Furar Danko 61
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣1️⃣
........Ƙarfe kusan tara Lulu ta tashi da ƙyar a dalilin kaɗawar alerm ɗin ƙaramin agogon da ke a side drawer ɗinta da ya gallabeta tun takwas. Amma nauyin da jikinta yay mata
yasata kasa kasheshi ko ta tashi har zuwa yanzu da ya sake buga taran. Ƙaramin tsaki taja da ɗan kai hannu tana lalube, sai dai sam babu ma alamarsa kusa da itan. Tamkar wadda aka ƙwalama kira sai kuma ta miƙe zumbur, yau fa ya kamata ta shigar da case ɗin mijin matar can court, dama tai alƙawarin sai ya kwana bakwai a police station su Shu'aibu sunci mata ubansa gwargwadon iko sannan, yau kuma kwana bakwan cif. Wayoyinta ta shiga nema, sai kuma ta tuna sunafa hannun Uncle You nan kuma gidan da aka kawota jiya ne. Ƙaramin tsoki taja da dafe kanta da yay mata matuƙar nauyi, dole ta sakko a gadon cikin ɗan tangaɗi kaɗan sai dai bana mayen bane na nauyin jikine dan abinda tasha ɗin sun saketa sai abinda ba'a rasa ba. Bayi ta shiga ta tsaya ƙarƙashin shower batare data cire komai ba daga jikinta ruwa ya fara sauka mata a haka. Ajiyar zuciya ta dinga saki a jajjere, sai da ruwan yay mata sharkaf ta gamsu ta ƙara komawa garau da take buƙata sannan ta fara zame kayan jikin nata ta fara wanka. Tana kammalawa ta jefa kayan a injin wanki dan komai na ƴar gata an ajiye mata shi, sai da ta gamsu sun wankun sannan ta ciresu ta maida indai zai busar. Sai ga kaya ras ta fitar sannan ta fito. Tana buƙatar waya domin kiran Zainab sakatariyarta da kuma su Shu'aibu ɗan sanda, dan haka ta fito da ga bedroom ɗin nata daga ita sai rigar wanka da towel ɗin data naɗe gashinta da take son ruwan data jiƙashi da shi ya naɗe. Sautin muryarsa yana raira karatun Alkur'ani cikin suratul An'aam daya karaɗe corridor ɗin ya sata gane yana a ɗakin dake kusa da wanda take. Sai da ta sake gyara yanayinta dan karma ya kawo mata wani raini sannan ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shiga kanta tsaye ba batun neman izini, sallama ma sai da ta gama shiga tayita ciki-ciki. Ƙamshin shower gal dana haɗin turarrukan wankan da masu gyara mata jiki suka shirya mata na musamman ne ya fargar da shi shigowar ta, dan cikin abinda baifi sakans ba ɗakin ya gauraye da masifaffen ƙamshinta. Kasancewar yazo inda ya kamata ya tsaya ya sashi rufe Alkur'ani ya ɗago ya kalleta. Kanta ta ɗauke daga kallon da take masa, shima sai ya janye nasa idanun yana ajiye Alkur'anin. Cikin izzar nan tata da gadara ta ce, “Ɗan bani aron phone ɗinka na kira Uncle You ya bada nawa a kawo min”.“Kinyi salla?”.
No comments