Sugar Mommies H
أم افنان✍️💞: Page *H*
Kamo hannun nuratu yayi dawo da ita tsakiyar falon yana rarrashinta ,ba tare da ya bi takan Fauza ba bare yasan a wani hali take .
Sai da ya tabbatar hankalinta ya komo jikinta sannan ya fara rawar jiki tsakanin falo da kicin ya dauko mata wannan ya bata ya dauko wannan ya ajiye duk dai abinda yasan mayb zata soshi yake dire mata ,tamkar dai yanzun nan ta shigo gidan ba dawowa yayi ya tarar da ita a ciki ba .
Ita dai Fauza saida tayi ta wurga ido tana kallonsu ta daɗe da zama speechless.
Nuratu ne ta ɗago kai takalleta "Anty ashe ke Anty ta ce"
Sakin fuskarta tayi da buɗaɗɗen murmushi
"Mamakin da nike tayi kenan noor ,muna raye daya daga cikin family member ɗin mu yina cikin irin wannan matsalar ? Ina amfanin arzikin da Ubangiji ya bamu ?
Shiyasa duk wani matsala da ka gani akwai wanda zai iya eradicating ɗin shi from the starting point,maana ba sai an cimma gomnatiba wannan primary responsibility dinmu ne da Allah ya barmu dashi amma mun kasa..."
"Aah Anty ai bakusan halin da nike ciki ba"
"Ai bamu matsanta bincike ba da mun sani ,You have been banned and forgotten...Haba wani abun kunya kenan wannan sun koreki fa kuma kowa ya manta dake"
"Anty nikanje ƙauye in na Tara kudin Bara saidai ba'a barina in shiga kona aika a kira mamana ta auri wannan mugun sabon srkin baya barinta ta fito kinga ba laifin kowa bane Allah ne ya jarrabeni kuma ban isa In tsallake jarrabawa na ba sai ranar da Ubangiji ya kawo mun iyaka "
Ahmed rafka tagumi yayi yina kallonta lallai yarinyar tayo hankali,shiyasa akace duniya makaranta na kwance baiga gari ba.
"Shikenan dai All praise be to Allah , a rufe chapter nan tuna bayan bayida wani amfani ,yanzu hakkin kula dae ya dawo kaina inshaalh bazaki sake kuka ba noor"
***
Sun yi sati guda tare tsawon satin nan bata da aiki daga barci sai cin abinci in lokacin sallah yayi ta tashi tayi .
A gefe guda kuwa Ahmed yaje ƙauyansu Kusan sau uku suna rabuwar Baran baran da sarki tunda dama tun lokacin mutuwar tsohon sarki sun dade da samun matsala ,so suna sa jikkansu koda yazo da rokon sassauci akan hukuncin da suka yanke ma Nuratu ba wanda ya sauraresa
Ga kwanakin komawarsa nata matsowa yafaa tunanin yakai ƙarar ƙauyen wa hukuma , saidai yina tsoron abinda kaje ka dawo .
Daƙyar ya samu magana da iya Talatu ,ta koɗe ta lalace sam ba rabinta
Tana ganinsa ta fara hawaye "Ahmad ka tsame hannunka a sha'anin wannan mutumin matsafine ,indai kayi niyyar taimakon Nuratu to ka maidata makaranta ,sannan ko aikatau ne ka samar mata don ta samu abunda zata rufawa kanta asiri basai ta saɓi Allah ba ,a jikina nikeji sharri akai aa ɗiyata ....
"Ke wuce gida !"
Tsawan da sukaji an doka mata kenan ta baya
A furgice ta waiga sarkine da zugegen dorina a hannu ,ciki tayi da sauri don tasan dukan sarki ba mai sauki bane
Daga murya Ahmed yai "Mama wani sako zan fada ma Nuratu ?"
"Gatanan na bar maka ita amana koda ta Allah ta kasance dani Allah bai hada fuskokin mu ba don Allah ku rokon mun ita gafara ,na gaza da sauke hakkin uwa da ya rataya a wuya na"
Zuuuu! Ya zuba mata bulala da gudu ta faɗa gidan .
Take hawaye ya tsiyayo ma Ahmed da sauri ya saka hannunsa a cikin Aljihu ya zaro handk yana gogewa
"Fitanmun a zauran gida"
Nunashi da yatsa Ahmed yayi "Kaci albarkacinta ,amma bacin haka sai na nuna maka kuɗi zai iya siyamun komai ciki harda takurarren karagar nan da ta saka izza da jin ƙuwwa ..."
Juyawa Ahmed yayi ya fita
"To na jiran sammaci,dukanta yanzu na soma tunda kwakwalwan tunkiyoyi gareta bata zubar mun da mutunci saboda karuwar ƴarta."
"Nuratu ba karuwa bace kaine nan dai kwarto ,tsohon banza kawai mai fuskar firauna wallahi sai naga bayanka,Kuma duk yanda zanyi inga na ɓantare ƙaddararren auren ka da mama sai nayi"
Cacan baki sukayi sosai kafin suka rabu ya kaɗa kan motarsa ,yina dab da barin gari ya hango wani yaro yana masa nuni da hannu ya keto ta cikin daji kansa da ƙullin damin rake.
Dukda a tsorace take saboda security purposes Amma ya zama keen ,bai fito daga motar ba .
Da numfarfashi Nuraddeni ya ƙaraso wajen motar ,ya tsaya yina gaishesa
"Nine nura kanin yaya Nuratu, Don Allah nima ka gudu dani wajen ƴar uwata kullum gori suke mun gashi basa bamu abinci sa munje wajen su Baba (Kakanninsu ta ɓangaren uwa) su kuma sun tsufa ,ga su yaya wasila duk sunyi aure ba a garin nan ba ,don Allah malam ka taimake Ni da iya zata iya mutuwa "
"Wannan wani irin masifa ne kai da kai anya bazai watsi da Alamarinsu duka ba ? Takan Nuratu abu yanaso ya zama dangi ? "
Bude masa ƙofar yayi ya shigo ya kulle ,kana yai gyaran murya yina basa hakuri
"Kaga Ni ba anan nike zaune ba bazai yuwu in ɗauke ka ba ,ina ne gidan Kakanninku? sai muje in rokesu su riƙeka hakanan... Inshaalh mamanka bazata mutu ba sai taga aurenku duka"
Murmushi Nura yayi "Allah yaso"
***
A gidan tsoffin nan sai sun baka tausayi a kauyen ma su talakokine bukkokine ɗakunansu an kewaye katangar gidan da Danni, kana ɗaga kanka saman ɗakunan zaka ringa hango hasken rana yina shigowa ta saƙo da saƙo .
Baka da maraba da kana waje ,wannan ya sukeyi lokacin ruwan sama?
Yina cikin Almajiransa yina bada darasi sukazo don haka ya ɗan dauki lokaci kafin ya samu keɓewa dashi.
Sunyi tattaunawa mai tsayi da baban iya daga ƙarshe ya ɗorar masa da jawabi akan kalma guda
"Tafiya da Nuratu zuwa wata ƙasa ba abu mai yiwuwa ba ne ,Ahmadu mun gode da karamci amma dole mu tuna da koyarwan Allah ,Ba iyakanka nike son gwada maka ba ,amma Inaso ne In tunasar dakai fadin Allah ,kai ɗin bakuda wani dangantaka na jini da nuratu ....Shedan yina yawo a tsakankanun Banu adam da zukatansu ,banaso ɓaraka ya faru .don haka Ni shawara daya na yanke yanzu haka ,tunda dai an samo yarinyar nan ,zan nema a cikin gardawan ɗalibai na wanda zai iya auranta mu bashi ita sadaka ,yanzu za'a ɗaura mata aure sai ..."
Ahmed katse shi yayi da sauri ya manta girmansa ma
"Ranku ya daɗe ,aure kuma? Ai tozartata zai yi. Aure Kum malam Nuratu yarinya ne bata isa aure ba"
Daure fuska yayi "Saointa duk sunyi aure da yaransu bana son ɗabiun yahudu da nasara"
"To naji ! A bata nagartaccen mutum mana wanda zai tausaya mata ya zama bango Kamar mahaifinta a rayuwarta ba wanda za wilakantata kamar yanda wancan mugun yake azabtar da uwarta ba kun barshi kun kasa raba auren"
"Bamu da wannan ikon ne Ahmadu karka tuhume mu da rashin Adalci "
"Shikenan Ni zan tafi bayan wata shida ina dawowa"
"Bazaka tafi da yarinya uwa duniya ba aure ba ,muce ma Ubangiji me? Kawai in kaje ka turota gida in sarki ya koreta zamu tattara mu fita garin damu da ita"
"Wai meye mafitar wannan masifa?"
"Ai mata aure sarki yace da zaran an mata aure mijinta ya sameta natsatsiya zai janye tsatsauran hukuncin sa a kanta"
Caɓe baki Ahmed yayi "To in Bata samu mijin ba fa?"
"Shine nace zan samar mata cikin Almajirai na"
Ransane ya ɓaci ,wai kamar Nuratu ne ake neman Wanda zai aureta ? Za'a nemo Almajiri a bashi ita sadaka?
"Ni a ɗaura auren dani?
Bai yi shawara da zuciyarsa ba yaji bakinsa yayi wannan suɓil da bakan
A take kuma kansa ya sara masa ya fara tuno matarsa da uwarsa anya zasu yarda da wanann bankauran hukuncin?
"Uhm uhm Ahmed idan hankali ya goce hankali ke tarosa ,babu nadama kuwa a hukuncinka?"
Daurewa yayi dukda yinajin kansa kamar yayi kuka "Nuratu amana ce a hannuna kuma na karba don haka hakkina ne In zaba mata miji ."
Godiya ya shiga yiwa Ubangiji ya fita tattaro Almajiransa a daura aure
Tagumi Ahmad ya rafka
"Bakayi wauta ba kuwa?
Tabbas nayi amma wannan auren zai zama na sirri ,bayan anyi zan dawo in wanke Nuratu a ƙauyansu tunda abinda suke so kenan,daga nan sai in sake ta ta samu mijinta mai sonta ba mai tausayinta ba ta aura ,na dai kashe wannan wutan"
Bai baro garin ba sai da auren Nuratu ,akan sadaki dubu talatin da biyu wanda suka kasance sauran canjin dake Aljihunsa
Ana gama daurin auren malam ya bashi sadakin ya kaima Nuratun amma ya girgiza kai
"Kawai kuyi amfani dashi kuci abinci in naje zan bata wasu "
Wannan shine mafarin tafiyar Nuratu Japan da Su Ahmed
Bai taba daukanta a matsayin mataba sai ƴar amana
Nuratu tunda ta shigo rayuwarsu komai ya sauya itace gyaran gidan girki da komai ,don haka kullum tana kallon tashoshin da suke koya girki na ƙasashe daban daban na turawa da larabawa .
Wannan ba karamar daɗi yayi wa Fauza ba ta sama mai aiki a sama duk wata Ahmad na biyanta itakuma sai ta kasa kudin biyar ta ɓoye kashi daya sauran ta aika ma mamanta gida .
A haka har ta gama secondary ,akazo shawarar karatun da zatayi a gaba da Sakandire tashin farko tace aikin jarida
Mamakine ya kama Fauza ta ɗago ta kalleta
"Noor why? Kina ganina I'm a doctor Yayanki maaikacin banki kr meyasa jarida?"
"Anty ke kika saka mun son aikin , saboda da ba aikin ɗebo rahotanni da har yanzu ina ƙasan gada sanadiyyar ki na dawo tsaftatacciyar rayuwa ,nima inaso in zama ƴar jarida inje in kwaso sauran yara marasa gidajen kwana irina a da!"
Murmushi tayi "To ai ni likitace"
"Ai a lokacin ya Ahmed cewa yayi aikin da ya kamata ƴan jarida suyi kikayi ,to Ni shi zanyi"
Ahmed dake gefe yina kallonsu kurɓan cafee yai "Shikenan abar bala'i tayi sleep😄🙊 Nuratu aikin jarida kike so ko ,yanzun na zan maki applying inshaalh zuwa dare Admission ɗinki na tare dake"
Wannan shine mafarin karatun Nuratu gashi yanzu ta kwashe zangon karatu na biyu a makarantar ma'ana tayi shekara daya
Yanzu shekarun Nuratu 19 duk wasu alamomin girma ya bayyana mata inda ta gama bajewa tayi manyan mazaunai daɗi ya huda ta ,ac yasa jikinta laushi rumumu koke mace sai ta motso Maki da sha'awa bare namiji .
Basuda matsalar komai a gidan sai rashin yara shima baya faduwa don basu taba nuna sun damu ba dukda Fauza ita ta ja ma kanta tun lokacin da take karatun medicine ta dinga shan maganin hana daukan ciki wai bazata iya haɗa karatu da rainon ciki da goyon yaro ba ,sai da ta gama shikuma ciki yace bai san wannan zancen ba gashi yau shekarunsu biyar da aure ba haihuwa
Ahmed a tunaninsa Allah ne bai kawo ba amma ita tayi bincike an tabbatar mata fallopian tube dinta ne ya tushe .
Don haka ta fara neman magani a net ta hadu da wani German doctor (Ɗan jamani) shi ya bata tips din da zatabi don daidai ta halin da take ciki
Ciki kuwa harda taƙaita kwanciyar aure da Ahmed bayan ta saka wani magani duk dare in zata kwanta,wanda shine zaije ya ringa wanko dattin har na tsawon watanni hudu in kuma ba haka ba saidai ai mata aiki .
Ta dauki shawarar likita ta fara yin maganin a ɓoye ba tare da sanin Ahmed ba ,a gefe guda kullum sha'awar Ahmed na ƙara karuwa amma baya samun wani gamsuwa a wajen ta ba a Sex da daddare sai da rana shima bata bari yai release a cikin jikinta sai ta waje.
Wannan ya haddasa masa fara sha'awar ƴar aikinsa takai ta kawo har mai afkuwa ta afku ga ƴar aiki ta ƙunsu😲🤰🏻
No comments