Recent Updates

Mijin Malama 19


MIJIN MALAMA

Paid book ne

Book 1 and 2 (1k)

08119237616

Nimcyluv19

Lokacin data koma gida ta same su duk suna breakfast Mami ta ce "Majeederh danƙi baya cin ƙosai shi ya sa ban kira shi ba" Majeederh ta san babu abin da Little baya ci kawai dai bata taɓa gwada bashi ƙosai bane balle ta ce. A hankali ta jinjina kanta kawai alamar "Eh" kana ta nufi cikin bedroom ɗinta. Ta samu Little a tsakiyar gado ya yi ɗai-ɗai tare da langwaɓe kai kamar mara lafiya ta yi murmushi tana ɗauke kai ya ce "Mami yunwa ina ji" a taushashe cikin sanyin murya ta ce "Na sani, bani 10 minutes"

Ya ɗaga mata ta fita wajan 15 minutes ta dawo hannunta ɗauke da plate ɗin Indomie gefe kuma ta soya masa ƙwai sai ƙamshi suke. Yana ganinta ya miƙe tsaye yana kyakkyawan murmushi tare da tsalle ya ce "Idan na yi kuɗi zan baki kuɗi da yawa"

"Aikin me za ka yi" ya É—aga kai sama alamar tunani kafin ya watsa hannu baya ya ce "Zan samu kuÉ—i, naiwa duk wanda ya saki kuka duka" "Allah ya shirya ka ya yi maka albarka"

Ya yi murmushi da kyawawan haƙoran shi ta shiga bashi Indomie a baki yana zaune akan cinyarta. Bashi abincin kawai take amma a zahiri tunanin yana wani wajan daban ita kanta ba zata iya lissafa inda tunanin nata ya je ba,idan ta tafi wazai kula mata da Little? Wazai jure rigamar shi da ɗakko mata magana da yake? Tana wannan tunanin ta ji yatsun shi biyar a cikin bakinta ya tura mata wainar ƙwan data soya masa, ta zare idanu cike da maɗaukakin mamaki ta kasa magana sbd ya yi mata yawa a baki Little ya dinga tun tsire dry. Ta ɗaga hannu kamar zata dake shi ya yi saurin rungumeta yana cewa "Sorry Mami" hugging nasa back ta yi tana shafa kansa tana gama bashi ta miƙar da shi tsaye akan gadon ta kama hannunsa ta marairaice fuska ta ce "Little" "Mamina"

"Za mu gidan Uncle Isma'il yanzu" nan da nan ya haɗe fuska kamar bai taɓa dry ba zuciyarsa ta motsa ya yi ƙasa da kansa. Ta yi murmushi domin ta san za a rina an saci zanin mahaukaciya.

Ta leƙa fuskarshi ya yi saurin rufe Idanu ta ce "Ba zaka ba?" Ya ɗaga kai da sauri ta ce "To ni zani, ka zauna a gida"

Ya maƙale ka faɗa ya ce "Mami mu zauna a gida" "Dole za mu, ai Uncle Isma'il ɗin baya nan ka ji kuma a bayana zaka goyaka zan" ya yi saurin cewa "Baki da Kuɗi?"

"A'a kawai tafiyar ƙafa akwai daɗi" Ta tallafo fuskarsa ta ce "Don Allah banda faɗa ka zama nice har mu taho yau ɗin zan zan maka siyayya harda motar da ka ce"

"Har bindiga?" Ta kame fuska tana É—auka shi zuwa toilet ta ce "A'a, ko soja zaka zama?" Ya yi mata shiru. Ruwan wanka ta haÉ—a kana ta É—aura masa towel ta cire masa kayan tayi masa wankan tana mamakin baÆ™ar fatarshi kamar Æ™ara mata baki ake amma baÆ™in irin mai kyau É—in nan da É—aukan Idanu.  A wajan saka kaya ma faÉ—a sosai shi baya son manyan kaya dole ta saka masa wata brown É—in t.shirt mai photon tiger a jiki sai wando 3gauter kayan su kayi masa wani irin sahihin kyau tare da amsar fatar shi. Tana gyara masa sumar kai ta ce "Ka tsaya na shirya ko ka fita parlour" ya ce "to"

Tana shiga wanka ta ya fita parlour ya leÆ™a yaga Aaliyyah ta ce "Big boy yau sai ina?" Ya lumshe idanu ya buÉ—e ya ce "Da Jee zamu" Aaliyyah ta ce "To daman ka isa ka fita kai É—aya? Zo na yi maka photo" ta tsayar da shi a gabanta ta shiga yi masa photo suna tsaye Raihana ta fito ta ce "A'a É—an baÆ™i na Anti Jeederh, kaga yaro mai uwar rana" bai kalleta ba daman jininsa bai zo É—aya da ita ba. Little yana da wanne irin hali ga shegen wayon masifa kamar wassafa masa wasu abubuwan ake. Duk wanda suke takura rayuwar Majeederh ya haddace su tar kuma baya kula su. Raihana har ranÆ™washin kansa tayi ta ce "Miskilin banza, daga gani uwarka fama tayi dakai kafin ya É“ata" "Mamin?" Ta ce "Uwarka na ce, ko an faÉ—a maka MAJEEDERH ita ce Uwarka?" Ya yi shiru kawai domin baya fahimta gabaÉ—aya. Suna nan yana yiwa Aaliyyah surutu yana itama zai siya mota bayan ya siyawa Maminsa  Æ™atuwa "Wato dole sai ka nunawa kafi son Maminka, to ai Mamin taka tafi so na" ya maÆ™ale murya ya ce "A'a" Aaliyah ta yi masa gwalo ta ce "Ohho, wooo Mami ta fi so na akan ka" nan da nan ya haÉ—e fuska duk da yaro ne amma ya tsani ace Mami bata son shi. Aaliyyah za ta yi magana ya ji an sakar mata ranÆ™washi akanta. Ta kwaÉ“e fuska ta ce

"Kai Anti Jeederh akan Little zaki dakeni" Little ya yi tsalle sosai ya ce "Mamina" Majeederh dake tsaye sanye cikin shigarta  as usual abaya ce mai kyau da É—aukan hankali ta yi rolling kana ta É—ora liÆ™ab. Cikin wani sabon yanayi data samu kanta ta ce "Ki kiyayeni Aaliyyerh" Aaliyyah ta tura baki ta ce "To Anti Jeederh ai da gaske kin fi so na" Little ya kalli Majeederh yana jiran ya ji me zata ce. Sai bata ce komai ba ta kama hannunsa zuwa bedroom É—in Mami ta sameta zaune ana ta buga waya ana faÉ—awa Æ´an-uwa an kawo kuÉ—in Rumana Dubu É—ari biyu cif. A sanyaye ta ce "Mami na ta fi" Mami ta ce "Zuwa ina?" "Gidan Uncle Isma'il, Yaya Bilkisu na kirana" Mami ta ce 

"To to na ji, yanzu Ruhuma zata wajan Widad maganar ankon biki Imrana ne zai kaita na ji ma ta ce yana hanya ki bari ku ta fi tare, kici arziƙin ƴar-uwarki ko?"

Bata son musu sai kawai ta ce "To" tana fitowa ta ja hannun Little su ka yi waje. A bakin ƙofa taci karo da Latifa cikin shigarta riga da skirt na atamfa ta yafa mayafi ta kalleta sosai sai bata ce komai ba. Latifa ta yi dry ta ce "A'a fa yadda kike takura kanki da zafi cikin duguwar riga da liƙab ni ba zan iya ba, shi imani a zuciya yake" Majeederh ta ce "Wane ya yi maganar imani?" Latifa ta ɗaga kafaɗa ta ce "yanzu zaki fara faɗar na bayyana tsaraici ki shiga kawo fatawa kala-kala, ke dai ka san ko a malamai tsaurin ra'ayi zaki" Ita dai Majeederh bata ce komai ba Latifa ta sake cewa "Sai ina?"

"Gidan Uncle Isma'il" "mu je na rakaki" tafiya suka fara a hankali Latifa ke surutu ita ɗaya domin Majeederh idan ka ji maganarta Little ne ya ce wani abu ko da Aaliyyah da suke Uwa ɗaya Uba ɗaya bata fiya hira da ita ba, sai dai faɗa idan ta yi kuskure akan abu. Tun da ya karyo kan motar shi idanunsa ya sauka akanta, wani irin maganaɗisun abu ya shiga fisgarsa zuwa gare ta. Ya tsorawa yatsun hannunta idanu wanda suke ɗauke da Little dake kafaɗarta a hankali yake lura da juyawar Idanunta tana bubbuga bayan yaron tafiyar a hankali mai cike da ɗaukan hankali wani abu ya ratsa zuciyarsa irin abun nan da ake kira da soyayyar fari, har suka zo daidai motarshi bai kula ba sai da suka gilma kaɗan ya sauke numfashi tare da buɗe motar shi ne ya fito. Kyakkyawan matashin saurayi mai fama da rufin asiri daka gani yanzu yake ji da samartakar shi. Fari ne kyakkyawa mai matsakaicin jiki nutsuwa da ilhama a tare da shi, yana sanye cikin kyakkyawar shigar dake nuna kamalar shi. Amy green ɗin shadda ce a jikinsa ya murza hula saman kansa zai ƙamshin turaren (Thierry mugler). Ƙamshin dake narkar da dukkan wata zuciyar ƴa mace. Ya ƙarawa tafiyarsa sauri harya tarar da su tunda ba wani sauri suke musamman tafiyar Majeederh wacce take kamar an zare mata laka. "Assalamu alaikum" Cak suka tsaya tunda sun san darajar sallama babu cancantar suna tafiya kuma wani na binsu. Ƙamshin Thierry mugler bai firgita Majeederh ba, deep down na zuciyarta addu'a take Rabbil izzati ya sanya wa'adin zamanta a gidan Abbu ne ya zo ƙarshe, addu'ata take Allah ya sa mai rusa zuwanta karatu ne ya bayyana, Al-hakkamu sarki kowa da kowa ya ƙaddarta masa ikonsa a yanzu nan, Allah ya da mai yaye mata damuwar dake sanyata azumi ne ya zo. Ta rufe Idanunta tana jiran ƴar manuniyyarsa ta tsaya akanta. "Wassalam" cewar Latifa tana duban matashin wanda ya amsa komai na kamalar mutum. Ya dinga kallon Majeederh ba zai ce ga kalar kyan fuskarta ba, amma yatsunta sun bayyana wace ita abubuwa da yake ji game da ita sai ya ji sun ninku ainun kamar zubar ruwan sama ya yi da hadari ya ƙara kankame. Cikin wani irin al'amara da gilamar wasu sabbin ƙaddarori masu wahalar fasaltasu ba tare da sanin abin da yake faɗa ba ya juya gabaɗaya kan Latifa ya ce "Amincin Allah ya tabbata ga ma'abociyar kyau da kwarjini, fatan san samu number wayarki ganin akan hanya kuke" a baɗini kalamar direct domin Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Ya zayyana su amma a zahiri tubalin ginin maganarsa da yadda ya zayyana su ya nuna mai fahimta da ganin komai cewa da Latifa Omar yake. Latifa ta yi jim ta ce "Ni, ko ita?" Ya ɗan tafe baki kaɗan ba tare sanin ainahin abin da yake ba ya ce "No, dake nake kyakkyaw" Dam! An koma. Zuciyar Majeederh ta bada sauti ta ƙara rufe Idanunta Allah ya sa zalamarta bata fiyi ba balle ta kunyatar da ita. Majeederh ta ƙara lamuncewa zuwa karatun nan nata na daga cikin ƙaddarorinta masu girma. Latifa ta ce "Amma sauri muke" "Kuyi mini alfarma ba don na isa a yi mini ba, sai dai ta yaku kare mutumci ku shiga na ƙarasar daku" ya faɗa yana haɗe hannu bibbiyu. Latifa ta juya ta kalli Majeederh ta ce

"Malama Majeederh ke ce me matsala Kinga Little har ya yi bacci ki zo mu je"  Bawai fuskarta suke gani ba,amma ta Æ™ara kame kanta bata da wani kuzarin yin magana. Ya juya a hankali da É—an sauri kuma ya buÉ—ewa Majeederh Æ™ofa ta shiga a nutse da addu'a bakinta. Ya buÉ—ewa Latifa Omar gaban motar ta shiga. Tafiya suke a nutse ya gyara zama ya ce "Sunana Barrister Aliyu Sufyan Alhassan" "Nice" Aliyu ya shafa gemu ya ce "A gida more especially Hajia suna ce mini Zaki, am the second born of my parents, ina da babba yaya Almustapha, mahaifina sunan shi Sufyan Alhassan yana nan tare damu, ya su nayi aikin jarida na Æ™i, to ya na iya abincina yana ga Shari'a, sai mahaifiyata we call her Hajiya, I love my mother more than anything dake duniyar nan tamu, na yi karatu mai yawa akan Shari'a now an working with Shari'a court of appeal ban jima da fara aiki ba" Tunda ya fara magana Latifa ta rufe Idanu sosai har cikin zuciyarta Aliyu ya kwanta mata irin mijin da take so daka gani zai yi haÆ™uri sosai. Har suka isa gidan Uncle Isma'il Majeederh ko tari ba tayi ba ta rungume Little kamar zata mayar da shi ciki, lokaci zuwa lokaci Aliyu ya dinga kallon Majeederh ta madubi, duk sanda ya kalleta sai ya sauke numfashi a É“oye. Suna tsayawa ta buÉ—e Æ™ofa ta fita ta shige ciki, da sauri kamar wacce wani abu ya biyota. Innati dake maÆ™ale a bayan labule ta buga tsalle tana faÉ—in "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, wahala haula wala Æ™uuwata, uban waye a wannan wajan?" Majeederh ta shiga tana sauke numfashi Innati ta ce "Amma dai Allah ya isa Kululu, Allah ya isa saura kaÉ—an na saki gudawa É—aukan hakÆ™in nan har ina? Ashe Æ™atuwar jahila muke zaune da ita kinsan alhakin da kika É—auka? To wallahi ba wani yafewa nayi Æ´ar banza da fuska kamar karas" Majeederh ta tura baki tare da kwaÉ“e fuska ta ce "Ki barni" Innati ta riÆ™e haÉ“a ta ce "Na barki ba? Idan na barki a duniyar nan Kululu na kama ubanwa? Wa kike da shi daga duniya har lahira wanda ya shige ni?" Majeederh dai ba tayi magana ba ta É—aga liÆ™ab É—in fuskarta Innati ta zabga sallati ganin yadda fuskar Majeed ta yi jajur kamar jini ya kwanta. Innati ta kwasa a guje zani na faÉ—uwa ta shiga faÉ—in "Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, Isma'ila masifa ta faÉ—o mana uban kowa ya yi ta kansa Aljana mai kama da Kululu a É—akina....



*A yi karatu a nutse, a fahimta a ilmance, a nishaɗantu. Muna nutsawa a labari zaku kasa bacci da sukuni. Soyayya ce mai wahalar gogewa, ƙaddara ce mai wahalar fahimta. Babu batun sadaukarwa faɗa ne akan Soyayya!*


Allah ya nuna mana Monday Lafiya, a yi weekend cikin farin ciki.... 08119237616

No comments