Recent Updates

Mijin Malama 20

 


Nimcyluv20

"Masifa da bala'i, Kamarni har wata Aljana ta isa ta firgita? Ina Isma'ila ya zo ya yi mini iyaka da wannan Aljanar tun kafin raina ya ɓaci" Innati ta faɗi hakan jikinta gabaɗaya rawa yake na fargaba da tsoro, tuni ta yi wurgi da zanin jikinta sai ɗan tofin daya rage mata banda haka tsirara za ta yi.

Uncle Isma'il daya fito a hargitse sbd jin kiran shi da Innati ke yi ya sa yana zuwa ya ce "Innati lafiya dai? Mene ya faru?"

Ta girgiza kai ta ce "Lafiyar kenan, maza maza a haɗa mini kayana yau sai gidan Bello, ba zan zauna matarka da kasheni ba, ina sane ita take tura mini Aljanu" Uncle Isma'il ya kusan tuntsirewa da dariya amma babu hali duk abin da ya kuro ɓera da ga wuta, ya fi wutar zafi. "Majeederh ta ƙarasu?" Ta zare idanu ta ce "Wata abace haka? Ka je dai kaga turan da akai mini da wata Bafullatanar Aljana" Uncle Isma'il ya bar Innati a tsaye, tare da nufar ɗakinta. Yana shiga ya samu Majeederh durƙoshe a saman gwiwoyinta ta dafe kanta da hannu bibbiyu wanda yake bazaranar rabe mata gida biyu sbd tsananin ciwon da yake mata, ta rufe idanu sosai sbd komai bibbiyu take ganinsa a cikin idanun nata. Uncle Isma'il ya zuba mata ido cike da tausayinta yasan duk abin da zai sanya Majeederh cikin wannan yanayin ba abu ne mai sauƙi ba. Ya dubi Little dake tsaye ya ɗora kansa a bayanta ya saƙalo wuyanta tare da yin lamo, yanayin Mamin tasa ya taɓa kuzarin yaron. Ya nemi waje ya zauna saman kujerar dake ɗakin na Innati, cikin kulawa ya ce

"Hawwa'u!" Ta yi sauri ta ɗago kanta tare da ƙaƙaro murmushi ta ɗorawa fuskarta matsayin dole. Cikin sanyin murya kamar kullum ta ce "Ina yini Uncle?" Ya ce

"Lafiya" ya yi jim kafin ya ɗora da "Ke kika firgita mini uwata ko?" Ta ƙara yin murmushi kamar ba za ta yi magana ba ta ce

"Da Aljana take haɗani fa" Ya yi murmushi ya ce "Dole ta haɗaki da Aljanu, ni kai na mamakin kyan da Ubangiji ya yi wa ƴata nake, sai yanzu nake ƙara ganin cancantar suturta fuskar da kike"

"To ALLAH ya isa, Allah ya isa shi kaɗai zai isar mini idan ka yafe Allah ya tsine" Innati dake bakin ƙofa tana leƙowa ta furta hakan lokacin data tabbatar Jikarta ce Majeederh Abdul'aziz Khan! "Ki yi haƙuri Innati"

Innati ta fashe da kuka sosai tana face hanci ta ce "Wallahi ba dani kike ba, ba kuma ni ki kaiwa ba, Ubanki mai faÉ—in ran nan da manyan Idanu Audil azizu shi kika tsoratar" Majeederh dai bata kulata ba, domin tunaninta baya wajan gabaÉ—aya zuciyarta tana wani birgire wanda kullum take ganin kanta acan, a cikin mafarkanta na kullum.

"Majeederh wa kika bari a waje? Na ga mota" Uncle Isma'il ya faÉ—i hakan cike da zumuÉ—in jin Majeederh ta ce wani ne ya kawota, addu'a yake Allah ya sa nata rabon auren ne ya zo.

"Latifa Omar ce"

"Ayya to, Allah ya amfana" Ya gyara zama sosai ya ce "Hawwa'u ki faɗa mini gaskiya, mene hujjarki na barwa Rumana saurayin dake son ki yake son aurenki a lokacin baya, sai yanzu kwatsam! Reshe zai juye da mujiya wai kin fasa auren shi ya auri ƙanwarki Rumana anya akwai ƙamshin gaskiya? Domin na lura da rashin nutsuwarki, A can gidan" Ta yi shiru domin bata da amsar tambayar Uncle ɗin nata, ita yanzu a yadda take ji ko sa'an mahaifinta Abbu aka bata matsayin miji da gudu zata amsa, koda ha za ta yi farin ciki ba da zama da shi muddin zai ɗauke buƙatar ta, wacce ke damunta take sanyata rama da ibadar dole.

"Ina jinki, kin fi ganewa ki zauna duka Æ´an-wanki su yi aure ke kina gida? Kin fi ganewa ki gansu da mazajansu gwanin sha'awa suna yin soyayya da rayuwar aure mai tsafta? Su haifi Æ´aÆ´a wanda ko wanne mai rai yake muradi, inma namiji inma mace? Zuciyarki ta yi rayuwarki adalci? Anya Hawwa'u-Jidderh?"

"Ka yi haÆ™uri Uncle, Idan da rabo zan yi auren" 

Maganarta ta narkar da zuciyar Uncle Isma'il, kalamanta sun nuna karaya zahirin fuskarta kuma ta amshi ƙaddarar tare da godewa Allah bisa tarin Ni'imar da ya yi mata, tasan yana sane da ita bawai barinta ya yi ba. "Shikenan, ALLAH ya yi miki Albarka ki je wajan Luba" caraf Innati ta ce "Wacce masifar ce Luba? Ka fita daka idanuna Isma'ila matar taka da ban gama sanin zuciyarta ba ita zaka turawa Kululu? Ƴar Gombe? Wato ta tsaface ta bayan kasan yadda Fulanin Gombe suke?"

"Allah ya baki haƙuri Innati, zan shige taron da ake yau babu mamaki na samu dacewa da aiki mai kyau" "A to! Ya dai fi maka, kamar tsiya akan ƴaƴana ta kare kowa fama yake da kansa da azababben talauci, In sha Allah tsalelen miji Kululu zata aura na tarkata na koma gidanta" Murmushi kawai Uncle Isma'il ya yi tare da shafa kan Little ya ce "Yau ba magana?"

"Mami kakewa faÉ—a"

"To É—an Maminta Allah ya baku haÆ™uri kai da Mamin"  Yana fita Innati ta yi Æ™asa da murya ta ce 

"Munafuki, ai duk tsinewa matarsa da nake to ta shi nake, daga shi har Ubanki Audil azizu sai na kai su hisba uban kowa ya huta, turmin atamfar ankon wannan yarinyar Wifat fa na ce ya siya mini wai bashi da shi?" Ta ƙara girgiza kai ta ce "Hoo! Ƙasa Ubangiji ya baki miji mai kuɗi wanda zai so ki"

Majeederh ta marairaice fuska sosai ta ce "Innati bar maganar auren nan"

Innati ta riƙe haɓa ta ce

"To ba zan bari ba, Annamimiyya ina nan watarana idan ban mutu ba sai mijinki ya sunkuya ya miki doki-doki dake da yaran da zaki haifa, wallahi ko bana raye sai kin tuna wannan maganar tawa, zaki haifi zuri'a mai yawa zuri'ar da babu Uban wanda ya taɓa haifarta a cikin ƴan-uwanki da iyayen naki" Majeederh ta lumshe idanunta a zuciyarta tana tona tsayin shekarun da zata ɗauka kafin tabbatuwar hakan! Innati ta fashe da kuka ta ce "Allah ba zai barki haka ba, wallahi halin Uwarki Fulani kika ɗauka, har tsinannen kyan da kike da shi duk nata ne, ki rubuta ki ajjiye watarana sai labari ni dai ki sani ina son ki ba zan baki gurguwar shawara ba, amma dai Allah ya yi ɗaiɗai da zuciyar Rumana" Surutun Innati ya hau wa Little ka, daman ba daɗi yake ji ba ta shagwaɓe fuska tare da fashewa da kuka ya faɗa jikin Majeederh ya ƙanƙameta "Mami gida"

Majeederh ta yi saurin rungume shi tana shafa kansa yau ɗin gabaɗaya ta rasa meke damunsa ga kanshi zafi kamar mai zazzaɓi. "Innati kin firgita mini yaro" Innati ta riƙe baki ta kasa cewa komai sai can ta ce "Ba zan ce komai akan yaron nan ba, amma dai a guji gobensa akwai abubuwan Al'ajabi cikinta" Majeederh ta ɗauke ɗan ta tare da rungume shi sosai a ƙirjinta tana ji yana sauke numfashi ya ƙanƙameta.

Latifa Omar ta yi murmushi mai kyau tare da kallon Aliyu ta ce

"Kana da abin dariya"

Aliyu Sufyan Alhassan ya ce "Uhm Latifa Ina son ki, bana son a É—auki lokaci ki bani dama"

"Daka ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaƙi?" Ya yi murmushi kawai kana ya ce "Bani labari"

"Na me? Akan wa?" Latifa Omar ta tambaya. Ya ce "Your friend"

Ya nuna Æ™ofar gidan da Majeederh ta shiga. Latifa ta juya idanunta ta ce "Oh, Sunanta Majeederh Abdul'aziz Khan! Iyayenta suna yawan ce mata Hawwa'u, Æ™annenta musamman Aaliyyah tana ce mata Jeederh. Mun yi makarantar primary lokacin É—aya, amma ta fini Æ™oÆ™ari ne sa ba kusa ba, da yawan lokaci ina hana kai na bacci ganin na zama ita, sai na fahimci iliminta baiwa ce, daga Allah. Biye É—aya takewa ayar Alkur'ani ta hadda ce ta, tun muna primary ta rasa mahaifiyarta, she left her, at the same time ta yi saukar Alkur'ani, ni kuma na maimaita aji, a lokacin da ta zama hafiza a lokacin na yi sauka ta farko" Ta yi jim,tana rayuwa da step mother É—in ta, kishiyar babbar ta, ilimin Majeederh ya sa Manyan mutane na primary school É—in mu suka shige mata gaba wajan samun scholarship a matakin secondary school, ta samu makaranta mai kyau tun a lokacin Karatun ta a É“angaren Islamic yake, yanzu maganar da nake maka ranar Candy ranar ta zama Gwarzuwa a É“angaren musabaÆ™ar Alkur'ani, wannan shi ne kashi na wajan uku na dai manta Makarantarmu Ahlul Madar tana bada sunanta matsayin wacce zata jagoracemu, yanzu haka sunanta yaje ko'ina duk wata gasar karatun Alkur'ani indai Kano zamu shiga to ita za ta yi" Ta ja aya tana sauke numfashi. Tunda ta farar maganar idanun Aliyu a rufe yake ruf ta ce 

"Lafiya?" A taushashe ya ce "Ina jinki"

"Majeederh ta zama malama a Ahlul Madar duk wata suna bata albashi, da albashin take kula da yaron daka gani a wajanta" Ya ware idanu da mmki ya ce 

"Yaro? I heard you kin ce single take, not house wife" ta ce "Eh,  Tsintar yaron ta yi, kuma tana son sosai banda kada na yi maka Æ™arya bayan iyayenta babu wanda take so kamar Little, tana iya haÆ™ura da cikinta ta bashi ya ci, kuÉ—in Makaranta, kayan sawa duk da albashinta take masa, kuma a ciki take taimakon Abbu da abincin gida, by the way yanzu tana shirin tafiya Æ™asar waje Africa, ta samu scholarship za ta É—ora University É—in ta a can É“angaren Islamic and Arabic studies"

Ta yi shiru ganin kamar Attention É—in Aliyu baya kanta ta ce "Ya dai?"

"Wacce ƙasa?" Ya faɗa yana murmushinsa mai kyau da aji. "Misira"

"Ok Egypt, Allah ya taimaka"  Latifa Omar ta ce "Amin".

A can cikin gida Hajiya Luba ta kalli Majeederh ta ce "Yanzu karatun zaki?" Majeederh ta sauke ajjiyar zuciya a fili tare da jinjina kanta alamar "Eh, Mama"

"To Ubangiji ya sa rabokin ke kiranki, Allah ya baki ikon cinye ƙaddarorinki mutane ne kawai da basu son zama lafiya gabaɗaya nawa kike balle ƴan-uwanki shekaru Ashirin bai ci har a fara gorantawa mutum bai aure ba"...

“...... Allah ya kyauta”

Ta ci-gaba da bata haƙuri da ban mamaki. Har Latifa Omar ta shigo suka ta fi gidan Yaya Bilkisu domin acan ake Sabgogin bikin Widad ɗin. Ko! Da ta je bata iya zama ba ƴan matan familyn Khan, suka shiga sauke magana. Kusan duk akan Idanunta aka haife su sbd rashin aure ya sa girmanta ya zube. Tana zaune kiran gaggawa ta sameta zuwa Orphanage for young children, kira ne daga kai tsaye daga Akeeth. Yaya Bilkisu ta bata kuɗin napep daman tuni ta ce Latifa Omar ta tafi kawai. Tana gab da zuwa ta sake kiranta.

"Assalamu alaika"

Majeederh ta furta cikin muryarta mai sanyi daÉ—i a kullum. Akeeth ya amsa ya ce "Am sorry Majeederh,na samu meeting na gaggawa idan na gama ko kiranki ne zan yi" Jikinta san yi Æ™alou ta kashe wayar ba tare data ko amsa masa ba. 


Unguwar Darmanawa

Idanunsa rufe yake kallon selling É—in dake cikin bedroom É—insa, lokaci na farko a rayuwa da ya yi nauyin baki wajan furta abin da yake so. Ya juya kaÉ—an yana sake mirginawa hoton idanunta kawai suke gilmawa cikin nasa idon, ganin abin bazai goge ba sai ma Æ™aruwa da yake ya sa a hankali ya miÆ™e ya shiga bathroom tare da sakarwa kansa shower yana riÆ™e Æ™ugunsa bugun zuciyarsa na Æ™aruwa gabaÉ—aya Latifa Omar ba tsarin aurensa ba ce, me ya kai shi? “Density” Shi kansa bai adadin lokacin daya É—auka a bathroom É—in ba, sai da ya ji ana knocking Æ™ofar part É—in shi ya fito É—aure da towel a jikinsa. 

"Meke damun ɗan autan Hajia yau da bai yi dinner damu ba?" Aliyu ya shagwaɓe fuska sosai autar ta motsa daman rauninsa da wuri yake fallasa asirin zuciyarsa. Ya ja baya yana zama kan kujerar dake kusa da gadon shi, ɗan ƙasar Turkiya. "Hajia"

"Na'am Autan Hajia" Hajia ta amsa tana jiran ta ji dame yau kuma ya zo, domin shi Aliyu baya rabo da issues sbd tsabar taɓara gashi kyakkyawan ajin farko sai ka ɗauka Half-caste ne. Looking so classic. "Aure zan yi, na samu mata" Ya faɗi hakan domin a tunaninsa shi ne mafita ga abin da yake ji, wacce zai aura daban, wacce ta yi zuciyarsa kamo daban. Ko mene hakan hakan? Only God knows.

Sosai Abbu ya yi wa Majeederh faɗa don me bata ƙarasa ta karɓo form ɗin ba? Ita dai bata ce komai ba ita kaɗai ta san abin da take ji. Yau ɗin ma sai da ta yiwa Little wanka ta sanya masa kaya masu ɗan sauƙi bata son ya kwana da zazzaɓi. Ta tsora masa idanu a hankali ta ce "Little zaka manta dani?" "Me?" Ta tambaya domin bai fahimta ba.

Ta ce "Idan na ta fi karatu, karka manta dani ka ji? Kada ka bawa wata matsayin uwa a zuciyarka idan ba Maminka ta gasky ba, ka da ka ci amana" Ita kaÉ—ai take magana ita kaÉ—ai kuma take fahimtar me take cewa. Ya shafa laɓɓanta da suke jajir ya ce "Mami ni ma irin naki" 

Ta yi murmushi tana ɗaukar shi tare ta ɗora a cinyarta ta ce "Until you grow up" Ya shiga buga ƙafa da yarfe hannu shi a dole sai laɓɓansa sun yi irin na Maminsa Jee ta tura masa baki ta ce

"Ok Shafi kaÉ—an, da safe sai koma red" Ya yi murmushi yana tsalle ya É—ora bakinsa a nata ya shiga goga sai ta gaji ta É—auke shi tana dungure masa kai, Æ™ara wayarta ta yi tana duba taga albashi akai mata sosai ta ti farin ciki gobe za ta yi masa siyayya. Tunanin yadda zata rabo da Little tsayin shekaru takwas shi ne  ya bijiro mata, rabon da ta yi kuka ta manta sbd kansa cewar ta mace jaruma da zurfin ciki. Ta samu kanta da rungume Little ta fashe da kuka sosai, kukan da rabon da ta yi shi tun rasuwar Fulani. Wani irin kuka take da dukkan Æ™arfinta wanda yake tasowa tun daga Æ™asan zuciyarta. Ganin tana kuka ya sa Little fashewa da kuka sosai.  Da Æ™yar ta rarrashe shi suka kwanta bacci. Kiran sallarsa farko ya farkar da Majeederh daga bacci a hankali ta shafa tana son taÉ“a jikinsa ta ji ko da zafi. Wayam! Ta buÉ—e idanu taga babu Little a kan gadon ta miÆ™e da sauri idanunta ya sauka akan Æ™ofar É—akinta dake buÉ—e bayan har rufewa ta yi. Da sauri ta ce "My Son, Little?....


No comments