Recent Updates

Nailah 12

 


*🌸NAILAH🌸*


   ~*(The abandoned flower🌹)*~




*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAY*



*PAGE 11(END)*



Sun daɗe a haka bata ɗago ba, sai shine da yaga wayarta tana ringing bata duba ba sai ma ƙara lafewa da tayi a jikinsa, ya ɗago ta tare da manna mata light kiss a bakinta ya miƙa mata wayar.



Bata san lambar ba dan haka tana ɗagawa tayi shiru sai da aka fara magana ta can ɓangaren ta gane Abba ne da jikinsa yayi sauƙi ras sai ɗan abinda ba'a rasa ba, sai ta maida dukkan hankalinta tana sauraro har ya gama faɗin abinda zai faɗa suka yi sallama ta ajiye wayar jiki a sanyaye da alamar tsoro tsoro a fuskarta tace "wai nema na ake a masarauta.



Ajiyar zuciya Eeyad ya sauke dan ya san zancen dama, ya ƙara janyo ta jikinsa sosai yana shafa bayanta yace karki ji tsoro, mahaifinku ne ya samu asalin danginsa.



Da sauri ta ɗago da mamaki ƙarara a fuskar ta, kenan dama sunada dangin uba bayan kakaninsu da suka rasu? dukda itama kanta bayan ta mallaki hankali tana yawan tunanin hakan a ranta, taya ne za'a ce mutum daga uwa sai uba kaɗai garesa sai kace su iyayen daga sama suka faɗo.




Gani yayi tana shirin ruÉ—ewa dan haka yace ta nutsu ta shirya kafin shima ya shiryo su je ya kaita da kanshi.



Babu ɓata lokaci ta shiryo cikin tsadajjen leshin ta wanda ya matuƙar amsar jikinta ya zauna daram ta ɗora mayafinta mai ɗan girma ta zauna tana jiranshi, bata ɗau lokaci ba ya shigo shima cikin dakakkiyar shadda sky blue, kasa ɗauke idanunta tayi a kansa har saida yazo ya hura mata iskar bakinsa sannan ta zabura sai kuma ta saki murmushi tana rufe fuska da tafin hannunta.



Suna isa ya ajiyeta sannan ya juya dan ba zai shiga ba ma saboda family issue ne, abinda ta tarar ya saka numfashinta kusan É—aukewa, nan ta fara jin tun daga haÉ—uwar Asma da wannan saurayi da sumewar da yayi bayan yaga Abba.



*Baya kaÉ—an*

Bayan sumewar shi cike da tashin hankali Abba yace Asma ta kira likitoci, suka zo suka bashi agajin gaggawa, Bilal kam yana farfaɗowa bai tsaya ko ina ba sai ƙayatacciyar masarautar Azhar direct zuwa gurin mai martaba, abinda Bilal ɗin yazo masa dashi ya saka mai martaba ƙure ɗanɗan ƙanwar tasa da kallo kamar yana hango wanda aka ambata a cikin fuskar Bilal ɗin, sam baya wasa da duk abinda ya danganci maganar ɗan uwansa rabin jikinsa kuma ɗan biyunsa, dan haka babu ɓata lokaci da kanshi ya saka Bilal ɗin yayi driving ɗinsu suka yi fitar sirri ba tare da sanin kowa ba.



Koda suka isa asibitin kai tsaye ya buƙaci a kawo masa file ɗin Abba wanda illahirin ma'aikatan Asibitin jikinsu ke rawa ganin me martaba da kanshi, babu ɓata lokaci aka kawo masa.



Ganin sunan Abba da na mahaifinsa ya saka mai martaba kusan yanke jiki Bilal yayi saurin ƙarasawa ya tare shi, bai damu ba ya nufi ɗakin da Abba yake wanda shima Abban ganin me martaba ya saka yi saurin miƙewa a tsorace haka ma Asma, shi Abba yana ganin fuskar mahaifinsa wanda ya rasu, ita kuma Asma fuskar kakanta take gani.



Mai martaba bai jira komai ba ya Æ™arasa ya rungume Abba da Æ™arfi hawaye suna É—an gangarowa daga idanun dattijon, a hankali ya É—ago yace Uban masu gida kaine? (da yake sunan mahaifinsu aka saka mashi) 


Sai kuma ya cigaba da faÉ—in "ina Husaini? Ina mahaifinka da mahaifiyarka?



Sai a yanzu Abba ya fara fahimtar abunda ke faruwa, kenan wannan É—in É—an uwan mahaifinsa ne.



Me martaba ganin abin ba zai yiyu a asibiti ba saida ya tabbatar da Abban ya samu lpy dama ana shirin sallamarsa ne, take yace a basu sallamar yanzu, kai tsaye kuma ya wuce dasu masarauta daga shi har Asma da kanta ke kulle har yanzu.




Tashin hankali da ba'a saka masa rana shi ya faru a masarauta da jin rasuwar Hussaini da matarsa, sai ɗanshi ne aka samu bayan shafe shekaru ana nemansa babu dare babu rana har aka gaji aka haƙura aka zubawa sararutar Allah ido, hatta ita wadda tayi ma Husainin da matarshi asiri suka bar gida da komai nasu tuni itama ta rasu bayan an gano makircinta an kore ta daga masarautar.



Anyi kuka, anyi jimami sannan aka kira masrautar garin Basrah aka sanar dasu halin da ake ciki sai dai yar tasu itama ta rasu sai É—anta ne aka gani.



Babu ɓata lokaci suma suka bayyana a nan, tuni soyayyar waɗanda aka rasa ta koma kan Abba da iyalinsa da suma tun tuni aka ɗauko su daga gida, Nailah da fatiya ne kawai basa gurin.



Abih kam sosai abin ya É—aure masa kai ya saka shi mamaki dan babu wanda bai san rikicin da ya faru a baya ba wanda har yayi sanadin bugawar zuciyar mahaifinsu kuma sarki a wancan lokacin, sai dai lamarin Allah ya wuce gaban tunanin mutum.



Ummi kam ita tama rasa a wane yanayi take ciki, ita dai ta san dole mijinta yanada wasu dangin a can wani gurin bayan iyayensa, tabbas iyayensa ma duka farare ne sosai shima haka, amma sai taga kawai tana haihuwar ya'ya baƙaƙe bayan ita duk danginta babu baƙi, kenan su Nailah a nan suka ɗakko kalar fatarsu? dan ta ga ko ƙanwar su mai martaba ɗin itama baƙa ce haka wasu cikin yan gidan ma.


*Present*

Nailah kam jin duk waɗannan abubuwan itama kasa tsaida hawayenta tayi, tayi kuka sosai wanda tuni aka rufu ana lallashinta cikin so da ƙauna ta duka ɓangarorin guda biyu.




Guri ɗaya aka samu matsala da aka buƙaci Abba ya zauna a masarautar ya dire yace ba zai iya zama ba, dan Ummi ma da suka keɓe ce mashi tayi ko shi ya zauna wlh ita ba zata zauna da yaranta a cikin wata masarauta ba.



Da yake lallaɓasu ake sai mai martaba ya amince amma a ranshi ya ayyana zasu ƙara zantawa a kan hakan koda gaba ne InshaAllah.



Gida ne da za'a kira shi aljannar duniya aka basu nan kusa da masarautar sannan aka zuba masu aiki da komai, da farko bai koma ba dan kar Abih yaga kamar bai gode da gidan da ya basu suka zauna ba dukda dama cewa yayi kafin ya samu lpy suga yadda za'a yi, baice ya bashi duka kai tsaye ba, Abih ya nuna masa ai hakan ba komai bane, sun ma fi sonshi kusa da masarautar shiyasa suka bashi gida a can, dan haka ya koma can É—in kawai.




A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya, ɓangaren su Nailah kam soyayya suke zubawa mai tsafta ita da Sir ɗinta da yanzu ya koma "hero", sosai ta goge ta zama DON a harkar da Eeyad yafi bukata dan kuwa haka zai ɗauki lokaci yana farauta, ya gama kuma ayi masa sannu, harda godiya, wani lokaci ana masa kallon ƙasa ƙasa a tambaye shi koda buƙatar ƙari ne? Aikam tuni mazan ke amsawa su nuna eh lallai da buƙatar ƙari.




Idan tana jin iya shege kam round ɗaya zai yi ta fara ihun a ƙyale ta haka, itafa ba abinci bace da za'a dinga ci ana ƙarawa, duk yadda yaso kuwa dole haka yake barinta dan idan tayi wannan tutsun ba zata taɓa bari ya samu abin yadda ya kamata ba, kuma ma baya buƙatar takura ta ko kaɗan.



A zamantakewarsu da Husnah da farko ba'a ga maciji suke dan babu mai shiga harkar wata, saida ya fahimci hakan ne ya ɗauki salon da zai haɗa kan iyalinsa dan ba irin wannan rayuwar yake so suyi ba gaskiya, ko wacce ranar girkinta a ɓangaren ta ake zama ayi fira da cin abinci har zuwa dare sannan kowa ya kama gabansa, wannan salon da ya zo dashi tuni suka saki jiki da junansu dan babu wacce keda matsala sosai a cikinsu, yanxu ko baya nan wannan zaman sai an yi shi, ba wai ba'a kishi ba, akwai kishi tabbas amma sai aka iya sarrafa shi ake yin me aji irin wanda Addini ya yarda dashi, sai suke rayuwa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.



Cikin Husnah nada wata huÉ—u Nailah ta fara laulayi mai É—an zafi wanda har saida ta kusa wata É—aya a kwance kafin jikinta ya daidaita.



A hankali ta cigaba da rainon cikin wanda a fitowarshi yayi wani irin girma dan yanxu watanshi bakwai kuma a wannan lokacin ne Husnah ta haifi É—anta namiji kyakkyawa MashaAllah, yaci sunan Muhammad, zo kaga murna dan ma ita Nailah yanxu komai tana yinsa ne amma bata jin daÉ—i sam saboda cikin duk ya takura ta.




A haka itama lokaci ya gangara saida ta cika wata tara cif sannan ta haifi yaranta yan biyu mace da namiji, macen ta ɗauko kamannin uwarta sai dai fatarta sam ba ta Nailah bace, dan kuwa farin da Nailah bata samu bane aka ninka ma yarinyar da farinta ya zarce na namijin wanda ya ɗauko Eeyad sak babu abinda ya baro nashi, macen taci sunan Ummi (Aminatu) ana kiranta Meenal, namijin kuma sunan Abih yaci (Abdulkarim) ana kiranshi Abdul kawai, farin ciki mara misaltuwa daga wannan ahali, Mommy da burinta yake cika tuni ta rasa inda zata saka ranta dan murna tana fatan bata ƙi duk shekara a sako mata jika ba, sai dai abinda bata sani ba Nailah tana haihuwar yaran tasa aka banka mata planning dan ita karatunta ma kawai take ji yanxu da suke shekara ta kusan ukku.




Watan yaran biyar aka yi bikin Khairat itama aka miƙata gidan mijinta dake ɗan nesa kaɗan, ɓangaren su Asma da Mariama ma tuni aka maida su makaranta bayan kawo masu malamin da ya koyar dasu na tsawon lokaci a gida suka san abubuwa da yawa, da yake suma sun fahimci ilimi ne kaɗai zai yaye masu duhun kai dan haka suka maida hankalinsu gaba ɗaya kan karatun na boko da na Addini har suka samu nasarar zana jarabawar fita a secondary cikin Sa'a suka samu cerfticate sannan aka sama masu gurbin karatu a jami'a.




*4yrs later*


Da gudunta na yara Meenal dake sanye cikin pink barbie dress, yanayin farin yarinyar da dogon gashin kanta baƙi ƙirin na gado ba zaka taɓa tunanin ta haɗa iri da baƙaƙen fata ba, ta ƙarasa inda Arif yake sanye da uniform ta riƙe shi gam tana faɗin "sai na bika yaya Arif, nidai kaje dani"



Da sauri Abdul da sai yanxu ya kula da Arifa ɗin shima ya taso suka riƙe shi gam suka hana shi motsi dan haka yayi tsaye yana dariya yana faɗin to ku sake ni mana sai mu tafi, babu musu suka sake shi murna fal ransu jin zai tafi dasu, saidai suna sakin shi ya falla a guje yana daga masu hannu yace "bye"


Wani uban kuka suka fasa da ya saka nanny ɗinsu saurin fitowa tana kama su ta fara lallashi sai dai kamar ƙara masu volume take yi.



A hankali Nailah da kukansu ya farkar da ita ta buɗe ido ta kalli time ƙarfe takwas ne kwata kwata dan haka ta dafe kai dan bata so tashi yanzu ba, ta sani kuma ba sake komawa baccin zata yi ba sai ta mike ta shiga toilet tayo wanka ta fito ta shirya cikin material mara nauyi babu komai a fuskarta sai kwalli ta sauka ƙasa.




Suna ganinta suka yi kanta da dugu suna cigaba da kukan da tuni ta san ko na miye dan haka ta kalli nanny É—in tasu tace "Asiya ba nace ki daina barinsu fitowa a daidai lokacin da kika san Arif zai tafi makaranta ba"



Da sauri ta girgiza kai tace "wlh Aunty na je kitchen ne na damo masu madara, kuma a É—akin na barsu ban san sun fito ba" tayi maganar jikinta na rawa dan kukansu ne ma ya saka ta fitowa ba shiri ko madarar bata gama damawa ba. 




Nailah bata ƙara ce mata komai ba ta kira driver sannan ta kalli Asiya tace ta jasu su wuce gidan Ummi kawai, dan ita ba zata iya da wannan jarabar ba gaskiya, daidai sun fita Eeyad ya shigo yana wurga idanun inda zai hango su ta ƙaraso ta zauna kusa dashi tana faɗin bafa su gidan nan, suna can na turasu gidan Ummi in huta.



Numfashi Eeyad ya sauke a hankali ya janyo ta dab dashi yana faɗin "miye damuwarki wai, kullum yara da sun fara kuka daga ki tura su gidan Mommy sai ki tura su gidan Ummi bayan kinsan ko ina suka je riƙe su ake ba'a maido min kayana da wuri, kuma kinsan lpy lau nike zuwa in ɗauko abu na a gidan Mommy amma ba zan iya zuwa gidan Ummi nace a bani yara ba ko, nikam idan basu dawo da wuri ba gaskiya a daren nan zamu je asibiti a cire abin nan mu dawo na ƙara baki wasu twins ɗin InshaAllah.



Sai kuma ya danyi shiru yana kallon yadda ta turo baki yace "nama fasa, yanxu zaki tashi muje a cire shi ai dama dan karatu kika saka kuma kin gama, tashi maza muje kuma daga yanxu ba zaki ƙara sakawa ba da yardar Allah.



Gani yayi ta saki murmushi, ta kamo hannuwanshi cikin nata ta kai bakinta daidai kunnenshi ta raÉ—a masa wani abu, da sauri ya zaro ido yana faÉ—in kenan dama kin cire ban sani ba.



Ido ɗaya ta kashe mashi tare da ɗan duƙo da kanshi ta zira bakinta cikin nashi tana bashi wani irin kiss na fitar hankali.



Sun jima a haka kafin ta sake shi ta miƙe a hankali dan tuna fitar da zasuyi tare da su Asma da bikunsu ya matso daf suke ta shirye shirye.




*Alhamdulillah*



*A nan na kawo ƙarshen littafin Nailah, ina roƙon Allah ya yafe man kurakuren da nayi a cikinsa*



*Ina godiya gare ku fans*

No comments