquri
Kuka ta fashe me tsuma zuciya haba suhailat kiyi haquri komai ya farko zaiyi karshe
Sannu d'an nan tana ci ne? eh iya tom in ta gama sai ka bata maganin ni bari naje wajen maigari nasanar masa da zuwan ku kamin munafukai su rugani Susa akore ku
To iya sai kin dawo Allah yasa a dace Ameen
Gumi dadyn suhailat ya share yana kaiwa da kawo wa a dakin lallai Hajiya kinyi gaskiya
Yaron nan ya raina mu kalli duk irin tsaron dana sa amma sai da yasan yanda yai ya sace ta
wllh indai kudi yana magani to sai na sa an nemo shi a duk inda yake an hukun tashi Ke bama shi ba har ita da ta bishi
Wata iska mai zafi momen suhailat ta furzar
hmmm alhaji ae sai da nagaya maka wannan hanyar da ka bi baza ta magan ce mana komai ba gashi nan ya batar mana da yarinyar mu
Kai ni ban san mai zance wannan auren ba ta fara kuka....
Wasila ce ta shigo dauke da sultan wanda Ke ta tsala kuka kamar ana kwakule masa ido
"Mome kinga sultan tun dazu yake kuka na rasa me yake damun sa ko zaki kar.......Ke da hallacen fita ki bani waje da me zan ji
Bayan bacin ran da uban sa yasa mu shine yanxu zai daga min hankali fita kan na bude idona
Kuka wasila ta sa ta fita tana kuka
Kai wannan wace irin rayuwa ce ya Adams me yasa zaka yi haka gashi kasa d'anka a wani hali shi da maraya sam basu da banbanci
Gashi yanxu sam ba'a samin ka a waya ina kuka shiga dan Allah ku dawo d'an ku yana tsananin bukatar ku,
Haka tai ta surutai kamar suna jin ta...
Sam be san dadin uba ba haka tai ta rarrashin sa har baccin wahala yai gaba dashi
Haba Amina wannan fa duk laifin ki ne
Ke kika nuna ma yaron nan duk abinda yake so sai ya samu tun bayau ba nake nuna miki illar haka ae gashin nan ya je ya sace mu yarinya
To alhaji.... Ke rufe mun baki sanda take cikin matsala kin magantu ne ko lokacin da yake hulakanta ta kin masa magana ne
Wallahi alhaji sam ban san haka ba sai daga baya yanxun ma addu'a zamu dage da yi dan ita ce kwai mafita to Allah yasa a dace Ameen..........
By
Marsal
[30/04 3:42 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
4⃣2⃣
*by 2besties*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
Sai da me gari ya sallami wasu maza sannan ya maida kallon sa wajen da iya marka take a gurfane
Lafiya marka ranka shi dade nazo ne da wani labari tare da neman alfar ma
Fadi bukatun ki fada na sauraron ki fadawa suka fada cike da kuwa
Ranka shi dade jiya ne cikin dare wasu baki suka shigo
Karya kike tsohuwa kinyi kuskure kin ma fada laifi wani d'an kanzagin bafadr ya fada
Alam ya dakata mai gari yai masa
Cigaba da magana marka
Jiki na rawa ta Cigaba da magana
Ranka shi dade suna bukatar taimako kuma gashi duk rauni ne a jikin su sosai musamman matar ta sa
shine yace nazo na neman masu alfarma a wajen ka ka basu izin zama ko zuwa lokacin sa zasu warke ne
Gyaran murya yayi sannan yai magana amma marka kinsan cewar bako wane bako muka yarda da shi yazo ya zauna anan ba ko?
Eh ranka shi dade cikin adalci irin naka muke so ka aminci ka basu izinin zama
Cikin iya magana da kirari irin nata tasa mai gari ya yarda da sharadin in aka sami matsala ko wani akasin za'a Kore su
Godiya nake ranka shi dade Allah yaja zamanin ka
Ta tafi tana godiya
Cikin farin ciki ta isa gida ta tarar da Adams zaune gaban suhailat yana mata fifita tare da lallashi
"Sunnun ku"
"Yawwa iya kin dawo?
" eh" ya aminci ki zauna "zuwa nan da wani lokaci"
Ina fatan zaka zauna da mutane da amana sannan sai ka kauda kan ku daga maganganun wasu jama'ar
Musamman na wannan gidan da gidan na gidan yawa ne cike yake da jama'a iri iri kuma kowa da halin sa
"Tom iya Allah ya saka da alkhaeri Ameen"
To yanxu ina zamu samu wajen Kwana kinga bazai yihu muzo mi takura ki ba
Wannan ba matsala bari na fara gyara muku can dakin dake gefen rumbu
Wani bangare ne ta shiga me dauke da wata karamar Katanga da kofar langa-langa daki ne Karami Guda daya mai dauke da gadon kara sai tabarmar kaba
Sai band'aki a gefen karamin tsakar gidan
Tsaf ta gyara wajen yayi kyau duk da na kasa ne amma ko ina ta gyara shi ba Kazanta
Ga inda zaku zauna can na gyara muku shi iya marka ta fada
Sai ku tashi muje kwafi sakewa acen tom
Koma suhailat yayi ya sako hannayen ta a wuyan sa sauka fito iya na gaba suna binta a baya
Eheeeeeee me nake ganin haka ne wai delo dasuke zaune ita da wasu mata
Gaba daya hankalin jama'an gidan yayi Kansu Tooo wata sabuwa
Lallai wannan munafukar tsuhuwar ina ta samo wadan nan?
Oho kinsan ta da neman suna da Jan masifa harira ta fada wadda Ke zaune taba tsinta
Sudai shigewa sukai suka barsu kowacce tana fadar abinda yazo bakin ta
Sai da suka shiga dakin sannan iya marka ta fita
Wani kuka suhailat ta saki mai tsuma zuciya
Kaga inda ka kawo mu ko tunda nake a rayuwa ta ban taba tunin zanzo nan ba ko a mafarki bare ido biyu
Rungume ta yayi yana rarrashin ta da irin nasa salon wanda yake kwantar mata da hankali...............
By
Marsal
[30/04 3:42 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
4⃣3⃣
*by 2besties*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
Bayan kwana biyu,suhailat tafara sabawa da rayuwar kauye,daukan tulu tayi,tace iya zani rafi in debo ruwa.
Iya tace anya yarnan za,ayi haka,kuwa da kinbar adamu ya debo,saboda matan karkarar nan tamu akwaisu da iya neman tsokana
Murmushi suhailat tayi tace a a iya badamuwa sonake insan gari,tunda adams yatafi gona ni na debo ruwa
Adu,ar kariya iya ta mata,yayinda suhailat ta tashi tanufi hanyar rafi,tana zuwa yan matane sosai wasu nahira da samarinsu wasu na wanki
Tulinta tasa acikin kofin,caaaa suka mata akai suna ke asuwa dazakizo kisa mana tulunki akoginmu,sai kin zuba mana guba munsha mun mutu
Suhailat tacika da mamaki tace haba bayin Allah ,ko maigari ya yarda da zamanmu agarinnan,kuma ai ance bakonka annabinka
Wata tasha jambaki tace oho miki dai,wayasan asalinki,duk nan munada asali
Zaginta suka dingayi wasu harda dungure mata kai,suhailat bata kulasuba harta gama diban ruwanta tatashi da niyyar tafiya
Wata tace dallah malama kin takani,ahankali suhailat tajuyo tace dan Allsh kiyi hakuri bansaniba
Tafiyarta tayi tana mamakin irin garinnan dabasa kaunar baki,
Sora kiris tafadar da tullinta,sakamakon ganin namijin gaske dawata sune zance,harda dariya
Hawaye tagoge tazo ta wuce takusa dashi,adams yace my dear inazaki?
Banza tayi dashi ita tasan dacin datakeji tayi nadamar sanin namijin gaske
Shan gabanta yayi,yana suhailat ko tsaya ki saurareni,kokari take ta raba tagefensa,kememe yahanata
Ajiye tullin tayi akasa tace wallahi adams ka cuceni ka yaudareni,kasa na ketare umarnin iyayena,ashe cin amanata kakeyi,wallahi Allah ya isa banyafe ba
Namijin gaske wace suhailat ki tsaya ki fahimceni
Wawan mari ta,wankamai tana harkana da bakin yimin magana,iye adams,ka rabani dajin dadin rayuwata ka kawoni karkara ina rayuwar matsi da wulakanci,wallahi nayi nadamar aurenka,
Wucewa tayi tagefansa tadauki tullinta tana kuka
Namijin gaske tun dayake bawanda yataba marinsa arayuwarsa,amma dawatace tamaresa ba suhailat ba day nuna mata kuskurenta
*kuyi hakuri da gajeran shafinnan masoya
By
Marsal
[30/04 3:42 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
4⃣4⃣
*by 2besties*
_salma ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
Suhailat tanashiga gidan tanufi,dakin iya tsohuwa,mutanen gidan inbanda harara da hantara ba abinda suke mata.
Kuka tasa,iya tsohuwa sai tambayarta take tana meye faru?
Inbanda aikin kuka ba abinda take,namijin gaskene ya shigo jikinsa yayi sanyi yace suhailat kishirya muje gida duk hukuncin daza,a mana gwanda amana
Tunanin suhailat ya tsaya cak tazaro ido tace gidafa kace?haba adams ko karen haune ,yake cizonmu bazamu tunkari gidaba,sokake a kashemu?
Iya tsohuwa tace adamu kana nufin yanzu gida zaku tafi bayan anriga ansaba.
Namijin gaske yace eh iya,ai wataran zamuzo mu kawo miki ziyara bazamu manta dakeba suhailat taso mutafi
Kuka suhailat tasa ,badaman musu tatashi,har bakin titi iya tsohuwa ta rakosu tana kuka suhailt mata tana kukan rabuwa.
Bus suka hau zuwa tasha,sukaje sukahau motar zuwa abujah.
Ana magriba suka iso,gidansu,maigadi sunanan da bodyguard gaisuwa suke ta kwasa,namijin gaske baibi takansuba yaja hannun suhailat sukayi shigewarsu ciki,ba abinda yasamu lafiyar gidan,saidai anzo ankwashe kayansu binta
Wanka sukayi,suka dauro alwala sukayi sallah,suhailat tadafa musu abinci sukaci.
Sunacikin cin abinci sojoji suka shigo,ajiye abincin namijin gaske yayi daya tsinkayi muryar dadyn suhailat yana officer arrest him,
Sojoji,suka nufo wajen danamijin gaske,yake zaune ya kura musu ido.
Suhailat ta kalli mominta tace momy?momy pls kice wani abu karki bari akama adams bashida laifi ko kadan.
Dasauri momy ta iso wajen ta wanke fuskar suhailat da mari,tana dan ubanki ke mahaukaciyar inace,ana neman a kwato miki hakkinki kina shirmen banza,adama barawone yayi kidnapping dinki ,shine kike goyamai baya.
Suhailat tafashe da kuka,tana no no momy,karku rabani da farincikin rayuwata,karku maidani karamar bazawara,.
Dady abin yasa ya fusata yace officer what are waiting?for arrest him
Sojojin suka nufo wajen,da niyyar sawa adams ankwa,suhailat ta kankame adams tana wallahi bazaku tafarmin da mijinaba uban yayana ba,
Dady yabada umarnin aja suhailat gefe atafi da namijin gaske amai horo maitsanani,ba abinci ba ruwa ata hanamai azaba.
Wani imani ne yashiga zuciyar momy dataga yanda suhailat tazage tana kuka idonta yayi jawur,fuskarta ya kumbura tace alhaji kaduba yarinyar nan zata iya shiga wani hali,kadan rage tsaurin horan nan,abashi ruwa da abinci.
Dady yace hajara kinyi kadan nariga nafada ,bawanda ya isa ya chanzamin ra,ayi
By
Marsal
[30/04 3:42 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
4⃣5⃣
*by 2besties*
_salma Ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
*this lovely page is dedicated to salma novels group,and yarmama and hajur novel group,thank you for ur love and support* WLUSM
suhailat dakarfi tace dady..... dady..... karka manta kamin alkawari tun ina karama komai nakeso zaka iya min arayuwa,kudi baya siyan farinciki,ka tuna innalaha ma,assabirin,kuma karka manta duk wani dan adam ajizine,
Jikin dadyne yafara sanyi sannan suhailat ta dora,da dady katuna kataba bani labarin wata masoyiyarka da aka rabaka da ita,ka gayamin zafin dakajo har yakaika ka kwanta asibiti,kamin alkawarin cewa bazaka taba rabani da abinda nakesoba,dady karka manta koba komai akwai aure atsakaninmu,inagodiya ga Allah duk mugancin mijina baikai fir,aunaba amma haka asiya tayi hakurin zama dashi,balle ni mijina;ba mugu bane yanasona,shine farincikina.kuma kai ka gayamin,kowa yanada human right din dazaiyi abinda yaso,dady kai adaline baka danne hakkin al,umma,
Woooho suhailat tagama kashewa dady jiki gaba daya,ahankali,dady yacewa sojojin suyi tafiyarsu,
Namijin gaskene yaja hannun suhailat,sukaje suka durkusa agaban dady namijin gaske yace dady gamu agabanka kamana hukuncin daya dace damu,ka yafemana duk abinda muka maka.
Jim dady yayi annurin fuskarsa yadauke,kowannensa gabansa dukan uku uku yake,suna Allah yasa kar dady yace su rabu.
Ahankali dady yabude baki yace go in peace nayafe muku,ubangiji Allah ya albarkaci auranku yabaku yaya nagari,
Wani dadine yarufesu,suka tsinci kansu asabuwar duniya,godiya sukayi,yayinda suka rakasu dady har harabar gidan suka shiga motonsu ta alfarma
Suhailat taji badadi,dataga ba,a taho da sultanba.
Shiga ciki sukayi,suhailat tace wai my man inasu bintane naji gida shiru?
Bata rai namijin gaske yayi yace kowaccensu nabata takardarta saki uku uku namusu,iyayensu sukazo sukaban hakuri nace a a aisaki uku namusu suje da halinsu.
Jikin suhailat yayi sanyi tace to ubangiji Allah yashiryesu,yaushe zamuje muga su momi ne?
Namijin gaske yace saimun gama dirzar amarcinmune.
Suhailat tace saikace sabon aure kajika awurin
Murmushi namijin gaske yayi yace,kema kinjiki aike kullum kara sabuwa kike,
Suhailat ta kyalkyale da dariya tace banspn zolayafa Ka kyaleni.
Shishigewa jikinta yayi yanajin kamshin jikinta,kwantowa tayi izuwa cinyarsa,tazura hannu cikin sumarsa mai sheki da laushi tana shafawa
Atare suke lumshe ido,suna karajin tsantsar kaunar juna .
By
Marsal
[30/04 3:42 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
4⃣6⃣
*by 2besties*
_salma Ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
*this lovely page is dedicated to salma novels group,and yarmama and hajur novel group,thank you for ur love and support,,,godiya ga duka masoya wannan littafin a duk inda suke, wanda yawan su bazai sa mu lissafo su ba ,marsal muna tare da ku kuma muna kaunar ku a duk inda kuke*
A hankali suhailat ta zame jikin ta daga na Adams,honey nifa ban banji ana zance za'a kawo sultan ba,
Suhailat saurin me kike tab Kasan kuwa yanda nake son ganin sa kuwa wllh nima gaba daya hankali na yana wajen Sau daurewa kawai nake Adams be karasa ba yaji daga kofa ana magana
Marasa kunya da kunsan kuna son sa kuka sa kafa kuka gudu kuka barshi
Momeen Adams ta fada wadda take kokarin shigowa
Lallai Adams kun kyauta Kona ce ka kyauta so ya rufe ma ido ya hana ka ganin abinda yake dai dai da wanda ba dai dai ba ko,
Cikin kunya suka durkusa har kasa
Adams ne ya fara magana momee kiyi haquri wallh nasan nayi kuskure amma dan Allah kuyi haquri
Momee kuyi haquri kar kuyi fushi da mu,dan fushin iyaye akan dan su ba karamar matsala bace
"Bakomai suhailat 'yata wllh sam ban rike ku araina ba taso,ruko ta tai tana kallon ga cike da so,
Ae yanxu momen ki tai min waya ta fadan amma dan Allah kuyi haquri da junan ku shi aure dan haquri ne,kar ku bari shaidan ya sake shiga tsaka nin ku
Musamman kai ta nuna Adams to Momeen in Allah ya yarda za'a kiyaye ya fada yana sosa keya
Momee ina dady ?
Yana can aiki yai masa yawa ka samu ka shigo ku gaisa to momee
" bari na tafi Allah yai muku albarka Ameen Momeen
Tana fita Adams ya kamo suhailat baby anyya kuwa su mome zasu bamu sultan kuwa?
In sha Allah za su bamu,
Ae ko ba su ba mu ba sai kawai ki fara zubo mana wasu babies din, tab kaji ka wai na zubo kamar wasu ruwa kai an fada maka haihuwa wasa ne?
Ae kuwa nan da wata nin kadan nake so naga gidan na ya cika da raya
Hhhhhhhh......kaje a sake sabon auren ka da su binta in yaso sai ka sami yara da yawa,
Wata cafka ya kawo mata tuni ta kauce tana hak'i ,to Mene abun jin haushi ae gaskiya na fada ma
Hmmmm Allah na kama ki sai kin yi baya ni
Matsowa ya fara yi kusa ta da ita tana matsawa,to Mene nawa bayan daga ni har sultan din ba son mu kake ba duk irin wahalar da kake bani kai da matan ka, shi sultan ma yasan dadin uba ne, ta fada fuskar ta ba alaman wasa
Haba suhailat be kamata ki dinga dawo da abinda UA wuce ba kiyi haquri ki yafe min gashi nan komai ya wuce ya zama tarihi,
To kan ya zama tarihin fa wane azaba ne baka ban ba,har duka na kak......da sauri ya toshe mata bakin ta
Rungume ta yai kam suhailat kiyi haquri in sha Allah bazaki kuma kuka da ni ba sai kin Kasan ce a cikin matan da sukai sa'ar miji a duniya
Zata magana sai jin bakin sa tai a nata nan ya fara nuna mata salo salo na k'wararrun masoya, cak ya dauke ta suka nufi d'aki inda suka Lula duniyar masoya......
By
Marsal
[30/04 3:42 pm] Ya Ummi: *👟NAMIJIN GASKE👟*
4⃣7⃣
*by 2besties*
_salma Ali wadah_
↓
_maryam yarmama_
*(marsal)*
®online hausa writter
Ummie ce durkushe agaban tarin kayan wanke wanke kamar hauka,hawaye ne yake zuba kamar fanfo, gashi yanxu sam kudi sun dai na shigo mata tunda namjin gaske ya sake su,ta dawo gida aka kori en aiki gidan duk wani aiki ita Ke yi bawa flowers ruwa,har bude gate idan za'a shigo gidan ita Ke yi gaba daya gidan an dai na sabgar ta a dakin en aiki take Kwana
Zaki yi wanke wanke ko sai ranki ya baci mara mutun ci,Ke dai wallahi kin yi asarar hali shegiya kawai waya sani ma ko a isakan cin naki ko kin kwaso kanjamau,
kanwar ta Ke fada mata wannan magana,
Rahma ni kike fadawa wannan maganar ba gaba nake da Ke ba
gaban banza gaban wofi yanxu ina girman yake shashasha kawai maza ki gama Kije toilet ki wanke min panties dina in kuma har na gama abinda nake baki yi ba mu taru muyi miki dukan tsiya
Share hawaye tayi da kyar ta gama sabida ciwon da jikin ta yake yi,
Ita kuwa binta tunda ta koma gida abubuwa suka cakude mata wahalar da take sha ga shi ya saba da kashe manyan kudi dan haka ta tattara kayan ta ta gudu ta tafi ta hadu da en iska irin ta suka Cigaba da sheka ayar su
Ummie tana gama wa tai sauri ta shiga daki ta wanda yake cike da kwari iri iri beraye kuwa anan majalisar su take ci ban sa dunkoki wanda sun mai da tamkar dakin su
Wata kod'addiyar wayar ta ta ciro binta zatai ma flashing taji ba kudi nan take tai mata please call me,
Ita kuwa binta suna zaune da abokan isakan cin nata taji massage ya shigo dubawa tai wani ihu ta saki ganin number din ummie da sauri ta kira
Sai da ummie ta rufe kofar dakin sannan ta d'auka,
'Yar uwa ina kika shiga kika barni a cikin wahala Ummie ta fada tana Karasa maganar ta da kuka
Me ya faru yar uwa kike kuka binta ta tambaya wllh gaba daya duniyar taimin zafi ga wahala
Ayya ya akai kika zauna am binta yanxu ba lokacin doguwar magana bane Mene abinyi?
Kina gida ne eh ina nan to ya za'ae nazo na tafi da Ke
Da kin zo ki yimin horn zan fito amma daya zaki yi dan kar asirin mu ya tono, tom shikke nan ki zama cikin shiri
Kashe wayar tai cikin farin ciki yau zata huta da wahala dakin Rahma taje ta kwaso kayan,Ke ina zaki da kayan nan ko satar ce da kika saba a'a mome Rahma ce tace na wanke mata,to zan yi naga fanfon ciki ya lalace,kallon banza Momeen su ta bita da shi sim sim ta fice,
A compound na gidan ta zauna daga gefe tana wanke wa tana jiran isowar binta
Bata fi 10 minutes da Farawa ba taji horn ae kuwa da gudu ta fita binta ce da ita da wasu mata bude mata motar tai ta shiga da gudu sabida kar azo a iske ta,at high speed suka ja sukai ta fi....
Tun komawar khalisat gida taji bata da samun sake wa gashi ba abokan iskanci nan take tace wa iyayen ta ita baza ta iya rayuwar 9ja ba zata koma cen Malaysia ta karo karatu,batare da bata lokaci ba suka aminci
Ta tafi inda khalisat ta zama goggaggiyar yar lesbian ko wace me ji da kanta a harkar tana Hulda da ita ashe ita bata sani ba sanyin yai mata mugun kamu a verginer din ta wanda ha huce har zuwa ovaries nata...
Su kuwa su suhailat da Adams duniya ta zame musu sabuwa soyayyar su suke ba ta kura,
Inda aka dawo musu da sultan wani irin so Adams Ke nunawa suhailat kamr ya hadiye ta
Gashi ta kara kyau kamar ba ita ba ta kara fari ta murje luwai-luwai da ita son kowa
Zaune take a parlo ta gama shirya sultan nocking taji shigowa akai ta bayan ta taji an rufe mata ido
Wasila ban son irin wannan wasa bude mata fuska tai ganin wadda take a gaban ta yasa ta rungume ta cikin farin ciki
Hajiya hassana daman kina nan kin yada ni,
Ah suhailat kar kice min komai Ke ce da laifi,kika tafi ba wanda yasan inda kike,
Allah sarki yar uwa ta wllh har gidan naki naje ban same ki ba,ae munyi tafiya ne nida Abban yara shiyasa shekaran jiya muka dawo
Nan suka fara hiran kamar ba gobe
By
Marsal[8/23, 2:14 PM] Salmah💍 💅🏽: 👟 *NAMIJIN GASKE*👟
By 2besties
Salmah Ali wada
&
Maryam Yarmama
(Marsal)
®online Hausa writers
4⃣8⃣
♥ Ni kuwa suhailat ina abokan zaman ki naji shiru ban ji d'uriyar su ba, uhnnn kema dai hajiya kin so tsokana tuni kowacce halin ta ya jamata tafi ta,suna can suna girbar abinda suka aikata,to suna ina?
Yo hajiya waya sani, to Allah ya sawwake Ameen,,,,,,
************
Rahma ce kanwar ummie ta fito tunin kayan wanki ne ya harde ta,cikin masifa ta Fara kiran ummie ummie kina ina ne kin zubar ma da muta ne kaya sabida baki san darajar su ba ko to wllh yau zaki gane baki da wayo
Da sauri ta nufi dakin ta fayo ba ummie Ba alamanta ko ina sai da ta duba amma shiru lallai ma ummie,
Dakin Momee ta shiga Momee ke kika aiki ummie,wace magana kike haka kin san Ba a barin ta fita ko,to wllh Momee na duba sama ko kasa Ba ummie ba alaman ta,
Na shiga uku yanxu idan Alhaji ya dawo da wane Ido zan kalle shi na fada masa wannan magana,
Muje dai a aduba kan kace me sun bazama neman ummie sai dai ina tuni zakara ya bata sa'a ta ware
Haka ake ta neman ta amma har dare ba'a ganta ba,
Hajiya wannan wane maganar banza kike fada ba'a ga ummie ba sai kace wata karamar yarinya wllh Alhj nima Rahma ce ta fadan kuma tun lokacin ake neman ta har ynx ba'a ganta ba,
Tom shikke nan duk inda taje Allah karka bata sa'a,a'a Alhaji karkai mata baki wane baki kuma tunda haka ta zabawa kan ta zata gani, kuma ina nan ina jiran ta idan da raina ta dawo sai ta gane kuren ta.
Binta da naja ne suke zaune,uhmm kawata ni fa ynx na rasa gane kan ummie ynx gaba daya ta canja mana,
ni wllh ba wannan ne ke damuna ba wllh rashin kudin da neke fama dashi,
kema dai binta Kamar wadda bata shiga aji ba,
kefa oska yayi miki tayi akan harkar sa amma kin share wai ke tsoro,
wllh in kika zauna wata ran sai kin rasa abinda zaki ci,ni da ni ce sai dai kijini tuni na fara,
Wllh naja ummie sai ta san ni taiwa butulci na hada ta da manyan mata yanxu da sun janye ta sun daina harkar mu,
hmmm ae kece binta yanxu kece baki da sauran haraka duk kin kare,
Ko maza sun daina yayin ki bare mata, kije wajen oska ya taimake ki ki dinga samun na abinci ki ki,
Ke saurara kin zauna sai fadan magana kike,kema ba duk daya muke da ke ba,
Kin San fa oska Dan homosexy ne kuma Dan fashi,
Binta ba zaki gane ba ynx wannan kudin da na baki da badan gafza ba da ban samu ba kin san fa yaron oska ne amma kudi gare shi,
To zan masa magana yawwa koke ya Yar gari,
Wai su binta an kuma bata Allah ya kiyashe mu,masu irin halin Allah ya shirye su Ameen ya nesan ta mu da su.
Kinga yanxu ma wata harka zamu yi dashi zan fidda masa da koken america hajiya inna dawo ya kika ganni,wata shewa sukai sannan suka tafa.
By 2besties
Marsal💞💞💞
[8/23, 2:16 PM] Salmah💍 💅🏽: 👟 *NAMIJIN GASKE*👟
By 2besties
Salmah Ali wada
&
Maryam Yarmama
(Marsal)
®online Hausa writers
4⃣9⃣
*Sadaukarwa ga duk masoya wannan littafin,muna kara baku haqurin shirun da kuka ji mu*
🔶Nifa har na tsagu lokacin yayi wllh,kin ga bari ma naje na same shi,ta tashi jiki a yankwane Kamar tsohuwar aljana,to sai kin dawo
Wayar ta binta ta dauka miss called din oska ta gani take ta kira shi,
Cikin masifa ya fara magana wai kina Ina ne sai kiran ki ake baki dauka ba,ke ni fa Bana son rashin mutunci fa,
Tuba nake oga bana kusa ne to yanxu ki maza ki zo Ina jiran ki kuma idan kin sa baki amince na karki zo,
Ma yarda oga kit ya kashe wayar tare da sakin wata mahaukaciyar dariya
Cikin sauri ta shirya sai gidan oska,tun daga bakin falon warin wuwi yasoma bugar hancin ta haka ta shiga,
Maza ne da mata fal wasu na shaye shaye da bushe bushe wasu kuma suna bad'ala a sarari ba kunya ba tsoron Allah,
Tana shiga oska yai mata nuni da wani daki shiga tayi ya biyo bayan ta,
wata cafak yai mata Kamar wani zaki,
Ko jiran ta be tsaya yi ba Dan tuntuni ya dade yana maitar yin iskanci da binta
Sai da ya fara sex da ita kusan awa biyu yana Abu daya,
da yake itama ta dade batai harka da namiji ba,ta biye masa,daga nan kuma su ka koma homo,
wa'iya zubillah sai da ya gaji Dan kan sa sannan ya kyaleta ba karamin jigata binta tayi ba,
Amma da yake kuda wajen kwadayi yakan mutu sannan kuma da boyyiyar bukatar ta a ranta.
Haka ta koma gidan oska da zama sannu a hankali har aka fara fitar dare da ita idan zasu fashi ita da kawar ta naja.
Abubuwa sun fara cakudewa ummie sakamakon zuwan wasu yara an fara baya da ita a harkar sai ta kure take samun Wanda xasuyi harka da ita,
Wayar binta ta kira, yafi sau goma amma bata dauka ba,
Wayyo ni kuwa ina binta ta shiga ga wayar naja ya daina shiga cikin sa'a ta kira binta ta dauka wani uban ashar binta ta sakarwa ummie
Ke inbanda Yar iska ce mara mutinci butulu sai yau zaki neman,
a'a ba haka bane ki tsaya ki saurare ni, ke da halla rufen baki karki kuma kira na,
ki sake kika kuma kira na wllh sai na yi miki rashin mutinci da baki taba tunani ba shashasha kawai ta kashe wayar tana huce tare da busar da hayakin wiwi
Tun da satin ya kama su binta suke shirin zuwa gidan wani attajiri fashi ba karamin shiri sukai ba,
A haka har dare yayi suka debi motoci sai gidan tun daga farkon layin suke harbe harbe,
Harbin masu gadi suka fara sannan suka sami damar shiga gidan Alhaji badamsi giwa
Haka suka kulle matan gidan da 'ya'yan gidan harda shi kan sa alhajin a toilet
Gwalagwalai sukai ta diba sannan suka koma kan kudi,
Sai da Ku yashe tas suna shirin fita suka ji an far musu da harbi,
take wasu suka fara guduwa binta kuma tana kiran oska tana neman temakon sa taji harbi,
a kafarta sauran da suke waje suka yo ciki suka fara musayar wuta da yaran gidan maza biyu a haka aka kwashi su binta suka shiga mota suka figi moto at high speed
Ba tare da sun dibi kayan da suka sata ba suka gudu dan tsira da ran su,
Tun daga wannan lokacin alkadarin oska ya karye ita kuma binta sabida rashin kula da ita wajen jinya kafarta ta fara rubewa daga nan ta fara tunanin yanda zata koma gida Sam bata San inda naja take ba.....
By 2besties
Marsal💞💞💞
[8/23, 3:08 PM] Salmah💍 💅🏽: 👟 *NAMIJIN GASKE*👟
By 2besties
Salmah Ali Wada
&
Maryam Yarmama
(Marsal)
®online Hausa writers
5⃣0⃣
♠Gashi kudin da motar da zata hau ta dawo gida bata da shi,
haka ta fara bara tana tafe kafar ta Kamar ta cire Dan azaba ga wani doyi da take ko wajen bara almajiran basa bari ta zauna kusa da su gashi gaba daya duburar ta ta rarake ba irin danasanin da nadamar da batai ba,wai yau duk gatan ta ita take bara da tai haquri a gidan namjin gaske da tuni tana can wasu hawaye masu zafi ta goge nan tana almajirai suna gudun zuwa karbar sadakar en dubu dubu sabida kafarta sai da ta kare sannan ta isa,wajen wani mutun ne ya daka mata tsawa ke ba'an baku ba me kike jira nan tasa kuka tana ba'a bata ba,haka me bada sarakar ya leko ta window ya bata 2k,binta bata zame ko ina ba sai tasha haka tashiga mota ana kyararta har gida,
Me gadi kememe yaki bude mata kofa Dan kwata-kwata be gane ta ba,motar alhajin su ce ta nufu nan yaga ana fada da ita da kyar shima Alhaji ya gane ta yace a bude mata ta shiga
Ita kuwa ummie sun sato diomond a gidan wata hajiya matar da gano ita tai mata sata hajiya A'i ta aiko barayi sukai mata duka garin gardama irin tata ta jaho suka watsa mata acid a fuska nan fuskar ta kone idanuwan ta suka zama kanana ba kyan gani,
Da kyar ta samu a cikin abokan harkar ta aka sami wadda ta dauke ta takaita gidan su,
Kinga irin abinda kika jawowa kanki khalisat ko kin kaso auren ki gashi kin kwaso cutar da bazaki warke ba da kyar take iya magana sabida ynda cancer ta kama ta mome Dan Allah kije gidan Adams ke Neman min gafar su Dan nasan mutuwa zanyi na rage wani alhakin ko na sami Dan sauki tom shikke nan khalisat Allah ya baki lafiya
Wani murmushi tai mai ciwo a Daren ta mutu,
Suhailat zaune da katon cikin ta inda sultana take mata shagwaba sai ta kai ta wajen momeen adams,
Adams din ne ya shigo rike da hannun sultan Dan shekara shida sannu da gida uwar biyu murmsuhi tayi barka da zuwa honey
Daukan sultana yayi sai da ya zauna sannan yace hmmm daga gidan mome nake naji wai amyima dady waya binta ta dawo tana asibiti an cire mata kafa, garin yawon ta ta fara fashi aka harbe ta, tab Allah ya sawwake
Suhailat ta jajan ta mata kwarai,a daren wani abokin Adams yayi masa waya ya fada masa mutuwar khalisat har kuka sai da suhailat tayi duniya kenan kamin a gama zaman makoki suhailat taje tai musu gaisuwa momen khalisat na kuka tana fadawa suhailat sakon khalisat bakomai Momee na yafe mata Allah ya yafe mata Ameen.
Haka ummie ta koma kamarkamar mu jiya a gidan su ko yan aikin gidan sun fita sakewa a gidan ga fuska a kone idon ta saura kadan ya rufe sabida kankanta,
Haka nan bita itama haka take fama da sanda dan kafa daya gareta ga tsangwama rayuwa kenan abinda kashuka shi zaka girba.
Bayan sati biyu suhalit ta haifo katuwar babyn ta aka samata sunan moomeen Adam suke kiran ta da Nasrah,
Rayuwan jin dadi Adams da suhailat suke tare da 'ya'yan su gwanin sha'awa.
*Tammat bihamdillah ana muka kawo karshen wannan littafin namu me suna NAMIJIN GASKE Allah yasa sakon mu ya isa kunnen isar fatan masu irin halin zasu ji su gyara*
Godiya ta musamman ga Allah da ya bamu ikon rubutawa tun daga farko har karshe
Godiyaga duk masoya wannan littafin da suka biyo mu tiryan tiryan tun daga farko har karshe
Fatan alkhairi ga duk Hausa writers association
Bamu manta da duk wani members na group din mu ba,da kuma duk Hausa novels group.
Story and written by
2besties
Salmah Ali Wada(aunty)
&
Maryam Yarmama
2besties
(Marsal)💞💞💞💞
No comments