Sugar Mommies T
أم افنان✍️💞: *T*
16 wks later
Nuratu cikin dare ta tashi da matsanancin ciwon mara ga wani abu mai ɗumi tana jin yina sakko mata kaɗan kaɗan...
Tun tana cijewa har ta kasa ,sa rarrafe ta fita ɗakinta zuwa ƙofar ɗakinsu ta fara dukan ƙofar da tsinin takalmi tana kiran sunan Ya Ahmed a hankali
Fauza da Ahmed a tare suka dirko daga kan bed ɗin wannan na tura ɗan uwansa kowa ya ƙosa ya riga ɗan uwansa buɗe ƙofan ,Ahmed shi yai nasaran budewa anan ya ganta yashe a ƙasa tana haki zufa na tsatsafo mata a goshi kana ganinta yarkace yarkace .
With a trembled voice yace "Nuratu lafiya whats going on ?" Ɗaya masa hannu tayi alamun ya duƙa ƙasa ,da sauri ya sunkuyo ,ta janyo hannunsa ta ɗaura masa a maranta "Ya Ahmed I'm dying zafin raɗaɗin ciwon nan zai kasheni"
"How long it takes? Tin Yaushe kike ciwon baki fada mana ba" Fauza ta tambaya a mugun ruɗe
"Ynz na jishi amma ƙafana ya riƙe,wani abu kuma inajin yina fito mun"
Waigawa tayi ta kalli Ahmed "Love haihuwa ne fa ,mu kaita asibiti it's urgent kwaso mana takalmi "taje ta kamo kafaɗar Nuratun tana mata sannu
Ahmed a yanda Yike da kayan barci haka ya sako takalmi itane ma ya dauko mata hijabin sallah ya mika mata ,ɗagota suke ƙoƙarin yi saidai ta kasa sai hawaye da ƙarfi kuma ta fara nishi
"Oh what? Ki bar nishi nuratu zaki yaga kanki this is not the righteous time da zaki fara nishi"
Ina ta kasa amsata kuma ta kasa bata amsa,waigawa tayi ta kalli Ahmed
"Love taso mr. John a fita hakkinsa na uban ɗa a fada masa Nuratu zata aihu " ,tsawa ya doka mata
"Fauziyya dama da gaske bakida imani? Meye amfanin kasancewarki doctor idan bazaki iya mata wani abu ba?"
"Love na rude ne sai inajin kaina kamar dankali kamar ban iya komai ba "
Dukda raɗaɗin ciwon da Nuratu take ciki bai hanata cewa "Bana son mata a kaini asibiti" abunda ke mind din Nuratu kuwa da yasa tace bata son Fauza ta karɓi haihuwanta Shine ,batason kishiya ta gane mata jiki watarana in komai ya fasu ta rainata.
Daure bakaken maganganun da suke yaɓa mata tayi a tunanin ta duk damuwane Jos daya dayake iya copping damuwarsa
Minti 15 ta kaisu asibitin da take aiki ,ai Nuratu ta kasa fiddo ƙafarta waje ,ji takeyi kamar komai na cikin ta will expell out quickly
Don haka ta dogare a zaune ,da sauri aka gungura delivery bed a gaban motar Nurses' da Fauzan suka kamata suka daurata aka gungurata Labour room
Ahmed ya gama ruɗewa gaba dayansa ,don haka ,ya fara kaiwa da komowa ya kasa tsayawa a gaban motarsa sai sambatu yakeyi yina ma Nuratu Addu'a
A Labour room kuwa ana shiga da nuratu ko sauya mata kaya basu kai ga yi ba suka ga kan baby na ƙoƙarin crowning ,da sauri sukai assisting dinta nan da nan sai ga baby boy ƙatoton gaske .
A kan cikinta suka daura mata yaron da sauri ta dafe ɗan tana masa addu'a tana hawaye ,tana matukar tausain yaron batasan irin rayuwar da zaiyi ba a gaba ,cikin gidan babansa amma za'a kirasa da ɗan shege adopted child da suka karɓa don su taimakesa ,saboda rashin gata zata mika gudan jininta wa kishiya ta raina ,anya zata iya kuwa? Bayan duk wuyar nan da tasha Anya bazata gudu da yaronya ba.?
Kafin asuba sun shiryasu ita da baby ,murna kuwa a wajen Fauza da Ahmed kamar an masu bushara da Aljanna .
Saida ta kwana washekari aka dawo da ita gida
Tana shigowa taga an sauya dakin an maidashi na mother_Baby room ,an kashe kudi kamar ba'a san zafin su ba .
Daga nan suka cigaba da kula da mai jego da yaronta
Ahmed dukda haihuwar sirri ne bai hana shi kiran abokansa da kauyen su Nuratu ba ta shaida masu haihuwarta ba ,don haka kowa yina zumudin zuwa Barka ,um_jafar ma ta shirya zata taho yin ma Nuratu zaman wanka,a cewar ta daga Fauzan har Ahmed basu san yanda akeyi ba so baza a barta ita kadai ta lalace ba .
Ahmed duk yanda yaso ya dakatar da um_Ahmed abun yaki yuwuwa dole ya ƙyaleta ta taho ɗin ,amma ko da wasa bai faɗa ma Fauza ba .
Fauza kam sai rawar kai takeyi an haifar mata baby boy a rana tayi masa hoto sama da goma ,yina cewa ehem zata fara damun Nuratu da tambayar me ya sameshi ko zata bashi nono ne? In kuwa Nuratu na barci baby na wajen Fauza har ta tashi ,Annual lv ɗin ta ta ɗauka zatayi wata guda tana kula dasu .
Wannan kenan
Yau Nuratu kwananta huɗu da aihuwa ,don haka Ahmed kullum cikin hidima da siyayya yake yauma tun safe yaje mall yayo siyayya sosai saboda Um_jafar tace masa tana hanya gobe ko jibi . Bayan ya biya kudin siyayyar sa Yina shirin fitowa aka kirasa a waya don haka hankalinsa baya gabansa yina laluben waya bai ankara ba saidai yaji ya ci karo da mutum gararaf haka
Da sauri ya waigo don ya ba wanda ya buge haƙuri ,Dafe kan nononta guda tayi ta saki nishi"Auchhhh" ta kama Nonon ƙam tana nufin ya buge mata nono .
"Oh sorry plz"
Wani yarrr taji tsikar jikinta ya tashi a ranta tace ashe akwai sauran Black Americans masu kyau haka
Turo baki tayi "Gaskiya Ni bazan haƙora ba " mamaki abun ya basa tunda yake a duniya bai taba jin wanda za'a ba haƙuri yaƙi haƙora ba sai yau
Shiru yayi ya rasa ma mai zaice "Kayi mun shiru ?"
"You're African haka ne?" Jinjina masa kai tayi "Ya akayi ka gane?"
"Saboda Ni ma ɗan can ne ,so zan roƙeki kiyi hakuri don kasancewanmu ƴan continent ɗaya"
Kafesa da ido tayi sai kuma ta washe baki "Kana da kyau ka sani kuwa? ...gaka da murya mai laushi ,ina maka fatan ka kasance ma'abocin lallaausan zuciya kamar kalmomin bakinka"
Daure fuska yayi don baya son rainin wayo "Kin haƙora ko A'ah"
Sa dogon manunin yatsanta tayi a baki tana siɗewa tana jan baki kamar ta samu lollipop
"Kana son in yafe maka?" Banza yayi mata yina kallon agogo
"Hey man ,idan kanason in yafe maka daga kanka nan..." Ta nuna masa wani dogon ginin hotel dake dama da inda suke "Ina cikin nan ka sameni a room 51" caɓe baki yayi
"Nima idan kina ganin bazaki iya yafewa ba ki sameni a mota in biyaki la'adar tureki da nayi amma bani da lokacin binki" yana fadin hakan ya kaɗa kai ya nufi motarsa ,a tunanin sa ya mata hands down
Ya kewaya ya buɗe mota kenan kamar ance ɗago ya ganta ta ɗayan ɓarin ƙofar gaban motar tana jiran ya buɗe ta shiga
"Wai lafiya?"
"Nazo in amsa haƙƙina as u promied to me"
Tsaki yaja mai ciwo ya buɗe motar aikuwa yina shiga ta buɗe itama ta fada front seat ta zauna
Take jikinsa ya fara rawa kawai ma sai yaji ta fara basa tsoro
Buɗe Aljihun dake jikin dashboard din motarsa yayi ya fiddo minti ɗaya na dollas ya miƙa mata "karɓi ɗan fita mun a mota"
Kafesa da ido tayi tana lashe baki lokaci bayan lokaci "Sister zaki fita ko sai na gama ki da securities"
Cikin wani irin sexy mirya ta soma masa magana gamida warce kudin a hannunsa "Zan fita amma ka sani zuciyar Na'ima ta gama macewa a soyayyar ka ,keep at d back of your mind Ina nan shigowa gidan ka don sai yau naga mijin aure" tana gama magana ta kumshe kafaffun Idanuwarta ta buɗe motar ta fice gamida bugo masa kofar bam!
Shima baya yayi da jikinsa bayansa ya daki da bayan kujeran bam ! Yayi maza ya cusa hannunsa a gashin kansa ya fara sosawa .
Ya kwashe yafi minti ashirin kafin ya iya tada motar ya bar wajen don ya rasa ma wani irin tunani zaiyi ,abu daya ne ya tsaya masa a rai sunanta .
Bamalli's care
09065990265
No comments