Recent Updates

Furar Danko 21

 


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣1️⃣




........Wayar da yake faman daƙila ya ajiye, dan dama yana dannawar ne kawai badan yana fahimtar komai ba da yake yi. Ta cikin mirror yake kallonta, sai kuma kamar wanda aka tsikara ya janye yana jan tsuki. Da sauri ya furzar da iska zuciyarsa tana masa kai-kawon tunanin ina ya dace ya dosa da ita. Gidansu ko gidan Uncle Yousuf?. A gidansu tana da ƙanne, kuma basu san halin da take ciki ba bayan iyayensu, ganinta a haka garesu zai ƙarasa zubar mata da mutunci ne a idonsu har ma da ma'aikatan gidan nasu da take takawa kamar ƙasa a duk sanda taso. Gidan Uncle Yousuf kam yaransa basu da wayo sosai kasancewarsu ƙanana, zai ma iya yiwuwa yanzu sunyi barci, ajiyar zuciya ya ɗan sake ja da kallonta ta mirrorn sai kuma ya janye idanunsa a lokaci ɗaya. Har ya ɗauki waya da nufin kiran Uncle Yousuf ɗin sai ya fasa, key yayma motar kawai ya cigaba da tafiya. Kaɗan-kaɗan sai ya dubeta ta mirror har suka iso gidan. Horn yay maigadi ya buɗe ƙofa ya fito, dan ba'ace masa wani zaizo gidan ba a irin wannan lokacin dan ƙarfe sha ɗaya saura. Ƙarasowa yay jikin motar sosai, Smart dake kallonsa shima yay ɗan murmushi da faɗin “Baba Barka da dare yaya aikin?”. 

      Murmushi shima maigadi yayi, dan ya ganesa. Cike da kulawa ya ce, “Mazan fama kaine yanzu da dare haka?”.

     “Eh baba na kawo wannan ne”. Yay maganar yana nuna baya, ɗan leƙawa baba maigadin yayi, ganin Lulu kwance a bayan ya sashi ɗan yin baya yana dafe baki dan shi a zatonsa ko barcin isa ne take yi. Da sauri ya koma ciki ya buɗe gate ɗin. Har gaban ƙofar shiga falon gidan Smart yay parking. Sai da ya kashe motar ya fito sannan ya ɗaga waya ya kira Uncle Yousuf. Ba'a jima ba aka ɗauka. Shi ya fara gaidashi dan a girme dai ya girmesa. Uncle Yousuf ya amsa da ƴar fargaba, sai yay saurin tambayarsa badai wani abu ya sake haɗasa da Mawaddat ba?.

         “A'a Alhaji komai bai faru ba. Itace dai na kawo nan ɗin gamu a ƙofar falo”.

     Da mamaki Uncle Yousuf ya miƙe zumbur, Jallabiyarsa ya ɗauka ya zura dan har sun kwanta ma. Ko amsa tambayar lafiya da Aunty Saliha ke masa baiyi ba ya fice cikin sassarfa yana faɗin, “Ina zuwa”. Shi da kansa ya buɗe motar ya leƙa, ƙirjinsa yay matuƙar bugawa, ɗagowa yay yana kallon Smart kallo na neman ƙarin bayani. Fahimtar hakan shi kuma ya sashi furzar da iska kaɗan. “Bayan tafiyata ta fita, jin hirarsu da ƙawarta a ɗazun ya sani sake dawowa, sai na samu zata fita shine na bita”.

        “Ya Arrahaman harma ta sha kenan?”. Uncle Yousuf ya faɗa cikin matsanancin damuwa.

     Tausayi sosai ya bama Smart, ya ɗan cije lips da faɗin, tana buƙatar saka ido sosai dan koba wannan halayyar bai dace ace mace kamarta tana fitar dare ba haka Alhaji”.

          “Gaskiya ka faɗa Aliyu, na kuma gode sosai da ƙoƙarinka, duk laifin na yaya ne da bazai iya tsawata mata ba a duk sanda yaga zatai fitar, amma inasha ALLAH zan ɗauki mataki ni da kaina. Sai dai abin damuwar nima ɗin wani lokacin bana nan tunda ina tafiye-tafiye, da zaka min alfarmar dawowa kusa da mu da naso haka Aliyu, wlhy na yarda da kai, ina jinka tamkar ɗan uwana na jini, zan iya bar maka amanar Mawaddat batare da jin ko ɗar ba a zuciyata....”

        “Nagode sosai da wannan karamci Alhaji. Sai dai maganar dawowa nan kam abun ne mai wahala gareni, dan Abba ma bazai yarda ba balle kuma Ammah. Sannan nima inada ƙanne, kuma suna buƙatar saka ido duk da dai ba wayona ke tsaremin su ba ko jajircewa. ALLAH ne gafurin rahimun”.

      Duk da Uncle Yousuf ya gamsu da bayanin nasa amma bai so hakan ba. Dan yana matuƙar buƙatarsa tare da su. Yaron nada wata nagarta mai matuƙar ƙayatarwa. Ga nutsuwa da cikar kamala tamkar ba talaka ba. Godiya yay masa tare da fiddo Lulu da ke sharɓan tana ɗan surutanta jefi-jefi a cikin barcin, wanda ba komai bane sai zagin Hon. Baita. Shi dai sallama yay masa zai wuce. Dakatar da shi yay da faɗin, “Kaga dare yayi yanzun. Kaje da motar gida dan abin hawa zai iya maka wahala”.

     Kamar zai ce a'a sai kuma ya tuna maganar Uncle Yousuf ɗin gaskiya ce. Dan haka ya gyaɗa kansa tare da godiya. Saida ya ga ya shige ciki sannan shima ya shiga motar ya tayar ya bar gidan. Mubarak kawai ya samu a waje alamar dai shi ake jira, cikin washe baki Mubarak ɗin ya taso yana masa sannu da zuwa da shafa motar har ya kasheta ya fito yana lucking. “Yaya ka sayi mota ne?”. Mubarak ɗin ya faɗa cikin zumuɗi. Karan farko yayma yaron ɗan murmushi. Cikin deep voice ɗin nan tashi da ta gaurayu da gajiyar son yin barci ya ce, “Daga ganin sarkin fawa sai miya tai zaƙi Mubarak? Ta mutane ce”. Kamar an zarema Mubarak lakar jiki ya ɗan rausayar masa da kai gefe kawai. Daga haka suka shige ciki gidan shiru alamar duk anyi barci, sai wasu a  ƴammatan dake waya da samarinsu, idan ka cire Asma'u da Maryam dako wayar Yayansu yama hanasu riƙewa sai ta Ammah suke ɗan ɗauka. Ɗaki kawai ya shige dan kwanciya yake matuƙar buƙata.......


         ★★★ ∆∆ ★★★


      Da asuba Uncle Yousuf da kansa ya shiga ɗakin aunty Saliha da ya kai Lulu dan ita a ɗakinsa ta kwana ya tadata yin salla. Sam bata da nauyin barci, damma yau akwai na maye tare da ita, da alama kuma ya bugar da ita da yawa, dan ma tana da jini mai ƙarfi, da ace tana da saurin buguwa ma abubuwan da MM Atik Kumo ya harmutsa mata zata iya ƙara shanye yinin yau bata san inda kanta yake ba. Amma sai gashi Alhamdullah ita da sauƙi ya saketa. Zata fara masa gardama ya daka mata tsawa. A firgice ta tashi zaune zumbur jin Muryar Uncle Yousuf tana mazurai. Sosai take zazzaro idanun mamaki, shiko ya watsa mata harara da faɗin, “Karna dawo Massalaci na tadda baki tashi kinyi salla ba, zan matuƙar ɓata miki rai”. Kai kawai ta gyaɗa masa mamaki fal ranta akan ganinta nan ɗin. Sai kuma abinda ya faru a daren jiya ya shiga dawo mata ɗaya bayan ɗaya. Cikin wani irin takaici da jin ƙuna a rai ta dafe kanta tana jan tsaki. A fili ta furta, “Sai nayi maganinka wlhy, illiterate kawai ko wa yace ya kawoni nan? To wai ubanwa ma ya nuna masa can ɗin da har ya bini?” Anya mutumin nan baida iskoki bisa kai ko? To inba mai iskoki ba itako mizata kirashi? A jiya dai tasan ya tashi a aiki ai da wuri ma. Amma kuma sai gashi ta gansa a inda babu wani mahaluki da yasan zataje. Kai wannan lamari da mamaki, dole ne tasan yanda ma akai ya bita can, kuma sai ta koya masa hankali akan shiga abinda bai shafesa ba. Nadiya ma sai ta shuka mata rashin mutuncin da bazata taɓa mantawa da shi ba da ga ita har su Hon. Baita ɗin. Jin ana neman idar da salla ya sata sauka a gadon dan tasan Uncle Yousuf babu wasa ne, ba ruwansa rufe ido zaiyi yaci mata uwa babu ruwansa da shirin da sukeyi. Wanka ta farayi sannan ta ɗauro towel Dan tana so ta sake wattsakewa. Batako zaman jiran tsanewar jikinta ba ta zura abayar Aunty Saliha. Sallar tai babu wani nutsuwar a cikinta, tana zaune a inda ta idar tana kulla mai fishseta Uncle Yousuf ya leƙo, gaidashi tayi, sama-sama ya amsa mata duk da yaga yanda ta koma kalar tausayi. Ba yanzu ya shirya mata magana ba dan haka yay ficewarsa. Ji Lulu tai gaba ɗaya hankalinta ya gama tashi, sam bata ƙaunar fushin Uncle You a rayuwarta, har gara ma Daddy yay fushi da ita dan shi tasan abu ɗaya zata masa ya rikice ya dawo lallaɓata. Kuka take so tayi, sai dai ita mai juriya ce da shegen taurin kai, ba a komai take iya kuka ba komai ƙololuwar ɓacin rai ko tashin hankali da zata tsinta kanta a ciki. A karan farko taji kunyar haɗuwa da mutanen gidan, tashi tai jikinta duk babu ƙarfi, bata ko nemi jakarta da takalminta ba ta fice cikin sanɗa, taji daɗin rashin samun kowa kuwa, da sauri tabi ta ƙofar kitchen ta baya. Tunda ta fito bayin fulawoyi ke mata kallon mamaki da ga nesa, dan shi dai bai san sanda tazo gidan ba kam, ƴar tsawar da tai masa ta sakashi dawowa a hayyacinsa. “Wawa mi kake kallo ne? Dilla buɗe min ƙofa!!”. Jikinsa har kakkarwa yake duk da kuwa a girme ma zai iya girmarta shima, kuma ba aikinsa bane, ta watsa masa harara lokacin da take ficewa tare da jan tsaki. Yasan laifinsa dan haka ma baiji haushi ba. Mawaddat ta tsani taga ana kallonta, gashi kuma yau shi ta kamasa dumu-dumu. Ya san dai bala'i bai ƙare ba, dan duk randa ta dawo gidan zai sha masifa. Ƙila ma harda zagin ƙare dangi za'a haɗa masa.


        Da ƙafa ta isa gida, kasancewar garin da sauran duhu ga ɗan sanyi-sanyin da aka fara na lokacinsa. Acan ma sai da maigadinsu ya samu rabonsa na zagi. Dan shima dai galala yay yana mata kallon mamaki. Amma tunda ta fara danna masa na maguzawa sai ya nutsu ya koma gaisheta a daburce. Bata amsa ba tai shigewarta tana jan tsaki..........✍️




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments